
06/09/2024
Yau Shekara Daya Da Rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu.
Marigayin ya rasu ne bayan jinya da yayi na 'dan lokaci a Birnin kebbi.
Sheikh Abubakar Giro fitaccen malamin addinin musulunci ne daga jihar Kebbi. An haife shi a karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi. Sheikh Abubakar Giro ya samu ilimin addinin musulunci tun yana karami. Ya fara ne da tsarin ilimin Almajiranci wanda ake kira Tsangaya a harshen Hausa wanda ya zama ruwan dare a yankin arewacin Najeriya.
Sheikh Abubakar Giro ya shiga makarantun Almajirai na cikin gida inda ya koyi karatun Alqur'ani.
Sheikh Abubakar Giro ya je kasashen ketare da dama domin neman ilmin addinin Musulunci da koyarwarsa.
Ya samu nasarar zama daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Najeriya
Tun a ranar 30 ga watan Janairu na Shekarar 2021 wasu kafafenen sada zumunta ke yawo da wani labarin karya da ke cewa Allah yayiwa Sheikh Abubakar giro Argungu Rasuwa..
Tuni dai Shafin JIBWIS na Facebook su ka bayyana cewa; wani makiyin Allah ya bada sanarwan cewa Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu, Wannan magana ta daga hankalin alβumma a fadin duniya, sannan mun kai karar wanda ya fara ruwaito wannan labari wajen Allah.
Sheikh Abubakar Giro Argungu yana Kasar Misrah neman magani, kuma baβa Asibiti yake kwance ba, a gida yake zaune domin rashin lafiyar bai kai a kwantar dashi a Asibiti ba, ko yanzu munyi magana da shi ta wayar tarho, kuma har sun fara shirya-shiryen dawowa gida Naijeriya.
Ya Allah Ya yi wa Malam Abubakar Giro Argungu Rahama AMEN π π€²