
12/01/2025
Tinubu ya sanya hannu a dokar da ta hana sojoji aikata baɗala
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan wani kundin dokoki da ya hana sojojin Nijeriya aikata dukkan nau'in baɗala da su ka haɗa da luwaɗi, maɗigo, zinace-zinace, lalata da dabbobi, daudu da sauran dangogin su da ake ganin sun saba wa ka’idojin aikin soja.
Hakazalika dokokin sun hana sojojin ƙasar huda jiki, zanen fata, rashin ɗa'a, da kuma buguwa da barasa a yayin aiki ko bayan aiki.
Wannan umarnin na kunshe ne a sashe na 26 na kundin dokokin aikin soja da aka yi wa kwaskwarima, wanda shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 16 ga Disamba, 2024.
A kwafin takardar kundin da wakilan gidan jaridu s**a samu a jiya Asabar, wani bangare na kundin na cewa, “An yi ga jami’in soja ya shiga harkar luwadi, madigo, da kuma lalata da dabba.
"Ba zai kasance cikin, ko shiga ayyukan ƴan madigo, luwadi, zina da daudanci ba, gami da shiga ƙungiyar LGBTQ ba.
“Bai k**ata jami’in soja ya riƙa huda jiki da kuma yi wa wani bangare na jikinsa zane ba. Jami'i ba zai aikata ko wanne nau'i na rashin ɗa'a, fada, ko wani aiki dai zubar masa da mutunci a idon al'umma ba. Kada jami'i ya bugu a kowane lokaci ko a lokacin aiki ko bayan tashi daga aiki."
Hakanan kuma dokokin sun haramta wa ko wanne soja shiga harkar kwartanci ko neman matan ma'aikatan da ke ƙarƙashin ofis ɗin su da sauran su.
Sai dai Rahotanni sunce ba a bayyana hukunce-hukunce ko matakan ladabtarwa ga duk wani ma'aikacin da ya karya dokokin ba.