Labaran Kano da Kewaye

Labaran Kano da Kewaye News and media

11/10/2022
16/08/2022

Wadan nan bata gari ne da kuma wadan da ake zargi da aikata munanan laifuka wanda akayi holin su a shedkwatar yan Sanda ta Bamfai dake Kano.

Breaking News...Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya aiko da sunayen mutum 8 zuwa majalisar dokoki ta jiha ...
15/08/2022

Breaking News...

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya aiko da sunayen mutum 8 zuwa majalisar dokoki ta jiha Kano domin tantance su da tabbatar da su a matsayin Kwamishinoni kuma yan majalisar zartarwa na Jihar Kano.

Ga sunayen k**ar haka:

1. Alh Ibrahim Dan Azumi Gwarzo
2. Abdulhamid Abdullahi Liman
3. Hon lamin sani Zawiyya
4. Rt. Hon ya'u Abdullahi yan'Shana
5. Hon Garba Yusuf Abubakar
6. Dr Yusuf Jibrin Rurum
7. Hon Adamu Abdul Panda
8. Alh Saleh kwasaimi.

08/08/2022

Takaitaccen tarihin Alh. Aliko Dangote.

Hukumar dake kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA tayi nasarar  cafke wani matashi yana sojan-gona da s...
04/08/2022

Hukumar dake kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA tayi nasarar cafke wani matashi yana sojan-gona da sunan shi Jami'in hukumar KAROTA ne.

A cewar mai taimakawa shugaban hukumar kan harkokin kafafen yada labarai na zamani, Ayuba Jarumi, KAROTA ta cafke matashin ne karfe 12 na daren litinin dai-dai lokacin da yake tsaka da tare motoci akan t**i yana karbar kudi.

Matashin mai suna Lukman Abdullahi mai shekaru 27 mazaunin unguwar Sabon Gari bayan k**a shi ya bayyanawa Hukumar Karota cewar shi ɗan Maiduguri ne.

Inda ya kara da cewa yana amfani da kayan ne saboda jama'a su fahimci shi ma'aikacin hukumar karota ne.

Dama chan Hukumar ta jima tana samun Rahoton yadda matashin yake amfani da sunanta wajen Musgunawa al'ummar Jihar kano, wanda sai a wannan karon dubunsa ta cika.

Daga karshe shugaban Hukumar ta KAROTA Hon. Dr. Baffa Babba Ɗan'agundi ya shawarci al'umma da su cigaba da kai rahoton duk wani jami'in da s**a ga yana karɓar cin-hanci domin ya fuskanci tuhuma.

Ya kumace da zarar Hukumar tkammala binke akansa zasu miƙa shi hannun jami'an Yansanda domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar tuhuma.

KanoCutar Kwalara tak**a mutane 189 a kanan hukumomi 20, Ta Kashe Mutum 5
19/07/2022

Kano
Cutar Kwalara tak**a mutane 189 a kanan hukumomi 20, Ta Kashe Mutum 5

An tsinci wannan gawar a ruwan da akayi na ranar lahadi. Yarinya ce yar kimanin shekaru 15. Idan an samu yan uwan sai a ...
19/07/2022

An tsinci wannan gawar a ruwan da akayi na ranar lahadi.

Yarinya ce yar kimanin shekaru 15. Idan an samu yan uwan sai a kira DPO na Zaria Road Division akan 08067298020.

: Bashir DURUMIN IYA Radiyo

KARIN FARISHIN MAN FETURAn kara farashin kudin man fetur a Najeriya zuwa sama da Naira 165 a sassan kasar, kuma gwamnati...
19/07/2022

KARIN FARISHIN MAN FETUR
An kara farashin kudin man fetur a Najeriya zuwa sama da Naira 165 a sassan kasar, kuma gwamnati ce ta bada umarnin daukar matakin k**ar yadda masu hada-hadar man s**a ce, yayin da farashin ya fi tsada a arewacin kasar.

A wata majiyar Shugaba Buhari yace yanzu kamfanin NNPC yan hannun yan Kasuwa.

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta Zirga-Zirgar Babur din Adaidaita Sahu daga karfe 10 na dare zuwa safiya.Cikin wata sanar...
18/07/2022

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta Zirga-Zirgar Babur din Adaidaita Sahu daga karfe 10 na dare zuwa safiya.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada Labarai Muhammad Garba ya sanyawa hannu, yace an dau matakinne dan inganta harkokin Tsaro a Kano.

Jaridar Daily News 24 ta wallafa Labarin.

Gwamnatin Kano Ta Rufe Kwalejojin Kimiyyar Lafiya Da Fasahar 26. Rahma Media Group July 15, 2022.Gwamnatin jihar Kano ta...
16/07/2022

Gwamnatin Kano Ta Rufe Kwalejojin Kimiyyar Lafiya Da Fasahar 26.
Rahma Media Group July 15, 2022.

Gwamnatin jihar Kano ta rufe kwalejojin fasahar kiwon lafiya masu zaman kansu guda 26 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na jihar.

Yaduwar makarantun a baya-bayan nan, a cewar jihar, yana da illa ga lafiyar jama’a, ci gaban ilimi da kuma ingantaccen tsarin kiwon lafiya baki daya.

Ga jerin sunayen makarantun da aka rufe:

Unity College of Health Science & Technology Dorayi Karama (K.G/Mai), Gwale LGA Danbatta LGA.
Khalil College of Health Science & Technology Zaria Road, Opp Gadar Lado Darmanawa
Unguwa Uku Opp. Hisbah Office, Karkasara, Opp. Bilal Mosque, Tarauni LGA; Danbatta LGA; Wudil LGA
Shamila College of Health Science & Technology Gezawa LGA
Autan Bawo College of Health Science & Technology Rano LGA
Trustee College of Health Science & Technology Jakara, Dala LGA – Kano
Bachirawa, Ungoggo LGA – Kano
Eagle College of Health Science & Technology, Bichi LGA
Albakari College of Health Science & Technology, Rijiyar Zaki, Ungoggo LGA – Kano
Jamatu College of Health Science & Technology, Kura LGA
Savanna College of Health Science & Technology, Wudil LGA
Institute of Health Education
Ahmadiyya, Opp. INEC Office
Jamilu Chiroma College of Health Science & Technology
Kings-Garden, Zungeru road, Opp. Airport Road, S/Gari
Sir Sanusi College of Health Science & Technology
Matan Fada Road
Aminu Ado Bayero College of Health Science & Technology
Ado Bayero Layout, Dandinshe Yamma – Dala LGA
Awwab College of Health Science & Technology, Salanta, Gwale LGA
Gwarzo Unity College of Health Science & Technology, Gwarzo LGA
Al-wasa’u College of Health Science & Technology, T/Fulani, Nassarawa LGA – Kano
Kanima Academy, Layin Dan-kargo, Zangon Dakata, Nassarawa LGA – Kano
Muslim College of Health Science & Technology, Zungeru Road, Fagge LGA – Kano
Utopia College of Health Science & Technology, Jigirya JSS, Yankaba, Nassarawa LGA – Kano
Jama’a College of Health Science &

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ce zata rufe rijistar katin zabe ranar 31 ga watan Yuli, 2022, bayan Kotun tarayya ...
15/07/2022

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ce zata rufe rijistar katin zabe ranar 31 ga watan Yuli, 2022, bayan Kotun tarayya ta yanke hukunci.

Duk da Kotu ta yi fatali da ƙarar, INEC ta ce ta ƙara wa'adin mako biyu bayan ƙarin kwana 15 da ya kare, zata rufe karshen wata.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labaran Kano da Kewaye posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Labaran Kano da Kewaye:

Share