16/07/2025
🚨Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar dalibai biyu na makarantar Sakandaren kwana ta gwamnati da ke Bichi.
Daliban da s**a rasu, Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa, ana zargin sun mutu ne sakamakon yadda wasu dalibai da ke ajin gaba da su su kabasu horo mai hadari da ake kira ‘Gwale-Gwale’.
Rahotanni sun ce manyan daliban ne s**a aikata wannan laifi inda s**a zargi wadanda aka kashen da aikata wani laifin da ba a bayyana ba inda s**a yanke shawarar hukunta su.
Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ta bakin babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike na gaskiya cikin gaggawa domin gano gaskiyar lamarin.
Iyalan mamatan sun roki a yi musu adalci. Malam Ibrahim Yusuf Dungurawa, dan uwa ga Umar Yusuf, ya bayyana yadda wannan labari ya rutsa da dan'uwan sa tare da yin kira ga gwamnati da ta tabbatar da adalci.
Hakazalika, Malam Idris Garba Tofawa, mahaifin marigayi Hamza Idris, a yayin da ya bayyana rashin a matsayin jarabawar Ubangiji, ya bukaci hukumomi da su yi abinda ya dace.