29/09/2025
Da dumi'dumi: Gwamna Uba Sani Ya Jawo Sama da Dala Biliyan 2bn — Kaduna Ta Zamto Sabon Gidan Zuba Jari!”
Kaduna, Najeriya – Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kafa sabon tarihi a fannin tattalin arziki tun bayan hawansa mulki a watan Mayu 2023. A kasa da shekaru biyu kacal, ya jawo fiye da Dala Biliyan 2 na alkawuran Zuba Jarin Waje (FDI) – abin da ke canza fuskantar tattalin arzikin jihar.
Babban Jari Daga Duniya
Ɗaya daga cikin manyan nasarorin shi ne yarjejeniyar Dala Miliyan $62.8 tare da Asusun Kuwait Fund domin gina muhimman ababen more rayuwa. Haka kuma, an kulla haɗin gwiwar Dala Miliyan $120 da Romania domin bunƙasa noma da masana’antu.
Hakar Ma’adinai Da Smart City
An rattaba hannu kan yarjejeniyar Dala Miliyan $300 da kamfanin Atlantic Mining Techniques Ltd domin hakar ma’adinai. Haka kuma ana shirin kafa “Smart City” mai darajar Dala Miliyan $150 don mayar da Kaduna cibiyar fasahar zamani.
Jarinsu Daga Asiya
Kamfanonin kasar Sin sun bayyana sha’awar zuba jarin sama da Dala Miliyan $350 cikin watanni bakwai kacal — a fannin noma, ababen more rayuwa da albarkatun kasa. Wasu daga cikin yarjejeniyoyin sun fara aiwatarwa.
Huawei, Qatar Charity Da AfDB
Kaduna ta samu shigowar FDI Dala Miliyan $503 daga kamfanoni k**ar Huawei da Qatar Charity, da kuma samun matsayi a cikin shirin SAPZ na African Development Bank da IFAD mai darajar Dala Miliyan $520, wanda zai samar da aikin yi har rabin miliyan.
Sabon Yanayi Na Tattalin Arziki
Ƙoƙarin Gwamna Uba Sani ya rarraba zuba jari a fannoni da dama — noma, hakar ma’adinai, yawon buɗe ido, ilimi, sadarwa, ababen more rayuwa da fasahar zamani. Masu lura na cewa wannan tsari ne mai natsuwa ba siyasar cin karo ba.
Kalubale Guda Ɗaya – Gudun Aiki
Babban ƙalubale yanzu shi ne tabbatar da waɗannan yarjejeniyoyi sun fita daga takarda zuwa ayyukan da za su amfani al’umma kai tsaye. Amma abin da ba za a musanta ba shi ne: ƙarƙashin jagorancin Uba Sani, Kaduna ta shiga fagen zuba jari na duniya da sabon ƙarfin gwiwa da fata mai haske.
Daga Dambatta
(Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Kaduna kan Harkokin Jaridu)