07/06/2026
Tsohon Kwamishinan Ma'aikatun Lafiya da Muhalli na Jihar Kano, kuma Memba a Kwamitin Gudanarwa na Jami'ar Sufuri ta Tarayya da ke Daura, Hon. Dr. Kabiru Ibrahim Getso, ya bayyana matuƙar alhini da jimami bisa rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso, tsohon Manajan Darakta na Radio Kano da ARTV.
A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka Masa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a, Aliyu Abdul Garo, ya fitar, Dr. Getso ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga al'ummar Getso, Jihar Kano baki ɗaya, da kuma fannin yaɗa labarai.
Ya ce labarin rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso ya girgiza shi matuƙa, tare da haifar da babban gibi da zai yi matuƙar wahalar cikewa, la'akari da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban al'umma da hidimomin jama'a a tsawon rayuwarsa.
Dr. Getso ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari, mai ba da shawara, gogaggen mai gudanarwa, kuma uba ga al'ummar Getso, wanda hikimarsa, nagartarsa, da jajircewarsa wajen cigaban al'umma s**a sanya ya samu girmamawa da karramawa daga jama'a daban-daban.
Ya ce, "Na yi matuƙar alhini da jin rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso. Wannan babban rashi ne ga al'ummarmu da ma jihar Kano baki ɗaya. Marigayin ba kawai ginshiƙi ne ga iyalansa ba, ya kasance uba, jagora, kuma abin koyi ga al'ummar Getso baki ɗaya. Gudunmawar da ya bayar a fannin yaɗa labarai, cigaban al'umma da gina ɗan Adam za su ci gaba da kasancewa abin tunawa har abada."
A madadinsa, iyalansa, magoya baya da masoyansa, Dr. Getso ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, Dagacin Getso Alhaji Bello Ibrahim (San Getso), al'ummar garin Getso, abokai da masu ruwa da tsaki, tare da daukacin al'ummar Jihar Kano bisa wannan babban rashi.
Ya kuma bayyana cewa marigayi Alhaji Adamu Ibrahim Getso ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al'umma hidima, inganta walwalar jama'a, da bunƙasa harkokin yaɗa labarai, inda ya bar kyakkyawan tarihi da za a ci gaba da alfahari da shi tsawon lokaci.
Dr. Getso ya ƙara da cewa, "Babu shakka rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso babban rashi ne ga al'ummar Getso da karamar hukumar Gwarzo baki ɗaya. Tarihin rayuwarsa na gaskiya, riƙon amana, shugabanci nagari da hidimtawa jama'a zai ci gaba da zama abin koyi ga masu zuwa bayansa."
Daga ƙarshe, ya yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya yafe masa kura-kuransa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa, 'yan'uwansa da daukacin masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Aliyu Abdul Garo
07 June 2026
Sunday.