Jama'atu Ahbab Rasulullah, Janbulo.

Jama'atu Ahbab Rasulullah, Janbulo. This is The Official Page of Members Of Jama'atu Ahbab Rasulullah Association Of Nigeria Media Team Head Quarter Janbulo, Kano.

Muna gayyatar 'Yan uwa Masoya Shugaba Alayhis Salaam zuwa wajen Ɗaurin Auren Ahmad Shariff Sani Janbulo (H), muna neman ...
29/12/2023

Muna gayyatar 'Yan uwa Masoya Shugaba Alayhis Salaam zuwa wajen Ɗaurin Auren Ahmad Shariff Sani Janbulo (H), muna neman addu'a da sanya albarkar ku cikin wannan aure.

Kuma In sha Allah akwai majalisai da za'a gabatar yau Alhamis 28th December 2024 daga sha'irai da dama, gobe Juma'a bayan ɗaurin aure akwai wasu majalisan duk a Janbulo ƙofar gidan Baba Sidi.

M. Isma'il Jagayya Na Sidi
M. Ibrahim Autan Sidi
M. Shehi Ahmad Tajilizzi etc.

Allah ya barmu da Sayyidina Rasulullah.

Allah ya jaddada rahama gare su saboda Shugaba.
10/12/2023

Allah ya jaddada rahama gare su saboda Shugaba.

Jama'atu Ahbab Rasulullah Association Of Nigeria, Janbulo Kano State Takutaha 1445/2023.Muna cikin farin ciki mara misal...
04/10/2023

Jama'atu Ahbab Rasulullah Association Of Nigeria, Janbulo Kano State Takutaha 1445/2023.

Muna cikin farin ciki mara misaltuwa da wannan rana mai tarin albarka, Allah ya bamu albarkar wanda ya sauka a cikin ta.

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Takutaha 1445/2023In sha Allah gobe Laraba 04th, October 2023 za'a futa zagayen takutaha karfe 09:00am na safe dan gaisa...
03/10/2023

Takutaha 1445/2023

In sha Allah gobe Laraba 04th, October 2023 za'a futa zagayen takutaha karfe 09:00am na safe dan gaisawa da Masoya Shugaba Alayhis Salaam na birnin Kano da kewaye da taya su murnar samun Sayyidina Rasulullah.

Taswirar hanyoyin da za'a bi sune kamar haka 👇

Gidan Baba Sidi Janbulo-Kabuga -Tal'udu- Mandawari-Masallacin Sarki-Shahuchi.

-Yola-Gabari-Yan Mota- Bakin Zuwo- Gadar Salga - Farin Gida - Jakara- Goron Dutse - Tal'udu- Kabuga - Janbulo.

Allah yasa Annabi ya fimu farin ciki da yabawa da Soyayyar da muke masa saboda alfarmar sa.

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 IIIBamu fara dan mu daina ba, lamarin Annabi gaba gaba dai, yau ma gamu a kofar gidan Bab...
03/10/2023

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 III

Bamu fara dan mu daina ba, lamarin Annabi gaba gaba dai, yau ma gamu a kofar gidan Baba Sidi Shariff Sani Janbulo (H) a rana ta uku (3) dan sauraren abincin ruhi Sayyidina Rasulullah.

Mu da Annabi Muhammadu Sall'ALLAHU AlayHi Wa Sallam amana ce idan gashi ba zamu yi ta wanin sa ba har abada, komai yayi tunda da Annabi namu ne!

Allah ya kara rura wutar qaunar Shugaba Alayhis Salaam a cikin zukatan mu dan alfarmar sa.

Ayyamul Muhammadiyya Day III

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Innalillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un 😪Allah ya yiwa mahaifiyar Buhari Na Sidi Wudil (Amanar Fadar Bege) rasuwa yau talata...
03/10/2023

Innalillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un 😪

Allah ya yiwa mahaifiyar Buhari Na Sidi Wudil (Amanar Fadar Bege) rasuwa yau talata 03/10/2023, wanda jiya ma muna tare dashi a wajen Ayyamul Muhammadiyya a Janbulo.

Allah ya jiƙanta ya sadata da Annabin Rahma mu kuma ya kyautata karshen mu.

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 IITabbas Soyayya bata daga cikin abubuwan da suke ɓuye tare da masoyi, indai har so ya za...
03/10/2023

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 II

Tabbas Soyayya bata daga cikin abubuwan da suke ɓuye tare da masoyi, indai har so ya zama soyayya ana ganin sa, sai yakai ya kawo dan nuna yunƙurin sa akan abinda yake so, babu shakka mu ahalin soyayyar Manzan Allah ne kuma itace addinin mu.

Allah ya barmu da Sayyidina Rasulullah duk runtsi.

Ayyamul Muhammadiyya Day II

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 IIBarka da futowa Masoyin Shugaba. A duk lokacin da muke cikin ƙishin ruwan karancin saur...
03/10/2023

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 II

Barka da futowa Masoyin Shugaba.

A duk lokacin da muke cikin ƙishin ruwan karancin sauraren darajoji, muƙamai, buwaya, Isa da ƙasaitar Shugaba Alayhis Salaam muna ganin Baba Sidi to tabbas wannan ƙishin zai gushe daga gare mu saboda sai ya jiƙa mu sharkaf da Shugaban Halitta.

Allah ya kara mana ƙaunar Shugaba.

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 IIDukkan godiya da yabo su kara tabbata ga Ɗayantaccen Sarki, wanda ya wadata mu da lafiy...
02/10/2023

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023 II

Dukkan godiya da yabo su kara tabbata ga Ɗayantaccen Sarki, wanda ya wadata mu da lafiya da kuma arziki mafi girma shine Manzan Allah.

Salati da taslimi ga Jagoran Halitta Sarki a ranar mahashar, mai tutar godiya, mai ceto, mai alkausara da Shafa'atul Uzma da alayen sa da Sahabban sa tsarkaka.

Cikin yardar Allah gamu a rana ta 2 cikin jerin kwanaki uku da muka ware dan nuna farin cikin mu da Shugaba Alayhis Salaam wato “Ayyamul Muhammadiyya” yanzu haka muna sauraren yabo da baitoci daga bakin Sha'irai kafin futowar Baba Sidi.

Allah ya barmu a tafarkin Shugaba.

Ayyamul Muhammadiyya Day II

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Ba'a son Allah sai da Annabi, ba'a bin Allah sai da bin Annabi, ba'a sallah sai da Annabi, ba'a wata ibada sai da Annabi...
02/10/2023

Ba'a son Allah sai da Annabi, ba'a bin Allah sai da bin Annabi, ba'a sallah sai da Annabi, ba'a wata ibada sai da Annabi, ashe shi kansa shima ibada ne.

Idan kaso wani bawan Allah saboda biyayyar sa ga Allah Allah zai soka, to idan kaso Annabi me Allah zai yi maka? Kullum gaba ake so aci ba baya ba, mu gwanin mu Annabi ne yayi mana, ko ku beyi muku ba ni dai yayi min kuma yayin sa zanyi har abada.

©Sheikh Shariff Sani Janbulo (H).

Tabbas Kowane rai akwai abinda yake saka shi cikin nutsuwa amma mafi girman abinda yake saka rai da zuciyar mumini nutsu...
02/10/2023

Tabbas Kowane rai akwai abinda yake saka shi cikin nutsuwa amma mafi girman abinda yake saka rai da zuciyar mumini nutsuwa shine ambaton Sayyidina Rasulullah.

Shariff yana tsuma mu da daɗaɗan kirari da yabo ga ɗawisun qudura Muhammadur Rasulullah.

Ayyamul Muhammadiyya Day I

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023Dukkan godiya da yabo su kara tabbata ga ubangijin Annabi Muhammad ﷺ wanda ya sake nuna ma...
01/10/2023

Ayyamul Muhammadiyya 1445/2023

Dukkan godiya da yabo su kara tabbata ga ubangijin Annabi Muhammad ﷺ wanda ya sake nuna mana wannan ranaku na “Ayyamu” da muke taruwa manyan mu da yaran mu, daga wurare daban daban dan nuna farin cikin mu da samuwar Shugaban Halitta.

Salati da aminci su kara dirar ɗango ga shalelen ubangiji, sarki a sama sarki a ƙasa, limamin Annabawa da manzanni, jagoran mala'iku Annabi Muhammad da alayen sa da Sahabban sa baki ɗaya.

Yanda muka taru a wannan waje dan soyayyar mu da Annabi ﷺ ana ruwa amma muka tsaya, Allah ya haɗa mu a gaban Annabi ﷺ a ranar da halitta ke neman ɗaukin sa.

Ayyamul Muhammadiyya Day I

©Jama'atu Media Team Janbulo.

Address

Kabuga, Janbulo 1st Gate
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jama'atu Ahbab Rasulullah, Janbulo. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jama'atu Ahbab Rasulullah, Janbulo.:

Share