27/07/2024
Ƙungiyar masoya sarkin kano mai suna"Muhammadu Sanusi II legacies inivative"ta rabawa mabukata mutum 400 kayan sawa, magunguna dakuma maganin sauro
Ƙungiyar masoya sarkin kano Khalipa Malam Muhammadu Sanusi II wato"Muhammadu Sanusi II legacies inivative" ta gudanar da rabon kayan sawa magunguna dakuma maganin sauro ga mabukata mutum 400 a karamar hukumar Warawa dake jihar Kano.
taron rabon kayan ya gudane a asabar dinnan 27/7/2024 a Islamic center dake karamar hukumar Warawa ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na kasa Najeriya Usman Aminu Sulaiman.
Ƙungiyar ta rabawa mabukata mata,maza da yara kanana mutum 100 kayan sawa inda ta rabawa mutum 200 dake fama ciwon maleria, zazzabi hawan jini dakuma gudawa magunguna bayan da kwararan likitan da taje dashi Dr Khalipa Muhammadu ya gwada wasu daga cikin mutunan.
Haka kuma ta rabawa mutum 100 maganin sauro na kunnawa domin kare kansu daga cizon sauro.
Kazalika,yayin taron anyi jawabin wayar dakai kan yadda iyaye mata zasu kare kansu daga kamuwa da cututuka wanda,Amina Yahaya Muhammad ta gudanar da jawabin.
Taron rabon kayan yasamu hallatar shugaban karamar hukumar Warawa da wakilcin maigirma magajin Garin Kano, Alhaji Muhammad Nasiru Inuwa Wada ,dakuma wakilcin Hakimin karamar hukumar Warawa mai girma,Dan Isan Kano.
Ƙungiyar Muhammadu Sanusi II legacies inivative kungiya ce da masoya sarkin kano s**a kafata shekaru 5 biyar dasu gaba inda suke gudanar da aiyyukan taimakon al'umma a karan kansu domin yin koyi da kyawawan halin sarkin kano Khalipa Malam Muhammadu Sanusi II.
Rubutawa
Umar Saleh Zara, Daraktan yada Labaran ƙungiyar na Najeriya.