27/07/2025
Rashin Matasan Sha’iskawa Ɗambatta: Labarin Jimami da Alhini
Daga Auwalu Nakarkata Dambatta
A cikin wani mummunan haɗarin mota da ya auku a daren Asabar, 26 ga Yuli, 2025, al’ummar Ɗambatta, musamman ma unguwar Sha’iskawa, sun shiga cikin jimami da alhini sakamakon rashin wasu matasa masu ƙwazo da burin rayuwa.
Matasan, waɗanda dukkaninsu ‘yan unguwar Sha’iskawa ne, sun rasu a garin Gada, dake cikin ƙaramar hukumar Kazaure ta jihar Jigawa. Wannan lamari ya faru ne a kan hanyarsu ta dawowa gida daga ɗaurin auren wani abokinsu da ya gudana a jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa motar da suke ciki, ƙirar Golf Wagon, ta yi gaba-da-gaba da wata babbar motar J5 yayin da ake samun iskar hadari a yammacin ranar. Sakamakon wannan hatsari mai firgita, direbobin motocin biyu tare da sauran fasinjoji shida da ke cikin motocin, s**a riga mu gidan gaskiya. Bugu da ƙari, wasu mutane biyu sun jikkata a cikin haɗarin.
Tuni aka gudanar da jana’izar matasan shida kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. An yi jana’izar ne da sanyin safiyar Lahadi, 27 ga Yuli, 2025, a Masallacin Juma’a na Hajiya ‘Yar Shehu da ke cikin unguwar Sha’iskawa Ɗambatta, karkashin jagorancin babban limamin masallacin.
Wannan babban rashi ya girgiza zukata da dama – daga iyaye, abokai, da dukkan al’ummar Ɗambatta da s**a san irin halin kirki, ladabi da burin da matasan ke da shi. Tabbas, sun bar gibi da ba zai cika da sauƙi ba.
Muna roƙon Allah Madaukaki Ya gafarta musu, Ya sauwake masu hisabi, Ya sanya su cikin rahama da jinƙansa, Ya kuma kyautata namu zuwan. Amin.