
04/09/2025
*🩸 SICKLE CELL: KADA A KASHE SOYAYYA DA HAWAYE 🩸*
Kafin aure, soyayya tana daɗi. Amma bayan aure, gaskiya tana bayyana. Sickle Cell ba cuta bace da ake ganinta da ido – tana buya a cikin jini, ta na tagayyara lafiya da kwanciyar hankali.
Ma'aurata da ba su yi gwajin jini ba kafin aure na iya haifar yara masu fama da ciwon sikila – rayuwa mai cike da wahala, jinya, hawaye da bakin ciki.
🧬 Ka san jinin ka (AA, AS, SS)?
🧪 Ka san jinin masoyiyarka?
❤️ Soyayya tana bukatar kulawa da sanin gaskiya kafin a ɗaura aure.
*Ka kare masoyinka. Ka kare zurriyarka. Ka je a yi gwajin jini kafin aure.*
Wayar da kai daga *SHALA 360 MEDIA ENTERTAINMENT* – Domin rayuwa cikin koshin lafiya da soyayya mai dorewa.