Tambarin Hausa TV

Tambarin Hausa TV Labarai da Shirye-Shirye na yau da kullum daga Gidan Talabijin na kasa da kasa mai yada shirye-shirye

01/12/2025

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na samar da daidaito a aikin jarida a faɗin jihar.

TAƁARBAREWAR TSARO: SHUGABA TINUBU YA AYYANA MATAKAN GAGGAWA A FAƊIN ƘASA. Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a bang...
26/11/2025

TAƁARBAREWAR TSARO: SHUGABA TINUBU YA AYYANA MATAKAN GAGGAWA A FAƊIN ƘASA.

Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a bangaren tsaro a faɗin ƙasa saboda tabarbarewar yanayin tsaro a jihohi da dama. Ya umarci rundunar Soja da ‘Yan Sanda su ɗauki jami’ai 20,000 ƙarin ma’aikata, a kan 30,000 da aka amince da su tun da farko, jimilla yanzu 50,000 kenan.

Tinubu ya kuma umurci a mayar da sansanonin masu bautar ƙasa (NYSC) a faɗin ƙasar, matsayin cibiyoyin horaswa na 'yan sanda, sannan jami'an tsaro na manyan mutane (VIP guards) da aka janye, su koma samun horo domin tura su wuraren da ke cikin haɗari.

Bugu da ƙari, Tinubu ya umarci DSS da ta hanzarta tura masu gadin dazuka, tare da ƙarin daukar ma’aikata domin fatattakar ‘yan ta’adda da ‘yan fashi.

Shugaban ya kuma bayyana cewa zai goyi bayan kowace jiha da ta kafa rundunar tsaro ta musamman, sannan ya bukaci Majalisar Dokoki ta fara aiki kan batun ‘yan sandan jihohi (state police).

Ya kuma yi kira ga makiyaya su daina kiwo a bayyane (ta cikin labika), su koma tsarin killace dabbobin wuri daya, tare da miƙa dukkan makaman da ba bisa ka’ida ba.

A ƙarshe, Tinubu ya yi ta’aziya ga iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu a hare-haren baya-bayan nan, da kuma sojojin da s**a mutu, ciki har da Brig.-Gen Musa Uba.

18/11/2025

Majalisar Sarakuna.

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin mai girma Gwamna Abba Kabiru Yusuf, ta kaddamar da majalisar sarakuna a faɗin jihar.

13/11/2025

Gwamna Abba Na Jihar Kano ya gargadi rukuni na biyu na daliban da aka tura kasashen waje domin karo karatun digirinsu na biyu kan su guji shiga zanga-zanga da hana kansu yin ta'ammali da miyagun kwayoyi.

05/11/2025

Gwamnan Jihar Kano ya kalubalanci bankuna da su rika bai wa al’umma rance mai sauƙin biya.

04/11/2025

Kimanin sama da ‘yan daba 1,600 ne s**a tuba a Jihar Kano, yayin da ake sa ran tantance wasu fiye da 2,000 a cikin wannan watan.

31/10/2025

Biyo bayan yawaitar mace-mace da ake samu, Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ta gudanar da horo ga jami’an ‘yansanda guda 100 a jihar, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta aikin ceton rayuka.

29/10/2025

Kimanin sama da shekaru 70 kenan wato tun zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, rabon da ayi bikin kalankuwa a jihar Kano, sai a bana.

24/10/2025

Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga iyaye mata da su riƙa shayar da jariransu nonon uwa kawai tun daga haihuwa har tsawon watanni shida, ba tare da an ba su ruwa ko wani abin sha ba.

20/10/2025

Tsoffin manyan mashawarta da mataimaka na musamman sun kai kuka ga Eng Abba Kabir Yusuf kan kin biyansu hakkokinsu da gwamnatin Ganduje ta ki.

07/10/2025

Gwamna Abba Kabiru Yusuf, ya yi alkawarin tura kansiloli na kananan hukumomi da kuma masu baiwa shugabannin kananan hukumomi shawara, yin bita ta kwanaki biyu wajen jihar Kano.

Gwamnan ya yi wannan jawabi lokacin da ya gana da masu ruwa da tsaki na sabuwar ƙungiyar "Abba Keep Moving" a ɗakin taro na Coronation da ke fadar gwamnatin jihar.

Cikakken rahoton cikin bidiyon da ke ƙasa. 👇

06/10/2025

Kwamitin tsofaffin ƴan jarida a Kano ya miƙa rahoto ga gwamnati kan yadda za a inganta aikin jarida a fadin jihar.

.

Address

No. 75 Club Road
Kano
700281

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tambarin Hausa TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share