04/10/2025
KOCIN CRYSTAL PALACE OLIVIER GLASNER YA MAGANTU AKAN TSARIN 3-4-3
“Tsarin wasa dole ne ya dace da irin ‘yan wasan da kake da su. Mutane suna yawan korafi kan tsarin wasa (formation), amma abin da ya fi muhimmanci shine ɗabi’u, halaye, dabaru, da kuma yadda ‘yan wasa ke motsi da fahimtar juna a cikin wasa. Wannan ne ainihin abin da yake da muhimmanci.
A aikin koci da na yi, na yi amfani da tsarin wasa iri-iri — na samu damar hawa tebur a Austria da tsarin 4-4-2, daga nan na koma 3-4-3, mun samu damar zuwa Champions League tare da Wolfsburg da tsarin 4-2-3-1, sannan a Frankfurt mun yi amfani da tsarin ‘yan baya uku saboda shi ne ya fi dacewa da 'yan wasan da muke da su.
Na fi son tsarin 4-4-2, amma hakan yana aiki ne kawai idan muna da ‘yan wasa da s**a dace da shi. A ƙarshe, nasara ba ta dogara kawai ga tsarin wasa ba, sai dai a kan kyakkyawan tsari, fahimtar juna, da haɗin kai. Dole ne ‘yan wasa su fahimci a bayyane abin da ake buƙatar su yi a fili.”
Muhammad Rabiu Rinji
Royal News Media