
03/11/2023
Muna Kira ga Yan'majalisar jaha da na tarayya da sanatoci da ministota Yan Arewa da su shiga duk inda ya dace su fada domin a bude bodar Nigeria-Niger.
Haka ma, Muna Kira ga Mai girma shugaban kasa da ya sa a bude Mana bododi Kamar yadda na kudu suke a bude, domin a halin yanzu Yan kasuwarmu na Arewa ke fuskantar kariyar tattalin arziki su Kuma na kudu a cikin walwala suke, yin haka shi ne adalci.
Rufe boda ba ra'ayin Yan kasa bane, an yi ne domin Kare muradun wata kasa da take ganin yin juyin mulki a wata kasa zai hana ta samun abunda ta Saba samu.
~ Inji Prof. Muhammad Sani Umar R/lemo.
Copied from Comrd Abba Sani Pantami