25/07/2025
Fadar shugaban kasa ta musanta ikirarin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, cewa gwamnatin Bola Tinubu ta ware yankin Arewa. Kwankwaso ya bayyana a taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Kano cewa gwamnatin na karkatar da albarkatun kasa zuwa Kudu, lamarin da ke kara jefa Arewa cikin talauci da rashin tsaro. Ya kuma koka kan halin da titunan gwamnatin tarayya ke ciki, yana mai cewa tafiyarsa daga Abuja zuwa Kano ta hanyar mota ta kasance mai cike da wahala saboda lalacewar hanya.
Sai dai a martanin da ya fitar a shafin X, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya soki kalaman Kwankwaso, yana mai cewa ba su dace ba. Ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da muhimman ayyuka a yankin Arewa, ciki har da hanyoyi, noma, kiwon lafiya, da makamashi. Daga cikin ayyukan akwai titin Abuja–Kaduna–Kano, titin Sokoto–Badagry, bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano, da fadada titin Mararaba zuwa Keffi.
Dare ya kuma lissafa shirin bunkasa harkokin noma da aka fara a jihohi tara na Arewa da kuma aikin hako man fetur a Kolmani a Bauchi da Gombe. Ya ce akwai shirin ACReSAL da zai dawo da kusan hekta miliyan 1 na ƙasa da ta lalace, da kuma sabunta cibiyoyin lafiya da dama a Arewa. Ya kara da cewa akwai aikin tituna da yawa a Kano, Jos, Maiduguri, Borno, da Adamawa; da kuma manyan ayyukan makamashi, wutar lantarki da layukan dogo, wadanda duka aka fara cikin shekaru biyu da s**a gabata.