24/07/2022
Shugabannin Da S**a Sauka Daga Muƙamansu Saboda Sun Gaza Magance Matsalar Tsaron Ƙasarsu
K**ar yadda kowa ya sani rayuka da dukiyoyin al'umma sune abu na farko da ya wajaba a wajen kowace gwamnati a duniya ta kiyayeshi ga 'yan Kasar ta, daga lokacin da ta gaza yin haka kuma to babu abinda ya saura mata face ta sauka ko a sauketa.
Akwai Shugabanni a duniya da dama da s**a sauka daga kan muk**an su sak**akon gaza magance matsalar tsaron Kasar su da s**ayi. Daga cikin su sun hada da:
1• Hani Qawasmi:
Shine Ministan Cikin gidan Kasar Palestine, ya sauka daga kan mukamin sa na Ministan cikin gida sakamkon rashin iya shawo kan matsalar tsaron Kasar a rikicin Gaza.
2• Christophe Joseph-Marie Dabiré:
Shine Prime Minister na Kasar Burkinafaso, ya sauka daga kan mukamin sa ne sak**akon gaza shawo kan matsalar ta'addancin da ya baibaye Kasar, dan haka ne ya sauka daga kan mukamin sa tunda ya gaza.
3• Joseph Jouthe:
Prime Minister ne na Haiti, wanda ya sauka daga mukamin sa Sak**akon rashin iya shawo kan matsalar tsaron da ya addabi Kasar ta bangaren satar mutane, kisan ba gaira-ba dalili da dai sauran ayyukan ta'addanci wanda hakan tasa yaga tunda ya gaza gwara Kawai ya sauka.
4• Najib Mikati:
Shine Prime Minister na Kasar Lebanon, shima kuma ya sauka ne daga mukamin sa domin maslahar tsaron Kasar.
5• Soumeylou Boubèye Maïga
Shine Prime Minister na Kasar Mali, shima ya sauka daga mukamin sa ne Sak**akon rashin iya shawo kan matsalar tsaron da ya addabi Kasar.
Kundin tsarin Mulki na Nigeria Babi Na 8, Sashi na 306 ya halasta Shugaban da aka nada ko aka zaba yana da damar da zai sauka daga mukamin nasa.
Hakanan, Wannan Sashin dai na 306 Karamin Sashi Na 4 ya bawa Shugaban kasa damar sauka daga mukamin sa, dan haka Shugaba Buhari yayiwa Allah yayi koyi da sauran Shugabanni ya sauka daga mukamin sa tunda ya gaza.
Allah ya bamu lafiya da zama lafiya, Ameeeen.
Bissalam
Shehu Rahinat Na'Allah