18/09/2025
Kisan Hakimin Dogon Daji A Zamfara Barazana Ce Ga Tsaron Ƙasa – In Ji Shugaban Arewa Media Writer’s, Comr. Haidar H. Hasheem
Shugaban ƙungiyar Arewa Media Writer’s, na ƙasa ya bayyana matuƙar takaici da bacin rai kan kisan gilla da ‘yan bindiga s**a yi wa Hakimin Dogon Daji a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda s**a yi masa yankan rago har lahira. Wannan lamari abin kunya ne ga ƙasa baki ɗaya kuma babban ƙalubale ne ga gwamnati da hukumomin tsaro k**ar yadda rahotan BBC Hausa da Leadership s**a kawo rahotan.
Wannan mummunan hari ya sake tabbatar da cewa lamarin tsaro a Arewacin Najeriya na ta ƙara tabarbarewa, inda ake ci gaba da kai hare-hare a ƙauyuka, sace jama’a, kona gidaje da gonaki, tare da hallaka shugabannin al’umma ba tare da tsoro ba. Wannan yanayi ya jefa dubban mutane cikin fargaba, gudun hijira, da rasa amincewa ga gwamnati.
Ya k**ata gwamnati ta gane cewa tsaro ba abu ne da za a siyasantar da shi ba. Tsaro shi ne ginshiƙin kowace al’umma, kuma kariya ga rayuka da dukiyoyi wajibi ne na gwamnati. Rashin ɗaukar mataki mai tsauri na iya ƙara dagula rayuwar jama’a da kuma barazana ga makomar ƙasa baki ɗaya.
A wannan yanayi, muna kira da:
1. Gwamnati ta tashi tsaye da gaggawa wajen murkushe ‘yan bindiga da duk wata ƙungiya ta ta’addanci a Arewa.
2. A samar da kayan aiki na zamani ga jami’an tsaro, tare da horo da ƙarfafawa domin su iya gudanar da ayyukansu yadda ya k**ata.
3. A shimfiɗa tsare-tsare na dindindin don tabbatar da tsaro a ƙauyuka da birane.
A madadin al’ummar Arewa da ƙungiyar Arewa Media Writer’s, ina kira da a ɗauki wannan kisan da aka yi wa hakimin Dogon Daji a matsayin kira na musamman ga shugabanni a dukkan matakai, domin lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen wannan masifar tsaro da ta addabi yankinmu.
A ƙarshe, ina addu’a ga Allah Madaukakin Sarki Ya jikan hakimin da aka kashe, Ya ba iyalansa da al’ummarsa juriya, Ya kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa ga Najeriya baki ɗaya.
✍️ Rubutawa:
Comr. Haidar H. Hasheem
National Ch