Arewa News

Arewa News Arewa News 🇳🇬

​Muna aiki da gaskiya da rikon amana. Madogarar sahihan labarai, masu armashi , kan Siyasa, Al'adu, Kasuwanci da Wasanni.

Zaku iya aiko mana da sakonni da rahotonni ta WhatsApp akan 09073204050

​Tashar Yaki da Labaran Bogi 🚫.

Harin mayaƙan Houthi ya kashe aƙalla 10 a YemenWani harin mayakan Houthi ya kashe akalla mutum 10 a birnin Marib na Yame...
08/08/2026

Harin mayaƙan Houthi ya kashe aƙalla 10 a Yemen

Wani harin mayakan Houthi ya kashe akalla mutum 10 a birnin Marib na Yamen.

Mayakan masu samun goyon bayan Iran da kuma ke rike da ikon babban birnin Yemen har zuwa yammacin Marib sun ce sun kai harin ne kan dakarun da ke samun goyon bayan Saudiyya.

Sun kai harin ne kwana guda bayan kashe wasu dakarun gwamnatin Yemen da dama a wani hari ta sama da mayakan na Houthi s**a kai a sasanonin soji na Marib da lardin Hadramawt bayan mutuwar wasu fararen hula 11 a wani harin na Houthi a yankin Najran na Saudiyya

07/08/2026

Matasa, ya kamata mu san darajar kanmu. Kada mu bari a riƙa amfani da mu idan ana da buƙatarmu, sannan a manta da mu idan an gama.

Mu kasance masu mutunci, mu girmama kanmu, kuma mu tsaya a kan gaskiya. Duk wanda ya daraja ka, zai nuna hakan ba sai lokacin da yake da buƙatarka ba.

゚ ゚

06/08/2026

Matasan Nasarawa, lokaci ya yi da za mu farka!

Duk wanda kake tare da shi amma ba ya son cigabanka, ba ya ƙarfafa maka guiwa, ko yana jan ka a baya, to karabu dashi.

Mu san darajar kanmu, mu tsaya kan gaskiya, ilimi, aiki tukuru, da ci gaba. Mutuncinmu da makomarmu sun fi komai muhimmanci.

05/08/2026

Rayuwar ɗan Adam ta fi siyasa da mulki muhimmanci.

Saboda haka, ya ku matasa, mu farka! Mu kasance masu hankali, mu fifita zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban al'umma. Siyasa ta zo ta wuce, amma rayuwar ɗan Adam ba ta da madadin.

Allah Ya kare ƙasarmu, Ya ba mu zaman lafiya da haɗin kai.

By Ismail-M-Jafar ✍️ and

Shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu ya amince da ƙarin albashi da ya kai kashi 30 zuwa 80 ga dakarun sojojin Najeriya.Ka...
04/08/2026

Shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu ya amince da ƙarin albashi da ya kai kashi 30 zuwa 80 ga dakarun sojojin Najeriya.

Karin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2026, kamar yadda wata sanarwar daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

Sanarwar ta ce sojojin Najeriya aƙalla 250,000 ne ake tsammanin za su amfana da wannan sabon ƙarin albashi.

Ƙarƙashin sabuwar sanarwar jami'an da suke daga matsayin kanar zuwa birgediya janar da manjo janar da laftanar janar da janar duka za su samu ƙarin kashi 30 ne cikin 100.

Tun daga matsayi na ɗaya da ake kira laftanar na biyu da laftanar da manjo da zuwa laftarnar kanar za su samu ƙarin kashi 80 cikin 100 na ƙarin albashin.

Yanzu ƙunshin albashin sojojin na shekara zai tashi daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924.

Shigaba Tinubu yace an ɗauki matakin ne saboda cika alƙawarin gwamnatinsa na "kyautata rayuwar sojoji da suke yaƙi da matsalolin Najeriya irinsu ɓarayin daji, da masu satar mutane domin neman kuɗin fansa da 'yan ta'adda da suke a faɗin ƙasar".

Arewa News

04/08/2026

BBC Hausa labaran Yau na dare

04/08/2026

...

04/08/2026

BBC Hausa labaran Duniya na safe

04/08/2026

04/08/2026

...

Address

Kano
09073204050

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share