Hausa Viral

Hausa Viral Labarai a ko da yaushe!
(3)

Kungiyar Arsenal ta cigaba da rike kambunta na rashin daukar kofin zakarun nahiyar Turai a tarihi, bayan doketa a wasan ...
30/05/2026

Kungiyar Arsenal ta cigaba da rike kambunta na rashin daukar kofin zakarun nahiyar Turai a tarihi, bayan doketa a wasan karshe da kungiyar PSG ta yi, a bugun PK.

Sai yaushe ne, Arsenal? 🤔

Monitan ajin su Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a Jami’ar Northwest da ke Kano, Ibrahim Hassan Bako Dambat...
30/05/2026

Monitan ajin su Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a Jami’ar Northwest da ke Kano, Ibrahim Hassan Bako Dambatta, ya jagoranci wasu ɗaliban ajinsu zuwa fadar sarkin domin kai masa gaisuwar Babbar Sallah.

Ziyarar ta gudana ne a safiyar ranar Asabar, inda É—aliban s**a samu damar gana wa da Sarkin tare da taya shi murnar Sallah a fadarsa da ke Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, na karatun digirin farko a fannin Shari’a (Law) a Jami’ar Northwest Kano, kuma a halin yanzu yana matakin aji na uku (300 Level).

A yayin ziyarar, É—aliban sun bayyana jin daÉ—insu kan damar da suke samu na kasancewa a aji guda da Sarkin Kano, tare da yi masa fatan alheri da samun nasara a harkokin karatu da kuma jagorancin masarautar Kano.

Da yake jawabi, monitan ajin, Ibrahim Hassan Bako Dambatta, ya ce ziyarar na daga cikin al’adun ƙarfafa zumunci da girmamawa tsakanin ɗalibai da abokan karatu, musamman a wannan lokaci na bukukuwan Sallah.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NDC Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana tsohon mataimakin gwamnan ji...
29/05/2026

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NDC Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, a matsayin dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar a zaben shekarar 2027.
‎
‎Haka kuma, Kwankwaso ya ayyana tsohon mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya karkashin jam’iyyar NDC.
‎
‎An bayyana hakan ne a safiyar ranar Juma’a a gidan Kwankwaso da ke Kano, jim kadan bayan kammala wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar da magoya baya s**a halarta.

Yaya kuka ji da Hukumar Yan Sanda ta kara dakatar da Hawan Babbar Sallah?
28/05/2026

Yaya kuka ji da Hukumar Yan Sanda ta kara dakatar da Hawan Babbar Sallah?

Amirul Hajj na Kano Ya Jagoranci Taya Alhazai Murnar Sallah a MinaAmirul Hajj na Jihar Kano kuma Sarkin Gaya, Alhaji Dr....
28/05/2026

Amirul Hajj na Kano Ya Jagoranci Taya Alhazai Murnar Sallah a Mina

Amirul Hajj na Jihar Kano kuma Sarkin Gaya, Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya jagoranci tawaga zuwa rumfunan alhazan jihar da ke Mina a kasar Saudiyya domin isar da sakon taya su murnar Sallah.

Tawagar ta hada da mataimakin Amirul Hajj kuma Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharaz Karaye, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano tare da wasu mambobin hukumar da kuma Darakta Janar na hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban tawagar yada labarai ta aikin Hajjin Kano na 2026, Mustapha Muhammad, ya fitar.

Da yake jawabi ga alhazan jihar, Amirul Hajj Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya yabawa alhazan bisa yadda suke gudanar da ibadunsu cikin tsari da natsuwa, tare da rokon su da su ci gaba da yi wa Jihar Kano da Najeriya addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.

Har ila yau, ya bukaci alhazan da su yi wa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, addu’ar samun nasara tare da dorewar zaman lafiya, arziki da bunkasar tattalin arziki a jihar.

A wani taro daban kuma, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya sanar da cewa Riyal 200 na kasar Saudiyya da gwamnan jihar ya yi alkawarin bai wa alhazai za a raba musu ta hannun jami’an cibiyoyi bayan sun koma Makkah.

Ya kuma tabbatar wa alhazan cewa hukumar za ta ci gaba da samar da ayyukan jin dadi domin tabbatar da walwalarsu a wuraren ibada masu tsarki.

Tun da farko, manyan malamai uku — Sheikh Aminu Daurawa, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi da Sheikh Abubakar Kandahar — sun gabatar da wa’azuzzuka kan muhimmancin aikin Hajji, darussansa da falalolinsa ga alhazai.

Malaman sun kuma yi addu’ar Allah Ya karbi aikin Hajjin alhazan tare da gafarta musu kura-kuransu.

27/05/2026

ÆŠan jihar Kano da ya tsinci makudan kuÉ—aÉ—e yayin aikin hajjin bana ya mayar da su ga masu su.

26/05/2026

Mahajjatan Kano sun nuna gamsuwa da irin kulawar da suke samu tare da yabawa shugabanci Hukumar Alhazai ta Kano

Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kula da lafiyar wata mahajjaciya daga jihar da ta sam...
26/05/2026

Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kula da lafiyar wata mahajjaciya daga jihar da ta samu rauni yayin gudanar da aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.

Amirul Hajj na Jihar Kano a Hajjin 2026 kuma Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Abdulkadir tare da mataimakinsa Sarkin Karaye, Muhammad Mahraz Karaye sun kai ziyara domin jajantawa da duba halin da mahajjaciyar ke ciki a otel din Al-Nakheel da ke yankin Western Central Area na Madina.

Mahajjaciyar mai suna Hajiya Zubaida Rabi’u ‘yar unguwar Zawaciki a Karamar Hukumar Kumbotso ta samu karayar ƙashi bayan isowarta filin jirgin saman King Abdul-Aziz da ke Jeddah.

Yayin ziyarar, Amirul Hajj da tawagarsa sun yi mata addu’ar samun lafiya tare da neman kariyar Allah ga dukkan alhazan Kano a yayin gudanar da aikin Hajjin bana.

Hukumar Jin DaÉ—in Alhazai ta Kano ta ce za a ci gaba da ba Hajiya Zubaida kulawar lafiya a wani asibiti da ke Makkah har sai ta murmure gaba É—aya.

Haka kuma, Sarkin Gaya ya ba da umarnin gaggauta duk wasu shirye-shiryen jin daɗi da s**a dace domin taimaka mata. Ya kuma amince da sayen tikitin jirgin ƙasa ga mahajjaciyar da masu kula da ita guda biyu domin tabbatar da tafiyarsu cikin kwanciyar hankali daga Madina zuwa Makkah.

Kwamitin Amirul Hajj na Kano ya sake jaddada ƙudirinsa na tabbatar da lafiya, tsaro da walwalar alhazan jihar baki ɗaya a yayin gudanar da aikin Hajjin 2026.

Yau ake fidda Gwani a gidan Madigu, wane fata za kuyiwa yan takara?
24/05/2026

Yau ake fidda Gwani a gidan Madigu, wane fata za kuyiwa yan takara?

Kungiyar magoya bayan Farfesa Isah Ali Pantami, wato Pantamiyya Movement Brothers ta yi mubaya’a ga Dr. Jamilu Isiyaku G...
23/05/2026

Kungiyar magoya bayan Farfesa Isah Ali Pantami, wato Pantamiyya Movement Brothers ta yi mubaya’a ga Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna, wanda jam’iyyar APC ta tsayar a matsayin dan takarar gwamnan Gombe.

A cewar shugaban kungiyar, Sunusi Hamisu Usman, matakin na da alaka da yadda Gwamna ya samu karbuwa tsakanin ‘yayan jam’iyyar APC da ma al’ummar jihar Gombe.

Sanusi ya roki Farfesa Pantami da sauran yan takarar kujerar gwamna a jihar da su hada hannu da Gwamna don cigaban jam’iyyar APC da ma jihar Gombe baki daya

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Viral posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category