18/05/2025
Daga T**i Zuwa Gaskiya – Sabon Hanya Ga Matasa a Kano
A yau wani muhimmin shafi ya bude a tarihin cigaban matasan Jihar Kano, yayin da aka kaddamar da shirin "Daga T**i Zuwa Gaskiya" wanda Mai Girma Abdulsalam Abdulkarim AA Zaura ya dauki nauyinsa ta hannun gidauniyarsa mai suna AA Zaura Foundation.
Wannan shiri ya gudana a cikin kyakkyawan yanayi a Meen Event Centre, inda fitattun shugabannin al’umma, masu fafutukar kare hakkin matasa, kungiyoyin farar hula, da dimbin matasa s**a hallara domin shaida wannan gagarumin sauyi.
Manufar wannan shiri ita ce: ceto matasa da ke yawo a tituna, wadanda s**a fada cikin yanayi na talauci, rashin kulawa ko aikata laifuka, domin dawo da su ga sahihin tafarki – ta hanyar horar da su da sana’o’i, samar da tallafin ilimi, da kuma ba su damar sabuwar rayuwa mai cike da burin gobe.
AA Zaura ta hanyar gidauniyarsa, ya bayyana cewar wannan shiri na daga cikin muhimman matakan da zai taimaka wajen rage yawan zaman banza, aikata laifi da rashin tsaro a cikin al’umma. Ya kara da cewa "Matasa su ne ginshikin al’umma. Idan muka basu kulawa da goyon baya, mun riga mun gina gobe mai kyau."
Wannan shiri zai ba matasa damar shiga aji na koyon sana’o’i daban-daban kamar gyaran waya, aikin kafinta, dinki, noma, gyaran mota, da sauran sana’o’in hannu. Haka kuma, ana sa ran za a basu tallafin kayan aiki bayan kammala horo domin su fara dogaro da kansu.
AA Zaura Foundation na ci gaba da zama tushen sauyi a jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya, musamman ta hanyar shirye-shiryen da ke bai wa talakawa da matasa damar ficewa daga halin kuncin rayuwa.
Tare da ku, za mu iya canza rayuka. Za mu iya bude sabbin kofa. Kuma za mu iya ceto rayuwar dubban matasa.
Muna kira ga iyaye, shugabanni, da daukacin al’umma da su marawa wannan shiri baya domin ceto rayuwar matasan mu.
Sulaiman Amir Rangaza
DG AA zaura media