Muryar Afrika Media

Muryar Afrika Media Sahihiyar Kafar Sadarwa Don Samun Labarai Da Dumi-Dumi.
08068833322
(2)

MURYAR AFRIKA MEDIA Sahihiyar kafar sadarwar Zamani mai dauke da ingantattun labarai daga dukkan sassan Afrika da ma duniya baki daya.

Inna Lillahi Wa inna Ilaihi Raji’unAllah ya yi wa Alhaji Muhammad Ali Adam Babura rasuwa a yau AlhamisMarigayin mahaifi ...
06/08/2026

Inna Lillahi Wa inna Ilaihi Raji’un

Allah ya yi wa Alhaji Muhammad Ali Adam Babura rasuwa a yau Alhamis

Marigayin mahaifi ne ga Shugaban Kamfanin Muryar Afrika Media Link Ltd, Malam Rabi'u Muhammad, wanda aka fi sani da Abu Hidaya.

An karrama Dr. Farouk Lawan Da’u a Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), Kamar yadda Kwamanda Janar ya sanar da hakan ...
05/08/2026

An karrama Dr. Farouk Lawan Da’u a Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), Kamar yadda Kwamanda Janar ya sanar da hakan a yayin gudanar da Kwasa-kwasan Rantsar da Jami’an Sashen Yaƙi da Zamba (Anti-Fraud Unit Induction Course) da aka gudanar a Hedikwatar Ƙasa ta NSCDC da ke Sauka, Abuja.

Wani mutum mai shekaru 60 ya rasu bayan ya shiga wani otel da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, tare da wata budurwa...
22/07/2026

Wani mutum mai shekaru 60 ya rasu bayan ya shiga wani otel da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, tare da wata budurwa mai shekaru 20.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:50 na rana a ranar Talata, 21 ga Yuli, 2026. Rahotanni sun ce bayan mutumin ya nemi a kawo masa abinci a ɗakin da yake ciki, sai ya fara fama da matsananciyar wahalar numfashi.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Shi’isu Adam, ya ce jami’an ’yan sanda na sashen Yalwawa sun garzaya wurin bayan samun kiran gaggawa, inda s**a kai mutumin Asibitin Koyarwa na Dutse domin ceto rayuwarsa. Sai dai likitoci sun tabbatar da rasuwarsa bayan isarsa asibitin.

Bayan faruwar lamarin, jami’an bincike sun killace ɗakin otel ɗin tare da gudanar da binciken farko. A yayin binciken, sun kwato wasu kayan abinci, abubuwan sha, wani abin da ake zargin maganin ƙara ƙarfin jima’i ne, da kuma wasu kayayyakin mutumin domin ci gaba da bincike.

Rundunar ta ce bayan kammala dukkan matakan da s**a dace, an miƙa gawar mamacin ga iyalansa domin yi masa jana’iza. Haka kuma, budurwar mai shekaru 20 da ke tare da mamacin a lokacin tana ba ’yan sanda cikakken haɗin kai tare da bayar da bayanan da za su taimaka wajen gano ainihin abin da ya jawo mutuwar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ya tabbatar wa al’umma cewa za a gudanar da binciken cikin ƙwarewa da adalci, tare da roƙon jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, yayin da ake jiran sak**akon binciken.

Iyalan wasu matasa uku da ake zargin ’yan daba masu alaƙa da siyasa sun kashe a Kano sun gudanar da taron manema labarai...
22/07/2026

Iyalan wasu matasa uku da ake zargin ’yan daba masu alaƙa da siyasa sun kashe a Kano sun gudanar da taron manema labarai domin neman a yi musu adalci.

Iyalan mamatan, tare da ɗaruruwan mazauna jihar, sun buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Babban Lauyan Tarayya da Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Ƙasa (NHRC) da su tabbatar an gudanar da bincike mai zaman kansa, gaskiya da adalci kan lamarin.

A cewar iyalan, an kashe Nura Usman, Albashir Tukur da Abba ne a ranar 5 ga Mayu, 2026, lokacin bikin rantsar da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, a kusa da Kano Medical Centre da ke Race Course Road.

Mai magana da yawun iyalan, Malam Nasiru Usman Idris, ya ce shaidu da kuma bidiyon CCTV da ya bazu a kafafen sada zumunta sun nuna cewa an daba wa matasan wuka sau da dama kafin su rasu. Ya kuma yi zargin cewa mutanen da aka k**a tun farko dangane da kisan an sake su ba tare da an gurfanar da su ba.

Iyalan sun ambaci sunayen wasu mutane da suke zargi da hannu a harin, ciki har da Nazifi Nanaso, Mai Daudu, Rabi’u Farar Gafiya, Suda, Manniru Kanabaro da Daba-Daba, suna mai cewa har yanzu ba a ɗauki matakin da ya dace a kansu ba.

Taron ya kasance cikin yanayi na jimami, inda mahaifiyar ɗaya daga cikin mamatan ta fashe da kuka tana roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar an hukunta waɗanda s**a kashe ‘ya’yansu.

Haka kuma, iyalan sun yi zargin cewa wasu manyan mutane masu faɗa a ji sun yi katsalandan a binciken lamarin, abin da s**a ce ya sa s**a rasa kwarin gwiwa kan yadda ake tafiyar da shari’ar. Saboda haka ne s**a roƙi Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya karɓi binciken kai tsaye domin tabbatar da an yi adalci.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar Spain ta zama zakarar gasar cin kofin duniya ta 2026 bayan ta doke mai riƙe da kofin, Argen...
21/07/2026

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar Spain ta zama zakarar gasar cin kofin duniya ta 2026 bayan ta doke mai riƙe da kofin, Argentina, da ci 1-0 a wasan ƙarshe da aka buga bayan an tafi karin lokaci.

Dan wasan gaba Ferran Torres ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Spain nasara a minti na 106, bayan shafe lokaci mai tsawo ana fafatawa ba tare da an samu ƙwallo ba. Argentina ta kammala wasan da ’yan wasa 10 bayan Enzo Fernández ya samu jan kati sak**akon katin gargadi na biyu.

Da wannan nasara, Spain ta lashe kofin duniya na biyu a tarihinta, tare da kawo ƙarshen burin Argentina na kare kambunta. An yaba wa Spain kan yadda ta mamaye wasan, musamman a tsakiya da kuma tsaron baya, yayin da Argentina ta kasa samun damar cin ƙwallo duk da ƙoƙarin da ta yi.

Sai dai bayan kammala wasan, an samu hatsaniya tsakanin ’yan wasan ƙasashen biyu, lamarin da ya sa Hukumar FIFA ta fara bincike kan abin da ya faru.

Sabon Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano (KIRS), Alhaji Bashir Yusuf Maitama, ya k**a aiki a hukumance, inda ya ...
21/07/2026

Sabon Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano (KIRS), Alhaji Bashir Yusuf Maitama, ya k**a aiki a hukumance, inda ya yi alƙawarin gudanar da shugabanci bisa gaskiya, riƙon amana da kuma inganta hanyoyin tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida.

A jawabinsa na farko bayan k**a aiki, Bashir Maitama ya ce zai faɗaɗa tushen masu biyan haraji, ya ƙarfafa amfani da sabbin dabaru wajen gudanar da aiki, tare da tabbatar da adalci da gaskiya a harkokin hukumar.

Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa amincewar da ya yi da shi, yana mai alƙawarin sauke nauyin da aka ɗora masa cikin ƙwazo da biyayya.

Sabon shugaban ya yabawa ma’aikatan hukumar bisa gudunmawar da suke bayarwa, tare da jinjinawa shugaban da ya gada saboda tubalin da ya shimfiɗa wajen bunƙasa hukumar. Haka kuma ya buƙaci ma’aikata su ba da haɗin kai da sabbin shawarwari domin cimma manufofin ƙara yawan kuɗaɗen shiga na jihar.

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta mika wa Alhaji Ibrahim Al-Amin Little takardar tsayawa takarar gwamnan Ji...
21/07/2026

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta mika wa Alhaji Ibrahim Al-Amin Little takardar tsayawa takarar gwamnan Jihar Kano daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), wato EC-13B, a wani mataki da ke nuna ci gaba da shirye-shiryen jam’iyyar gabanin babban zaben shekarar 2027.

Ibrahim Little ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce shugaban riko na jam’iyyar ADC a Jihar Kano, Dr. Umar Bala Kwalwa, ne ya mika masa takardar.

Ya ce:

“Da yardar Allah na karɓi takardar tsayawa takarar gwamna ta INEC (EC-13B) daga hannun shugaban riko na ADC a Kano, Dr. Umar Bala Kwalwa. Muna addu’ar Allah Ya sanya alheri kuma Ya ba mu nasara.”

Wannan na zuwa ne bayan jam’iyyar ADC ta rusa tsohon kwamitin gudanarwarta na Jihar Kano tare da kafa kwamitin rikon ƙwarya domin sasanta rikice-rikicen cikin gida da s**a dabaibaye jam’iyyar, yayin da take shirin tunkarar zaben 2027. Bayan sasanta rikicin ne aka mika takardar tsayawa takarar ga Ibrahim Little.

Wata babbar kotun tarayya ta amince da bayar da belin shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal H**e, Bello Bodejo, kan kuɗ...
20/07/2026

Wata babbar kotun tarayya ta amince da bayar da belin shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal H**e, Bello Bodejo, kan kuɗin Naira biliyan biyu, bayan gurfanar da shi kan zargin damfarar kuɗi da s**a kai dala miliyan 2.63.

A cewar masu gabatar da ƙara, ana zargin Bodejo da hannu a wasu mu’amalolin kuɗi da ake bincike a kansu, zargin da yake musantawa.

Kotun ta shimfiɗa wasu sharuɗɗa kafin a sako shi, ciki har da gabatar da waɗanda za su tsaya masa da sauran buƙatun da kotun ta gindaya.

Sai dai har zuwa lokacin kammala zaman kotun, shugaban na Miyetti Allah bai cika sharuɗɗan belin ba, don haka zai ci gaba da zama a hannun hukumomi har sai ya cika su.

Ana sa ran za a ci gaba da sauraron shari’ar a ranar da kotun ta ɗaga zaman domin bangarorin biyu su gabatar da hujjojinsu.

Mutum ɗaya ya mutu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 39 da s**a ɓace bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da fasin...
20/07/2026

Mutum ɗaya ya mutu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 39 da s**a ɓace bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da fasinjoji sama da 40 ya kife a ƙauyen Malamawar Yan Dutse da ke ƙaramar hukumar Ringim a jihar Jigawa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi lokacin da kwale-kwalen ke jigilar manoma da ma’aikatan gona, waɗanda akasarinsu mata ne, zuwa gonakinsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya ce da samun rahoton hatsarin jami’an tsaro tare da masu ceto da masu nutso na yankin sun garzaya wurin domin gudanar da aikin ceto. Ya ce an gano gawar mutum ɗaya, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutanen da s**a ɓace.

Hukumomin jihar sun ce suna aiki tare da sauran jami’an agaji da al’ummar yankin domin gano dukkan mutanen da hatsarin ya rutsa da su, tare da alƙawarin sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu.

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun sanar da k**a wasu mutane biyu a jihar Borno da ake zargin suna da alaƙa da ayy...
20/07/2026

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun sanar da k**a wasu mutane biyu a jihar Borno da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan ‘yan ta’adda.

Waɗanda aka k**a sun haɗa da wani ɗan ƙasar Sudan da ake zargin yana haɗa kai da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, da kuma wata mata ’yar ƙasar Ghana.

A cewar rundunar sojin, an k**a mutanen ne a wasu hare-haren sintiri da aka gudanar bisa bayanan sirri a sassa daban-daban na jihar.

Sojojin sun ce ana ci gaba da bincike domin gano irin rawar da kowane daga cikinsu ya taka, da kuma ko akwai wasu da suke aiki tare da su.

Sun ƙara da cewa kamen wani ɓangare ne na matakan da jami’an tsaro ke ɗauka na dakile hanyoyin da ‘yan ta’adda ke samun tallafi da bayanai a yankin Arewa maso Gabas.

Hukumomin tsaron sun jaddada cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da na tattara bayanan sirri domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

Address

No. 17 Tarauni Kano
Kano
100001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Afrika Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share