02/11/2025
Tsara Tunani Kafin A Fara Daukar Content
Akwai wani abu mai muhimmanci da yawancin masu editing ke mantawa da shi — tunanin kafin fara Aiki
Ni kaina, kafin in fara aikin content creation ko editing, sai na fara da tunani.
Na zauna in tambayi kaina:
🧠 Me nake son na nuna?
💬 Me sako na yake nufi?
🎥 Wace irin hoto ko bidiyo ce zata bayyana ma’anar da zuciyata ke tunani?
🎧 Wanne irin editing zai sa mutane su ji abin da nake ji?
Lokacin da ka tsara tunani kafin ka fara aiki —
👉 Ka fi yin content mai ma’ana.
👉 Mutane zasu gane labarin da ke bayan hotonka ko bidiyonka.
👉 Kuma kai zaka ji daɗin abin da kake ƙirƙira fiye da da.
Kada ka fara recording ko editing ba tare da ra’ayi a kai ba.
Domin ra’ayi shi ne tushen kirkira ✨
#