31/10/2025
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta yi bayanin cewa gayyatar da ta aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da sauran sanatoci, domin halartar bikin ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa a Jihar Kogi, ta yi ne don bin tsarin majalisa, ba don dalilai na ƙashin kai ba.
gayyatar ta miƙa ta ne a jiya Alhamis bayan dawowa daga dakatar da ita da majalisar ta yi, a matsayin wani ɓangare na shagulgulan cikar ta shekaru biyu a ofis.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa ta bi tsarin majalisa ta hanyar miƙa gayyatar ta ta hannun shugabancin majalisar.
“Yau, kamar yadda aka saba idan ana yin irin wannan sanarwa, na rubuta wasiƙa zuwa majalisa ta hannun wanda ke jagorantar zaman domin Shugaban Majalisa ya karanta ta a gaban zauren,” in ji ta.
Ta ce ta yi hakan ne domin gayyatar ta ta zama abin da zai haɗa kowa, ba ta son nuna cewa tana bikin nata ne kaɗai ba.
“Na fito da gayyatar ne don kada a ɗauka kamar ina yin bikin a kaina. Ni mutum ce mai hangen ci gaba. Ko da yake har yanzu ana da wasu shari’o’i a kotu, ina ci gaba da gudanar da aikina a majalisa bisa tsarin da ya dace,” in ji ta.
Akpoti-Uduaghan ta jaddada cewa wannan mataki nata yana nuna kishinta na bin doka da girmama majalisa, tare da jaddada cewa kaddamar da ayyukan ba don neman yabo bane, illa don hidima ga jama’a da ci gaban al’umma.