Fasihiya

Fasihiya Labaran Hausa Rahotanni, Adabi bunkasa aikin fasaha.

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya Ministan Yaɗa Labar...
30/09/2026

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masu watsa shirye-shirye da su tabbatar da sahihanci, adalci da bin ƙa’idojin aikin jarida wajen gudanar da rahotanni yayin da Nijeriya take tunkarar zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa watsa shirye-shirye cikin ɗa’a yana da matuƙar muhimmanci wajen kare dimokiraɗiyya.

Mai Taimaka wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabiu Ibrahim, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Ya ce ministan ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a Bauchi, a cikin jawabin da Darakta-Janar na hukumar gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace, ya gabatar a madadin sa a taron ƙasa na shekara-shekara karo na uku na Society of Nigerian Broadcasters (SNB).

Idris ya ce irin faɗin tasirin kafafen watsa shirye-shirye ya ɗora wa masu aikin wannan fanni nauyin ƙwarewa na tabbatar da cewa bayanan da suke gabatar wa da jama’a sahihai ne, an tantance su, kuma an gabatar da su cikin mahallin da ya dace.

Ya ce, “Duk da haka, bai k**ata a fahimci watsa shirye-shirye cikin ɗa’a a matsayin watsa shirye-shirye masu goyon bayan wani ɓangare ba. Kafafen yaɗa labarai masu ƙwarewa dole ne su ci gaba da tambayar gwamnati, jam’iyyun siyasa, ’yan takara da hukumomin gwamnati. Dole ne su gudanar da bincike, su tantance, sannan su ɗora alhakin ayyukan su a kan waɗanda ke riƙe da muƙaman da ke da alhaki.”

Ministan ya buƙaci masu watsa shirye-shirye da su bambanta tsakanin gaskiya, zarge-zarge, ra’ayoyi da iƙirarin da ba a tantance su ba, musamman a wannan lokaci da ƙirƙirarrar fasaha basira (AI) da kafafen sada zumunta suke sauƙaƙa yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma abubuwan da aka sauya ko aka ƙirƙira.

Ya ce, “Ba za a ɗauki tantance sahihancin bayanai a matsayin wani abu da ake yi lokaci-lokaci a ɗakin labarai ba; dole ne ya kasance ginshiƙin aikin watsa shirye-shirye na ƙwararru.”

Idris ya ce dole ne masu watsa shirye-shirye su guji kalaman ƙiyayya, tunzura ƙabilanci da addini, da kuma yaɗa bayanan ƙarya da gangan a lokacin zaɓen 2027, tare da ci gaba da samar da damar gudanar da sahihin muhawara da s**a.

Ya ce, “Gasar siyasa wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya, amma bai k**ata a bari ta zama sanadin tunzura jama’a, kalaman ƙiyayya, tunzura ƙabilanci ko addini, ko kuma yaɗa bayanan ƙarya da gangan ba.”

Bugu da ƙari, Ministan ya bayyana irin jarin da Gwamnatin Tarayya take zubawa a ɓangaren watsa shirye-shirye, ciki har da dandalin 'Digital Switch Over' (DSO) da kuma shirin zamanantar da NTA, FRCN da VON.

Ya ce, “Fasaha ce za ta tsara makomar harkar watsa shirye-shirye, amma amincin da jama’a za su yi da ita zai ci gaba da dogaro ne da mutane.”

Ya buƙaci SNB da masu watsa shirye-shirye da su ƙara ƙarfafa horas da ma’aikata, musamman kan rahotannin zaɓe, tantance sahihancin bayanai da kuma matakan daƙile yaɗuwar bayanan ƙarya da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI.

Tinubu ya dawo Najeriya bayan hutun makonni uku a Birtaniya da FaransaShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya b...
30/09/2026

Tinubu ya dawo Najeriya bayan hutun makonni uku a Birtaniya da Faransa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya bayan shafe makonni uku yana hutun aiki a ƙasashen Birtaniya da Faransa. Dawowar shugaban ƙasar na zuwa ne bayan ya kammala hutun da ya yi a waɗannan ƙasashe biyu na Turai.

Tinubu ya fara hutun ne a ranar 30 ga Agusta, 2026, inda ya fara sauka a birnin Landan na Birtaniya kafin daga bisani ya wuce birnin Paris na Faransa. A yayin zamansa a Faransa, ya gana da Shugaba Emmanuel Macron da ɗan kasuwa Vincent Bolloré.

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Tinubu ya ci gaba da bibiyar al’amuran Najeriya tare da bayar da umarni kan gudanar da ayyukan gwamnati a lokacin hutun nasa.

28/09/2026

Bidiyo:🎥

Yadda aka gudanar da addu’o’i na musamman ga Najeriya yayin Sallar Juma’a, a babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, domin murnar cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, a jiya Juma’a, 25 ga Satumba, 2026.

Muhimman Abubuwan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Gabatar a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Wanda Mataimakinsa Kashim Sh...
25/09/2026

Muhimman Abubuwan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Gabatar a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Wanda Mataimakinsa Kashim Shettima Ya Karanta

1. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da ƙudurin Najeriya na ci gaba da amfani da diflomasiyya, haɗin gwiwa da dokokin ƙasa da ƙasa, maimakon tilastawa, ware ƙasashe ko amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.

2. Ya yi kira da a gaggauta gyara Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC), yana mai cewa tsarin rarraba iko na shekarar 1945 bai dace da yanayin duniya na shekarar 2026 ba.

3. Najeriya ta buƙaci Afirka ta samu aƙalla kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaro, tare da cikakken haƙƙi da nauyin da ke tattare da kasancewa mamba na dindindin, ciki har da ikon amfani da veto, matuƙar ana ci gaba da amfani da wannan tsarin, da kuma kujeru biyar marasa dindindin.

4. Tinubu ya bayyana shirye-shiryen Najeriya na ƙara taka rawa a harkokin duniya, bisa dogon tarihin ƙasar wajen wanzar da zaman lafiya, sasanci da ayyukan tsaro a Afirka.

5. Ya danganta manufofin harkokin wajen Najeriya da gyare-gyaren tattalin arzikin cikin gida, yana mai jaddada muhimmancin ingantaccen tsarin tafiyar da tattalin arziki, ƙarfafa hukumomi, saka hannun jari da bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu.

6. Najeriya ta yi watsi da ra’ayin cewa dole ƙasashe masu tasowa su zaɓi tsakanin ci gaban tattalin arziki da yaƙi da sauyin yanayi. Ta ce ya k**ata ƙasashe masu tasowa su samu damar bunƙasa masana’antu, rage talauci da faɗaɗa samar da mak**ashi ta hanyoyin da s**a dace.

7. Tinubu ya yi kira da a samar da tallafin kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, fasaha da ƙwarewa, bisa adalci da kuma la’akari da nauyin da ya rataya kan kowa.

8. Najeriya ta sake jaddada Energy Transition Plan da burinta na cimma net-zero nan da shekarar 2060, ta hanyar amfani da mak**ashi mai sabuntawa, tsaftataccen girki, iskar gas a matsayin mak**ashin miƙa mulki, noma mai la’akari da sauyin yanayi da kuma hanyoyin kare muhalli.

9. Tinubu ya yi kira ga duniya da kada ta bari tsoron Artificial Intelligence (AI) ya hana amfani da damar da fasahar ke da ita wajen inganta kiwon lafiya, ilimi, noma, shugabanci da tattalin arziki.

10. Najeriya ta gayyaci ƙasashen duniya su haɗa gwiwa da matasanta a fannin fasaha da kirkire-kirkire, tare da ƙara saka hannun jari a harkokin dijital, broadband, bincike da kasuwancin fasaha.

11. Tinubu ya yi kira da a yi sauyi mai zurfi a tsarin kuɗaɗen duniya, tare da samar da sauƙaƙan rance da tsarin kula da basuss**a da zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar saka jari a ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

12. Najeriya ta bayyana African Continental Free Trade Area (AfCFTA) a matsayin muhimmin ginshiƙi na sauya tattalin arzikin Afirka, tare da kira ga nahiyar ta daina dogaro da fitar da albarkatun ƙasa kawai, ta mayar da hankali kan ƙara musu daraja, masana’antu, kirkire-kirkire da tattalin arzikin da ilimi ke jagoranta.

13. A fannin tsaro, Najeriya ta yi kira da a ƙarfafa musayar bayanan sirri, dakile hanyoyin samar da kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci da safarar mak**ai ba bisa ƙa’ida ba. Ta kuma jaddada muhimmancin ilimi, damar tattalin arziki, shugabanci na gari da kare haƙƙi da mutuncin al’umma wajen magance matsalolin tsaro.

14. Tinubu ya yi kira da a gaggauta amfani da diflomasiyya wajen magance rikice-rikice, musamman a Sudan, tare da kare fararen hula, tabbatar da isar da agajin jin ƙai da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.

15. Najeriya ta bayyana ƙudirinta na fifita haɗin gwiwa maimakon faɗa, tattaunawa maimakon rarrabuwar kai, fata maimakon tsoro, da haɗin gwiwa maimakon warewa, tana mai jaddada cewa Majalisar Ɗinkin Duniya mai gyara, haɗa kowa da inganci na da muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, adalci da ci gaba mai ɗorewa a duniya.

HOTUNA:Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa, ya halarci Sallar Juma’a tare...
25/09/2026

HOTUNA:
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa, ya halarci Sallar Juma’a tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, da sauran manyan baki, a Babban Masallaci na Ƙasa da ke Abuja, a yau 25 ga Satumba, 2026, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

Yadda Aka K**a Manyan ’Yan Ta’adda, Ba Tare Da Harba Ko Harsashi Ɗaya Ba – Minista IdrisGwamnatin Tarayya ta ce inganta ...
25/09/2026

Yadda Aka K**a Manyan ’Yan Ta’adda, Ba Tare Da Harba Ko Harsashi Ɗaya Ba – Minista Idris

Gwamnatin Tarayya ta ce inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na leƙen asiri ya taimaka wajen k**a ɗaya daga cikin ’yan ta’addan da aka fi nema a duniya, Mamuda, tare da babban mataimakinsa, ba tare da an yi harbi ba.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake amsa tambayoyi kan halin da tsaron ƙasar ke ciki a wani taron manema labarai na duniya gabanin bikin cikar Nijeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Idris ya ce k**a waɗannan mutane na nuna yadda musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro ke ƙara inganta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Tun lokacin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mun ga ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na leƙen asiri. Wannan ya taimaka wajen k**a ɗaya daga cikin ’yan ta’addan da aka fi nema a duniya, wato Mamuda, tare da babban mataimakinsa. A yau, Mamuda da babban mataimakinsa suna fuskantar shari’a,” in ji shi.

Ministan ya ƙara da cewa waɗannan waɗanda ake zargi, waɗanda ya ce Amurka da wasu ƙasashen Turai sun sanya kuɗaɗen lada domin a kamo su, an k**a su ba tare da an harba ko harsashi ɗaya ba.

“Waɗannan mutane ne da hatta ƙasashe irin Amurka da na Turai s**a sanya kuɗaɗen lada domin a kamo su. Amma a yau, an k**a su ba tare da an harba ko harsashi ɗaya ba.

“Wannan alama ce ta irin haɗin gwiwa, aiki tare da musayar bayanan sirri da ke gudana tsakanin rundunonin soji da hukumomin leƙen asiri, wanda ke ƙara inganta yadda ake tunkarar waɗannan miyagun mutane,” in ji Idris.

Sai dai ministan ya amince cewa har yanzu ƙasar ba ta shawo kan dukkan matsalolin tsaro ba, yana mai cewa ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuka na ci gaba da zama abin damuwa.

Ya ce Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa rundunonin sojin ƙasar ta hanyar samar da ƙarin kayan aiki da na’urorin yaƙi, tare da kusantar da sojoji zuwa wuraren da ake gudanar da ayyukan tsaro.

Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ƙara yawan rundunonin sojin ƙasa daga takwas zuwa 12.

Ya ce, ƙarin rundunonin na da nufin tabbatar da cewa sojoji suna kusa da wuraren da ake buƙatar gudanar da ayyukan tsaro, maimakon su riƙa yin doguwar tafiya kafin su isa wuraren da ƙungiyoyin masu aikata laifuka suke.

“Dukkan wannan ana yin sa ne domin a kusantar da rundunonin soji zuwa wuraren da ake gudanar da ayyuka, ta yadda ba za su riƙa yin doguwar tafiya ba kafin su tunkari waɗannan miyagun mutane da kuma ’yan bindigar da ke wahalar da rayuwar jama’a,” in ji shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da ware kuɗaɗen sayen ƙarin kayan aiki da na’urorin yaƙi ga Rundunar Sojin Ƙasa, Rundunar Sojin Ruwa da Rundunar Sojin Sama.

Ya ce, wasu daga cikin kayan aikin, ciki har da jiragen yaƙi masu saukar ungulu da sauran kayan aikin soji, ana kawo su ne yanzu bayan an yi odarsu tun ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata, yana mai cewa irin waɗannan sayayya na ɗaukar lokaci mai tsawo saboda matakan da ake bi.

Idris ya ce gwamnati ta kuma amince da inganta jin daɗi da albashin jami’an rundunonin soji, yana mai bayyana matakin a matsayin wani abin ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin ta kuma ƙara kaimi wajen inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na leƙen asiri, a wani ɓangare na ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da rayuwa yadda ya k**ata a al’ummomin da matsalar tsaro ta shafa.

“Wannan ba yana nufin mun magance dukkan matsalolin tsaro ba ne. Gwamnati ba ta taɓa cewa an kawo ƙarshen dukkan matsalolin tsaro ba. Amma muna kan hanyar kawo ƙarshen wannan matsala baki ɗaya,” in ji shi.

Ministan ya kawo sauƙin zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna a matsayin misalin ci gaban da aka samu a fannin tsaro, yana mai cewa zirga-zirga a wannan hanya ta fi sauƙi idan aka kwatanta da shekarun baya.

Sai dai ya amince cewa akwai sauran aiki da ya k**ata a yi wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar.

“Shin muna buƙatar yin ƙarin aiki? Eh, babu shakka muna buƙatar yin ƙari. Amma shin har yanzu muna inda muka kasance a baya ne? Ko kaɗan. Ina ganin muna kan hanyar magance wannan matsala,” in ji Idris.

Ya yi kira ga ’yan Nijeriya da kafafen yaɗa labarai da su fahimci ƙoƙarin da rundunonin soji da sauran hukumomin tsaro suke yi, tare da ci gaba da bayar da rahoton abubuwan da s**a shafi tsaro da matakan da gwamnati ke ɗauka.

20/09/2026

Shekaru sama da 40 bayan da marigayi Shugaban ƙasa Shehu Shagari ya yi tunanin yin hanya ɗaya da ta tashi daga Sakkwato zuwa Badagry a bakin teku, a yanzu Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya duƙufa domin gina wannan babbar hanyar ta Sokoto-Badagry Superhighway. Dubi yadda aikin ke tafiya da kuma tasirin sa ga al'ummar yankin.

CNG Ya Fara Sauya Kudin Sufuri a Najeriya — TinubuShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce amfani da CNG wajen sufuri ya fa...
20/09/2026

CNG Ya Fara Sauya Kudin Sufuri a Najeriya — Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce amfani da CNG wajen sufuri ya fara rage wa ’yan Najeriya kuɗin mota a wasu jihohi, inda ya bayyana cewa ƙarin jama’a za su fara ganin sauƙin kuɗin sufuri daga 1 ga Oktoba, 2026. Ya ce a Borno, motocin CNG da na lantarki na jigilar jama’a kan N50 zuwa N100, maimakon N300 zuwa N600 da ake biya a wasu motocin kasuwanci, yayin da a Kaduna motocin CNG guda 100 s**a kwashe kusan fasinjoji miliyan 3.2 a shekarar farko, tare da ceton sama da N3.5 biliyan ga matafiya.

Tinubu ya ce a Oyo, motocin CNG na Pacesetter Transport sun sauke kuɗin mota daga Lagos zuwa Ibadan daga kusan N8,000 zuwa N3,200, yayin da a Adamawa aka rage wasu kuɗaɗen sufuri da kusan kashi 50 cikin 100. A Enugu, kuɗin mota daga Enugu zuwa Nsukka ya sauka daga N2,500 zuwa N1,500, sannan a Plateau motocin da gwamnati ke tallafawa suna jigilar kusan mutane 13,000 kullum kan N200, idan aka kwatanta da sama da N500 da ake biya a motocin kasuwanci.

Shugaban ya ce irin wannan sauƙin ya kuma bayyana a Abuja, inda haɗin gwiwar gwamnati da NURTW ya samar da rangwamen kashi 40 cikin 100 ga fasinjojin wasu hanyoyin da motocin da aka sauya zuwa CNG ke bi. Ya ce kuɗin mota daga Area 1 zuwa Gwagwalada ya ragu daga N1,500 zuwa N900, Nyanya daga N700 zuwa N420, yayin da Wuse ya sauka daga N400 zuwa N240. Ya ƙara da cewa a cikin shekaru uku, an sauya sama da motoci 120,000 zuwa CNG, tare da cibiyoyin sauya motoci sama da 400 da tashoshin CNG sama da 90 a faɗin ƙasar.

Tinubu ya buƙaci jihohi su ƙara kaimi wajen faɗaɗa shirin kafin 1 ga Oktoba, yana mai cewa Najeriya na da isasshen gas da za ta iya rage dogaro da farashin man fetur da dizal na duniya. Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa faɗaɗa ababen more rayuwar CNG da sauya motoci, domin tabbatar da cewa tanadin da ake samu daga mak**ashi mai rahusa ya koma ga jama’a ta hanyar rage kuɗin sufuri.

Yadda Kotun ICC Ta Tono Badaƙalar Dala 500,000 da Ya Shafi Atiku a Rikicin MambillaWata kotun sasantawa ta ICC da ke Par...
20/09/2026

Yadda Kotun ICC Ta Tono Badaƙalar Dala 500,000 da Ya Shafi Atiku a Rikicin Mambilla

Wata kotun sasantawa ta ICC da ke Paris ta gano cewa dala 500,000 da aka tura wa tsohuwar matar Atiku Abubakar sun shiga cikin muhawarar shari’ar kwangilar aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla.

Batun ya fito ne yayin da kotun ke sauraron takaddamar da Sunrise Power and Transmission Company ta shigar kan Gwamnatin Tarayya game da aikin Mambilla.

A cewar bayanan shari’ar, Leno Adesanya, wanda ya kafa Sunrise Power, ya tabbatar cewa ya tura dala 500,000 zuwa asusun bankin Amurka na Jennifer Douglas, tsohuwar matar Atiku, a ranar 30 ga Janairu, 2003. An tura kuɗin ne ta wani kamfani mai suna China Castle Investments Limited, wanda Adesanya ke iko da shi.

Adesanya ya bayyana wa kotun cewa kuɗin na da alaƙa da wani cinikin canjin kuɗi da aka yi wa Atiku, ba wai biyan kuɗin cin hanci da ya shafi kwangilar Mambilla ba.

Sai dai kotun ta ce ba a gabatar mata da takardun da za su tabbatar da wannan bayani ba, ciki har da shaidar biyan naira, farashin canjin kuɗin, umarnin Atiku ko wasu bayanan kasuwanci da s**a tabbatar da dalilin tura kuɗin.

Kotun ta kuma lura da cewa Atiku da Jennifer Douglas ba su bayar da shaida a gaban shari’ar ba domin ƙarfafa bayanin da Adesanya ya bayar.

Bugu da ƙari, kotun ta duba lokacin da aka tura kuɗin, inda ta lura cewa an aika dala 500,000 ne kimanin makonni biyu bayan gabatar da tayin Sunrise kan aikin Mambilla, kuma ƙasa da watanni huɗu kafin wasiƙar da ta yi ikirarin ba kamfanin kwangilar aikin a ranar 22 ga Mayu, 2003.

A gefe guda, kotun ta gano cewa Atiku yana da hannu cikin tattaunawar aikin Mambilla tun daga shekarar 2001, ciki har da ganawa da wakilan Sunrise da abokin hulɗarta na China, sannan ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa China a shekarar 2002 domin tattaunawa kan ayyukan wutar lantarki.

A ranar 17 ga Satumba, 2026, kotun ICC ta yi watsi da buƙatun Sunrise na sama da dala biliyan 3.38, tare da umartar kamfanin da Adesanya su biya kashi 75 cikin 100 na wasu kuɗaɗen shari’ar da Najeriya ta kashe.

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al'ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincikeGwamnatin Tarayy...
18/09/2026

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al'ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa gwamnatin Jihar Neja da al’ummar ta kan mutuwar mutane a wani samame na daƙile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Wushishi/Lukoto.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce yanayin da ya jawo mutuwar mutanen yana buƙatar a gudanar da cikakken bincike cikin gaskiya da adalci.

Idris ya ce Gwamnatin Tarayya ta riga ta ɗauki matakan gano abin da ya faru, bayan da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya dakatar da Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Idris ya ce: “Matakin gaggawar da Mai Girma Ministan Harkokin Cikin Gida ya ɗauka yana nuna irin muhimmancin da Gwamnatin Tarayya ta bai wa wannan lamari. Za a bar binciken ya gano ainihin abin da ya faru, kuma gwamnati na tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa za ta ɗauki matakin da ya dace bisa sak**akon binciken.”

Ya jaddada cewa duk da ci gaba da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da sauran ayyukan da s**a saɓa doka, waɗanda ke barazana ga tsaron ƙasa, albarkatun tattalin arziki da muhalli, dole ne a gudanar da ayyukan tabbatar da bin doka bisa ƙa’ida tare da mutunta rayuwar ɗan'adam da mutuncin sa.

Ya ce: “Ba za a yi ƙoƙarin kare duk wanda aka samu da laifi ba. A lokaci guda kuma, bai k**ata mu riga mu yanke hukunci kan sak**akon binciken ba. Nauyin gwamnati shi ne tabbatar da cewa an gano gaskiyar abin da ya faru kuma an yi adalci."

Idris ya yi kira ga al’ummar Wushishi da sauran al’ummar Jihar Neja da su kwantar da hankalin su, tare da ba da damar gudanar da binciken ba tare da katsalandan ba.

Ya jajanta wa iyalan waɗanda s**a mutu, al’ummar Wushishi da kuma al’ummar Jihar Neja baki ɗaya, yana mai tabbatar musu da cewa za a gano cikakken abin da ya jawo wannan mummunan lamari.

Ya roƙi Allah Ya jiƙan waɗanda s**a mutu, Ya bai wa iyalan su da al’ummar Jihar Neja ƙarfin jure wannan rashi.

Address

Kano

Telephone

+2349028483925

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fasihiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Fasihiya:

Shortcuts

Share