01/11/2022
YADDA ZA KA SAMU CORE TESTNET GUDA DAYA KULLUM......
Da farko dai sanin kowa ne MetaMask Wallet shine Wallet din da Core Team na Core Dao(Satoshi btcs)s**a yarda kuma s**a Amince a yi Gwajin gar da gar na Testnet,don gujewa Hasara a lokacin da za su dora Coin na su a kan Babban Dandalin su na Hada Hada(Mainnet),kuma sun Umurci dukkan wadda ya ke Mu'amala da Core Coin ya je yayi Gwajin gar da gar na Testnet.
A kullum ko wanne Miner yana da kyautar Coin guda daya na Testnet,sai dai idan ba ka je ka karba ba,ko ba ka san yadda ake karba ba,INSHA ALLAHU,Wannan rubutun zai gwada maka yadda za ka samu kyautar Coin daya kullum domin Gwaji na Transaction a kan Dandalin su na Gwaji,har ka saba da yadda Abin ya ke don kada a samu Hasarar Dukiya lokacin Mainnet ko kuma bayan Mainnet.
Allah ya sa mu Amfana da wannan Project din ya sa shine Sanadiyyar Qwato Kawunan mu daga Talauchi,donTalauchi Annabi s.a.w ma yayi Addu'ar Allah ya raba shi da Talauchi,don mu ma mun yi ba Laipi ba ne,Sunnah ce muka bi.
MATAKAN DA ZAKA BI SUNE:-
1. Kamar yadda na nuna a wadannan Hotunan,Za ka bude MetaMask Wallet na ka zai nuna maka Shafin Farko wadda shine Wallet na ka,sai ka duba sama chan Qololuwa ta bangaren Hagu Akwai wassu Layuka a kwance guda uku,sai ka taba su,kana taba su zai kai ka ga Mataki na biyu wadda shine.....
2. Hoto na biyu "View on Scan" sai ka taba wajen,kana taba wa zai yi Search ya kai ka kan Shafi na 3,wadda shine.......
3. Shine wajen da za ka yi Copy din Wallet Address na ka,idan ka lura na sanya Kibiya a kan wajen,kawai tabawa za ka yi,shikenan Wallet Address na ka yayi Copy,ka gama da wajen,sai kuma Mataki na 4........wadda shine.....
4. Faucet:- Za ka tura Wayar ka (Scroll) zuwa qasan shafin ,nan za ka ga(Faucet)Faucet a nan ne za ka samu Kyautar Coin din Gwaji na gar da gar wato Testnet,kana taba shi zai nuna maka yana Search,idan ya bude,zai kai ka shafi na 5,6,7,wadda a nan ne Asalin Aikin ya ke,k**ar yadda Kibiyoyin s**a nuna,a wajen da aka sa "Input your Core Chain Address,dogon Akwati ne a kwance sai ka taba shi daga farko,za ka ga wata sanda ta fito,a gefen sandar ko ta dama ko ta hagu sai ka danna hannun ka na tsawon second 2 zuwa 3 kawai sai ka daga,da ka daga za ka ga kalmar nan ta "Paste" ta bayyana a saman Akwatin,kwai sai ka taba ta,kana taba ta,za ka ga Wallet Address na ka ya bayyana a ciki,sai ka dawo lambar ta 6,Qaramin Akwati ne mai k**a da gidan Dara(Square)sai ka taba shi,wajen da aka sa "'I'm not a Robot" wato "ni ba Mutum Mutumi ba ne"