03/01/2024
Yau Shekaru 15 Da Kaddamar Da Bitcoin
A Rana Mai Kamar Ta Yau Ga 3 Ga Watan Junairu 2009 Satoshi Nakamoto ya Kaddamar da Bitcoin.
An fara wallafa Bitcoin ne a wani jerin sakonni na intanet ga masana kimiyyar komfuta da ke karantar da yadda za a iya aika sako ta intanet cikin tsaro a 2008.
Wanda ya fara wallafa shi na da wani suna na bogi Satoshi Nakamoto amma babu wani mutum ko mutane kawo yanzu da aka tabbatar shi ne Satoshi.
Mene ne Bitcoin, sannan ya ake amfani da shi?
Bitcoin wani nau'i ne na kuɗin intanet. Ba shi da siffa ta zahiri. Madadin haka, ana sayar da rukunin kuɗin a intanet da sauran shafukan sada zumunta. Ba shi da wata iyaka, ma'ana iya shafukan da za a iya amfani da su, sannan ba su da banki, kamar kudin zahiri da aka sani.
A maimakon haka, yana aiki ne a hanyoyin intanet da wasu dubban na'urori da ke hadawa da ajiye bayanan yadda ake kashe kuɗin.
Dubban na'urorin ke hana samun bayani dangane da yadda kuɗin ke shiga da fita - amma akwai wata fasaha da ake kira 'blockchain' da ke iya ba da damar gano shiga da fice kuɗin.
Blockchain bayanai ne da ake iya aikawa kan yadda aka kashe bitcoin - yana hana wani 'kashe kuɗin bitcoin sau biyu' kuma zai yi matukar wahala wani ya iya sauya bayanan shige da ficen kuɗin. Da wahala, a iya cewa ma ba zai yiwu a sauya shi ko a wawushe shi.
Ana amfani da shi har yanzu kuma a ina ake amfani da shi?
Ana amfani da Bitcoin har yanzu kuma ana sayen shi a matsayin kuɗin da ba na zahiri ba, wanda ke ba masu amfani da shi damar sauya kuɗin zahiri da aka saba da shi zuwa bitcoins.
Don amfani da Bitcoins, matakin farko shi ne bude abin da ake kira 'wallet' ko lalita (wadda ke iya zama a intanet ko a manhajar waya ko a wata na'ura mai tsaro). Wannan na kare duk wani sirri da ake amfani da shi wajen hadahadar bitcoins.
Lalitarka za ta kunshi 'adireshi' wanda yake aiki kamar lambar asusun banki sannan ana iya amfani da shi wajen karbar bitcoins. Haka kuma zai kunshi password din da ake bukata wajen aika bitcoins (ana