21/01/2025
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Ɓanagaren Mata Reshan Jihar Kano (CNG-WOMENS WING) Ta Yi Watsi Da Sabuwar Dokar Gyaran Haraji
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) reshen mata ta gudanar da wani babban taro a jiya a birnin Kano, wanda ya maida hankali kan batutuwan da s**a shafi mata, shugabanci, da tasirin dokar gyaran haraji da ake shirin zartarwa a Najeriya.
Kamar yadda Katsina Reporters ta samu, taron ya samu halartar fitattun masu magana, ciki har da Shugaban Kwamitin Amintattu na CNG, Dakta Nastura Ashir Shariff, da kuma wasu mataimakiya ta musamman kan harkokin mata ga Gwamnan Jihar Kano Haj. Fatima tare da fitaccen Malamin Addini na Kano Sheikh Ibrahim Khalil.
Kin amincewa da Sabuwar dokar gyaran haraji
Ƙungiyar matan ta bayyana rashin amincewarta da sabuwar dokar gyaran haraji, tana mai jaddada cewa dokar na da tasirin da zai iya shafar gajiyayyu, musamman mata da yara. A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron, mahalarta sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da tattaunawa mai fadi kafin ta zartar da wannan doka.
A cewar shuwagabannin taron gyaran harajin ya rasa adalci da la’akari da yanayin tattalin arziki na yankuna daban-daban a Najeriya. Hakan ya sa s**a nemi a haɗa kungiyoyin al’umma, makarantu, da kananan hukumomi a cikin shawarwarin, domin tabbatar da tsarin da zai dace da kowa.
Tasirin Tattalin Arziki Ga Mata da Iyali
Mahalarta taron sun nuna damuwa kan yadda wannan doka za ta iya jefa nauyin haraji kan talakawa, musamman a irin wannan lokaci da ‘yan Najeriya ke fuskantar tasirin cire tallafi, hauhawar farashin kayayyaki, da darajar Naira.
Kungiyar ta jaddada cewa mata, wadanda ke matsayin kula da iyali da kuma masu tasiri a bangaren kasuwanci na ƙananan hukumomi, za su fuskanci mafi tsananin tasirin wannan gyara. Hakan zai iya rage musu damar samun ababen more rayuwa da kuma hana su samun ‘yancin tattalin arziki.
Masu jawabi sun jaddada muhimmancin samun shugabanci mai adalci da kuma tsarin tattalin arziki wanda zai amfani