19/09/2025
TUNATARWA:
1. Ka riƙe sallah, domin ita ce hasken rayuwa.
2. Ka yi biyayya ga iyaye, domin albarkar rayuwa tana tare da su.
3. Ka yi hakuri da jarabawa, domin Allah yana tare da masu hakuri.
4. Ka guji zalunci, domin zalunci duhu ne ranar ƙiyama.
5. Ka riƙe amana, domin rashin amana yana lalata mutum.
6. Ka kasance mai gaskiya, domin gaskiya tana kaiwa aljanna.
7. Ka riƙe zuciyarka da tsoron Allah, domin shi ne ginshiƙin kwanciyar hankali.
8. Ka taimaki marasa ƙarfi, domin taimako yana jawo rahamar Allah.
9. Ka guji son zuciya, domin son zuciya yana kai mutum ga halaka.
10. Ka tuna mutuwa, domin ita ce mai ƙarfafa mutum ya shirya lahira.
Shaykh Muhammad Bin Uthman [Hafizahullah]