07/05/2025
Yaƙe yaƙe har uku aka gwabza tsakanin Indiya da Pakistan tun bayan da s**a sami yancin kai a shekarar 1947. Ga shi kuma na hudu na kokarin ballewa.
Kashmir yanki ne da ke tsakanin Indiya da kasar Pakistan wadda kasashen biyu s**a shafe shekaru da dama suna rikici dangane da mallakarsa.
Rikicin da aka dade ana gwabzawa kan yankin Kashmir da ta'addanci a kan iyakokin kasashen biyu, shi ne musabbabin rikici tsakanin kasashen biyu, in ban da yakin Indo-Pakistan na 1971, wanda ya faru ne sakamakon tashin hankalin da ya samo asali daga yakin 'yantar da Bangladesh a tsohuwar Pakistan (yanzu Bangladesh ).
Ga duk me bibiyar rikicin dake faruwa yanzu a kasashen indiya da fakistan, bazai kasa sanin rikicin yankin kashmir tsakanin Indiya da makociyarta Pakistan ba. Rikicin neman mallakar yankin tsakanin kasashen biyu ya janyo asarar dinbin al'umma musamman mabiya Addinin Musulunci. Kowace kasa tsakaninsu nason mallakar yankin da yake da yawan al'umma akalla miliyan 69,07,623. Srinagar ita ce yanki mafi yawan jama'a a kwarin Kashmir, tare da mazauna 1,269,751. sannan yanki ne me dinbin arziki musamman ta bangaren noma da sana'oin hannu, da yawon buɗe ido.
Bisa tarihi kasashe uku ne suke rikici akan mallakar yankin, banda Indiya, Pakistan akwai kasar sin (China). Yankin na Kashmir da ake kira Jammu Kashmir yana karkashin ikon Indiya yanzu haka, amma kuma sauran kasashen biyun su ma suna da iko da wasu wuraren. Indiya nada iko da akalla kaso 70, inda ya kunshi Jammu, Jammu ladakh da kuma Siachenglacier. Ita kuma Pakistan tana da iko da kaso 30 daya kunshi Azad Kashmir da Gliqit Baltisan, yayinda China kuma takeda kaso 15 daya kunshi Shashgam Valley da kuma Aksai chin.
Yankin Jammu Kashmir jiha ce karkashin kasar Indiya, amma kuma tanada kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai, wanda ya kunshi cewar babu wata doka da 'yan majalisun Indiya zasuyi da zatayi amfani a yankin, sai dokar da 'yan majalisun yankin s**ayi. Sannan yankin ne kadai yake da tutar sa ta kashin kansa, wato