11/09/2026
JAN HANKALI: Ba Ni Na Kaiwa Sheik Musa Lukuwa Farmaki Ba, Ni Masoyinsa Ne Na Gidi, Inji Aminu Usman
Sunana Aminu Usman, kuma ni ne matashin da ake ta yaɗa hotonsa a kafafen sada zumunta, ana cewa wai ni ne wanda ya yi ƙoƙarin kashe Malam Musa Ayuba Lukuwa.
Ina so in bayyana wa kowa gaskiyar abin da ya faru:
Ni ina yawan yin posting na bidiyon karatukan Malam Musa Ayuba Lukuwa. A mafi yawan bidiyon da nake wallafawa, nakan ɗora wannan hoton a saman bidiyon. Idan kuma posting ɗin ya shafi Malam, nakan ɗora hoton da muka taɓa ɗauka tare.
A yau, bayan abin da ya faru a masallacin Malam, na yi posting game da lamarin, sannan na sake amfani da wannan hoton kamar yadda nake yi a sauran posting ɗina.
Sai abin ya baɗu, wasu s**a fara yaɗa hoton suna cewa ni ne matashin da ya yi ƙoƙarin kashe Malam.
Wallahi ba ni ba ne. Wallahi ba ni ba ne.
Ina kira ga kowa da kowa da ya guji yaɗa wannan zargi ba tare da tabbatar da gaskiyarsa ba. Hoton da ake yaɗawa hotona ne, amma abin da ake danganta min da hoton ba ni na aikata shi ba.
Duk wanda yake son tabbatar da yadda nake amfani da wannan hoton, ina roƙonsa ya shiga page ɗina na Sakkwatawan Shehu, ya duba tsoffin posting ɗina. Za ku ga cewa a lokuta da dama nakan yi amfani da wannan hoton tare da bidiyon karatun Malam.
Don Allah, a daina yaɗa wannan zargi a kaina. Ina roƙon kowa ya bincika ya tabbatar kafin ya yada labari, domin irin wannan zargi na iya cutar da mutum sosai.
Allah Ya bayyana gaskiya, Ya kare Malam Musa Ayuba Lukuwa, Ya kuma kare kowa daga zalunci da zargin da ba shi da tushe.
NA GODE DA FAHIMTA.