30/12/2025
ALLAH SARKI: Yadda Shahararrun Mutanen Ingila S**a Gamu Da Hàdari A Nijeriya
Daga Sa'adatu Baba Ahmad, Daga Ingila
Yanzu kusan dai wannan labarin na hatsarin fitaccen ɗan damben Britaniya a Najeriya, shi ne labari ma fi shahara a manyan gidajen jaridun ƙetare, yanayin dai yadda aka fito da shi daga motar ne dai ba ambulance, ba kurar ɗaukar mara lafiya da ma’aikatan lafiya da sauransu ya fi ɗagawa mutane hankali a nan Ingila.
Sannan zarge-zarge sun yi nisa ana cewa ragowar biyun ma da s**a rasu ba su sami kulawar gaggawa ba ne.
Duk da kulawar jaje da shugaban shugaban ƙasar Najeriya Asiwaju ya fitar da gaggawa da wasu shahararrun mutane k**ar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauransu wannan bai sanyaya zuciyar ƙasashen waje ba.
Dukka matasan uku ‘yan ƙasar Ingila ne, sai dai ko wannensu yana da tushe daga wasu ƙasashe.
Anthony Joshua haifaffen Wartford ne a yankin Hertfordshire ta ƙasar Ingila, uwassa Yeta ‘yar Najeriya ce, Babansa Robert ruwa biyu ne ɗan yankin Ireland ne da kuma Nigeria. Ya yi matuƙar sabawa da Nigeria da mutanen Nijeriya domin wasu rahotanni sun ce ya taɓa zama na tsawon lokaci a Najeriya kafin afkuwar wannan hatsarin na yau. Shi dai yanzu ya bubbugu tare da wasu raunika ne, yanzu yana asibiti, Allah Ya ba shi lafiya.
Ragowar mutane biyu da s**a rasu a yayin hatsarin akwai Sina Ghami ya kasance mai horar da ƙarfi da juriya na Joshua tsawon fiye da shekaru 10. Hakanan yana daga cikin masu kafa Evolve Gym a London.
Ghami kwararre ne a fannin kiwon lafiya da motsa jiki wanda ya ƙware a fannin raunukan ƙashi da motsa jiki na gyara. Ya yi aiki tare da 'yan wasan kwaikwayo da manyan shahararru a cikin National Football League (NFL), National Basketball Association (NBA), da kuma kungiyar kwallon ƙafa ta Michigan State University.
Abdullatef Latif "Latz" Ayodele ƙwararre ne wajen wasan motsa jiki, shi ne mai horar da Joshua na ƙashin kai. Sha'awarsa ga motsa jiki ta bayyana a shafukan sa na sada zumunta, haka nan kuma sadaukarwarsa ga addinin Musulunci. Ya karɓi Musulunci a shekarar 2012 ya kasance mai bayar da gudummowa ga matasa da aiyukan Sadaqatul-Jariya iri-iri daban-daban a wurare daban-daban. Yana yawaita cewa ‘babbar albarkata ita ce shiga musulunci “ wannan shi ne abinda ya rubuta a cikin wani sakon da ya maƙala a shafinsa tun shekarar 2020.
Asali, Kevin Ayodele, Latif ya buga wasan ƙwallon ƙafa ne, ya buga wasan kwallon ƙafa ne ga Aylesbury United, Tooting & Mitcham United, Hillingdon Borough, AFC Hayes, Chalfont Wasps da Northwood. bayan ya karɓi addinin Musulunci kuma ya koma suna Abdul Latif – wanda aka fi sani da Latz.
Ban samo takamemen a wacce jiha ya gina makaranta ba, sai dai na ga wani bidiyonsa inda yake cewa ya samar da kujeru da tebura na ajujuwa da kuma wajen motsa jiki da duk abinda ake buƙata don bunƙasa ilimi da jin daɗin matasa, kuma ya fara samar da ayyukan jin ƙai manya ga marasa ƙarfi tun a 2019.
Tallafin Lateef na kusan ƙarshe shi ne, ya bayar da kekunan motsa jiki guda ɗari. Allah Ya ji ƙansa.
Wannan hatsari yak**ata ya zama wani darasi ga Najeriya na samar da kayan aikin gaggawa a lokutan hatsari, domin ire-iren waɗannan abubuwa sun sha faruwa da gama-garin mutane ba tare da wani ya damu ba amma yanzu duk ɗaukin da gama garin mutane da jami’an tsaro su ka kai yayin hatsarin, bai hana mutanen ƙasashen waje kuka da ƙorafin wasarere da rayuka ba. Babbar tambayar da wasu ke yi mana anan shi ne wai dama babu ambulance babu stretchers na ɗaukar mara lafiya a Najeriya ne? Amsar dai ko akwai to ba ta yi rana ba gaskiya.
Sa'adatu Baba Ahmad ɗaliba ce mai karatun degree na uku a Jami’ar Bedfordshire da ke Ingila.