View Point Hausa

View Point Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from View Point Hausa, Media, Kano.

View Point Hausa dandalin labarai ne mai zaman kansa da ke bayar da sahihan bayanai, bincike mai zurfi da nazari kan al’amuran da s**a shafi Arewacin Najeriya da duniya baki ɗaya.

Jerin kadarorin da kotu ta bayar da umarnin ƙwacewa waɗanda ke da alaƙa da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.Educ...
16/07/2026

Jerin kadarorin da kotu ta bayar da umarnin ƙwacewa waɗanda ke da alaƙa da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.

Educational Institutions

1. Rayhaan University, Kebbi State

2. Rayhaan University Permanent Site

3. Rayhaan University Temporary Site

4. Rayhaan University Third Site

5. Rayhaan University Vice Chancellor's House

Media

6. Rayhaan Radio, Birnin Kebbi

Hotels

7. Meethaq Hotels, Jabi, Abuja (53 rooms)

8. Meethaq Hotels, Maitama, Abuja (15 rooms)

9. Zeennoor Hotel, Kabuga Satellite Town, Kano (131 rooms)

10. Old Zeennoor Hotel Building

11. Former Harmonia Hotels Limited, Area 11, Garki, Abuja

Residential Properties

12. Luxury duplex in Maitama, Abuja

13. Three-storey building in Area 11, Garki

14. Terraces in Asokoro, Abuja

15. Property at Yakubu Gowon Crescent, Asokoro

16. Four-bedroom bungalow in Gesse Phase II, Birnin Kebbi

17. House at BUA Estate, Abuja

18. House at EFAB Estate, Gwarimpa, Abuja

19. Four-bedroom house in Abakpa GRA, Kaduna

20. Duplex in Wuse II, Abuja

21. Twin houses in Apo Legislative Quarters, Abuja

Commercial Properties

22. Shop at Citiscape-Shariff Plaza, Wuse II

23. Two warehouse shops at Wuse Market

24. Commercial plaza near Birnin Kebbi Market

25. Uncompleted two-storey plaza opposite Central Motor Park, Birnin Kebbi

Lands

26. 100 hectares along Birnin Kebbi–Jega Road

27. Another 100 hectares along Birnin Kebbi–Jega Road

28. 5.4 hectares at Academic Garden City, Birnin Kebbi

Kano Properties

29. Property at Ahmadu Bello Way, Nasarawa GRA

30. Property at Lamido Crescent, Nasarawa GRA

Housing Estate

31. Nine three-bedroom bungalows at Academic Garden City

32. Three two-bedroom bungalows at Academic Garden City

Industrial & Agricultural Assets

33. Rayhaan Agro Allied Factory

34. Factory buildings

35. Factory machines and plant units

36. Factory mosque

37. Rayhaan Mill staff quarters

38. Rayhaan Bustan Building

Azbir Arena Assets

39. Azbir Hotel

40. Printing Press

41. Gallery

42. Gardens

43. Mosque

44. Azbir Clothing

45. Azbir Pharmacy and Supermarket

Other Assets

46. Al-Afiya Energy tanker garage

47. Rayhaan Security House

48. Amasdul Oil and Gas filling station structure

Barazanar Kachalla Maha Ga Kano: Lokaci Ya Yi da Gwamnati Za Ta Nuna ƘarfiRahotannin da ke yawo cewa shugaban ƴan bindig...
02/07/2026

Barazanar Kachalla Maha Ga Kano: Lokaci Ya Yi da Gwamnati Za Ta Nuna Ƙarfi

Rahotannin da ke yawo cewa shugaban ƴan bindiga, Kachalla Maha, ya yi barazanar tayar da hankali a wasu sassan Jihar Kano sun ƙara jefa al’umma cikin fargaba, musamman a wannan lokaci da ake sa ran gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro.

Tambayar da ke yawo a bakin jama’a ita ce: Shin me ya sa har yanzu ƴan bindiga ke ci gaba da yin irin waɗannan barazana? Shin gwamnati ba za ta iya dakile su ba, ko kuwa sun fi ƙarfin gwamnati?

A zahiri, gwamnati ce ke da cikakken iko da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Duk da ƙalubalen da hukumomin tsaro ke fuskanta, jama’a na sa ran a ɗauki matakan gaggawa na tattara bayanan sirri, hana hare-hare tun kafin su faru, da kuma hukunta duk masu hannu a ayyukan ta’addanci.

Babu wata ƙasa da za ta ci gaba da bunƙasa idan jama’arta na rayuwa cikin tsoro. Saboda haka, lokaci ya yi da hukumomin tsaro za su nuna ƙwarewa da ƙarfi wajen kawo ƙarshen barazanar ƴan bindiga, domin tabbatar wa al’umma cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.

Allah Ya ci gaba da kare Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Point Hausa

22/06/2026

RAHOTANNI DAGA JIHAR KEBBI SUNTABBATAR DA MASU GARKUWA DA MUTANE SUN SAKE TAYAR DA HANKALI A YAURI, JIHAR KEBBI

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai hari gidan Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Yauri, Alhaji Yusuf Alhasan, da ke unguwar Low Cost a garin Yauri, inda s**a yi awon gaba da matarsa da ɗansa.

Bayanan da s**a fito sun nuna cewa lamarin ya faru ne da tsakar daren Lahadi zuwa safiyar Litinin, lamarin da ya sake jefa al’ummar yankin cikin fargaba da rashin tabbas.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san inda masu garkuwar s**a tafi da mutanen ba, yayin da ake ci gaba da kira ga jami’an tsaro da su gaggauta daukar matakin ceto wadanda aka sace tare da kamo masu hannu a wannan aika-aika.

Ci gaba da yawaitar sace mutane a yankunan Arewa na nuna bukatar karin hadin gwiwa tsakanin gwamnati, jami’an tsaro da al’umma domin dakile wannan matsala da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

— View Point Hausa

Barkanku da SallahAllah Ya Maimaita Mana
27/05/2026

Barkanku da Sallah
Allah Ya Maimaita Mana

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UNRahotanni daga Bayero University Kano sun tabbatar da rasuwar Dr. Musa Adamu Labaran, ...
25/05/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN

Rahotanni daga Bayero University Kano sun tabbatar da rasuwar Dr. Musa Adamu Labaran, mataimakin Dean na Faculty of Communication kuma malami a Sashen Mass Communication na jami’ar, wanda ya rasu a safiyar yau Litinin bayan gajeruwar rashin lafiya. 

Marigayi Dr. Musa Adamu Labaran fitaccen malami ne kuma masani a fannin sadarwa da harkokin yada labarai a Bayero University Kano. Ya kasance daya daga cikin manyan malaman Faculty of Communication, inda ya bayar da gudunmawa sosai wajen koyarwa, jagoranci da ci gaban dalibai.

An san shi da kwarewa da jajircewa wajen gudanar da ayyukan jami’a. Ya taba rike mukamin Assistant Exams Officer a Faculty of Communication, sannan daga baya aka nada shi Mataimakin Dean (Deputy Dean) na Faculty din bayan sake zaben Farfesa Umar Faruk Jibril a shekarar 2024. 

Dr. Musa Adamu Labaran ya samu digirorinsa na B.Sc, M.Sc da PhD daga Bayero University Kano, abin da ya nuna cikakkiyar alaka da jami’ar tun daga matakin karatu har zuwa koyarwa da shugabanci. Ya kasance cikin malaman da s**a sadaukar da rayuwarsu wajen bunkasa ilimi da tarbiyyar dalibai. 

A tsawon shekarun aikinsa, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa Sashen Mass Communication tare da bayar da gudunmawa a harkokin gudanarwa da shirye-shiryen Faculty of Communication. Abokan aiki da dalibansa sun bayyana shi a matsayin mutum mai mutunci, tawali’u da son taimakon al’umma.

Rasuwarsa ta girgiza iyalai, abokan aiki, dalibai da daukacin al’ummar jami’ar BUK, musamman Faculty of Communication inda ya yi fice wajen koyarwa da jagoranci. Sakonnin ta’aziyya na ci gaba da fitowa daga malamai, dalibai da abokan arziki suna addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya baiwa iyalansa, abokan aikinsa da daukacin al’ummar Bayero University Kano hakurin jure wannan babban rashi.
View Point Hausa

Wanene Zabin Ku?
23/05/2026

Wanene Zabin Ku?

21/05/2026

HANYOYI UKU DA ZA’ABI ABI A DAKILE FADAN DABA A JIHAR KANO.
SHEIKH IBRAHIM KHALIL
VIEW POINT HAUSA

Shugabannin Arewa Su Tashi Tsaye Domin Ceto Yankin — Janar Ibrahim Badamasi BabangidaTsohon Shugaban Ƙasa, Janar Ibrahim...
21/05/2026

Shugabannin Arewa Su Tashi Tsaye Domin Ceto Yankin — Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya yi kira ga shugabannin Arewa da su tashi tsaye domin ceto yankin daga mawuyacin halin da yake ciki, yana mai bayyana damuwarsa kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ci gaba da s**a addabi yankin.

Janar Babangida ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna damuwa kan yadda Arewa ke cigaba da fuskantar ƙalubale iri-iri da s**a haɗa da rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma koma bayan ilimi da tattalin arziki.

A cewarsa, lokaci ya yi da shugabanni da masu ruwa da tsaki za su haɗa kai domin nemo hanyoyin da za su fitar da yankin daga halin da yake ciki kafin lamarin ya ƙara taɓarɓarewa.

“Shugabannin Arewa kuyi ƙoƙarin fidda yankin Arewa daga mawuyacin halin da yake ciki. Mu tamu ta kare. Ina ji a jikina kamar bazan tsallake wannan shekarar ba,” inji Janar Babangida.

Tsohon shugaban ƙasar ya jaddada cewa makomar Arewa tana hannun shugabanninta da matasa, yana mai kira ga al’umma da su rungumi haɗin kai, zaman lafiya da kuma jajircewa wajen cigaban yankin.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan hanyoyin da za a magance matsalolin da s**a dabaibaye yankin Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.

View Point Hausa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso: Samun Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa Babbar Nasara Ce ga Jihar KanoJagoran Jam’iyyar NDC ...
19/05/2026

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso: Samun Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa Babbar Nasara Ce ga Jihar Kano

Jagoran Jam’iyyar NDC a Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa samun takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa wata babbar nasara ce ga al’ummar Jihar Kano da ma Arewa baki ɗaya.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan muhimmancin bai wa Kano damar taka muhimmiyar rawa a siyasar ƙasa, inda ya ce wannan ci gaba alama ce ta yadda jihar ke ƙara samun karɓuwa da tasiri a harkokin siyasar Najeriya.

Ya ƙara da cewa wannan dama da aka samu na iya zama wata kafa da za ta buɗe ƙofofi ga Kano domin samun cikakkiyar takarar Shugaban Ƙasa a nan gaba, idan aka ci gaba da haɗin kai da kyakkyawan shugabanci.

A cewarsa, Kano jiha ce mai yawan al’umma, tarihi da kuma ƙarfin siyasa, don haka tana da dukkanin cancantar da za ta iya kai ta ga jagorancin ƙasa a lokaci mai zuwa.

Sanata Kwankwaso ya kuma yi kira ga matasa da sauran al’ummar jihar da su ci gaba da bada goyon baya ga manufofin da za su kawo ci gaba, haɗin kai da cigaban dimokuraɗiyya.

Ya jaddada cewa siyasa ba ta ƙare da neman mukami kawai ba, illa tana buƙatar jajircewa, haɗin kai da sadaukarwa domin tabbatar da muradun al’umma.

DA DUMI-DUMI:Abba Kabir Yusuf ya amince da bai wa kowane maniyyacin aikin Hajjin bana daga Kano State tallafin Riyal 200...
11/05/2026

DA DUMI-DUMI:
Abba Kabir Yusuf ya amince da bai wa kowane maniyyacin aikin Hajjin bana daga Kano State tallafin Riyal 200 domin rage musu nauyin kashe-kashen da ake fuskanta yayin gudanar da aikin Hajji.

Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin jihar wajen tallafawa maniyyata da saukaka musu harkokin tafiya da gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when View Point Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category