
27/07/2025
Gaza: Falasɗinawa Sun Fara Samun Kayan Agaji Bayan Watanni 6
Daga { Abubakar Bashir Adam Yakasai}
Bayan kusan watanni shida da dakatar da kai kayan agaji zuwa Gaza, rahotanni sun tabbatar da cewa an fara shiga da kayan tallafi zuwa yankin a yau Lahadi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Falasɗinu ke ci gaba da fama da mummunar matsalar jin ƙai sakamakon rikicin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Hamas, wanda ya janyo tsananin karancin abinci, magunguna da sauran kayan bukatu.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa motoci dauke da kayan abinci da magunguna sun samu damar shiga wasu sassan Gaza, lamarin da ya tayar da ƙwarin gwiwa ga dubban fararen hula da s**a shafe watanni cikin tsananin bukata.
Tun bayan da rikicin ya kazance a watan Oktoba, an dakatar da yawancin hanyoyin kai agaji, musamman daga iyakar Rafah, lamarin da ya janyo s**a daga kungiyoyin agaji da na kare hakkin bil’adama.
Har yanzu dai akwai bukatar karin kayan agaji domin biyan bukatun dimbin mutane da ke cikin halin matsi a Gaza. Kungiyoyin jin kai na duniya sun ce matakin bude hanya na yau babban cigaba ne, amma suna kira da a bude dukkan hanyoyin agaji gaba ɗaya ba tare da wani jinkiri ba.