20/08/2023
Takanolaji kenan...!
Wannan hoton da kuke gani, Photo Album ne, wasu dalibai s**a karɓo shi daga hannun wani Bawan Allah da zai musu Physical Photo Album (Na Littafi 📖).
Tun lokacin da wani Monita na wata makaranta yaga sample na "Online Photo Album" da muke yi, a lokacin yayimin message ta WhatsApp muka fara magana, na cewar 'suna so suma a kirkirar musu Digital Album'.📱
But, a lokacin da yake min maganar already sun kai ayi musu na littafi. Monitan yake cewa su zasuje gun wancan mutumin idan har baiyi ba, kawai ya basu kudin su (but, already mutumin ma ya gama komai, printing kawai ya rage ya fara musu), tunda dai yanzu anayin wannan abun a zamanance.🌐
Ganin yanda zai zamto a cikin waya, ga shi kuma za'a dora a Playstore (duk inda mutum yake a fadin duniya zai samu access da shi), kuma ko da shekara nawa za'ayi ko wani class member zai iya samun Colleagues dinsa cikin sauki 👥, bugu da kari ga tarin features a wannan application na ONLINE PHOTO ALBUM da za ayi musu.🤹🏽♂️
To cut the story short, a yanzu dai aikin da aka bawa wancan na samar da Physical Photo Album ya dawo hannun mu, mu masu Online Photo Album.🤳🏼
KU SANI: Babu sa hannun Haruna a warto wannan aikin, laihin Takanolaji ne🤌🏼, yauwa. 🙄
_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_
Wani kallo kuke yiwa ONLINE PHOTO ALBUM dinnan, shin zai iya maye gurbin Physical Photo Album (Wanda akeyi na littafi)❓