05/08/2025
ABIN FARIN CIKI: Matashiya Daga Jihar Yobe Tayi Nasarar Lashe Gasár Turanci Bayan Doke ƙasashe 69 Na Duniya .
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Nafisa Abdullahi Aminu kenan, matashiyar yar shekaru 17 wacce ta fito daga jihar Yobe, ta makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC) Yobe, ta wakilci Najeriya inda tayi nasarar doke ɗalibai kimanin Dubu ashirin, waɗanda s**a fito daga ƙasashe 69, ciki waɗannan ƙasashe akwai waɗanda Harshen Turanci shine Yarensu na Asali.
Nafisa ta cancanci kowacce irin girmamawa dakuma Karramawa, k**a daga gwamnatin tarayya dakuma gwamnatin jiha.
Wannan abin farin ciki ne ga yankin Arewa, kuma abin alfahari ne, domin wannan ya ƙara nuna yadda yankin Arewa yake da mutane masu hazaƙa dakuma baiwa, idan har aka inganta harkar ilmi tabbas babu matsayin da yan Arewa bazasu kai ba.
Abin taƙaicin shine a wajen al'ummar Arewa wannan ba abin yaɗawa bane, lokuta dayawa anfi maida hankali akan abinda Bashine damuwar Arewa ba.
Allah yaƙara Basira nafisa, Allah yaƙarawa Yaranmu hazaƙa, kuma ya kawo lokacin da za'a inaganta harkar ilmi a yankin Arewa, dama ƙasa baki ɗaya.