29/07/2025
LABARIN WATA TIRELAR GIYA DA HISBAH
Wannan labarin na ɗauke da ƙalubalen da hukumar Hisbah take fuskanta game da abin da ya shafi doka.
Yadda Abin ya faru
Hukumar Hisbah ta taɓa k**a tirela maƙare da giya, ta kai wannan mota kotu, masu giyar s**a ɗau lauya, hukumar Hisbah ita ma ta ɗau lauya, aka je Hisbah ta gabatar da dokokin ta da s**a hana sha da sarrafawa da kuma ta,amuli da duk kayan maye, don haka ta nemi Alƙali da yayi hukunci akan wannan TIRELAR, cewa ya ƙwace ta, ya damƙa wa hukumar Hisbah tare da court order aje a ƙone ta.
Sai lauyan ɓangaren masu mota ya tashi yace, ita wannan mota ta giya da aka k**a an k**a ta ne akan titin gwamnatin tarayya, inda dokar jiha bata aiki, saboda haka ina roqon mai girma Alƙali da ya saki wannan motar kuma ya umarci yan HISBAH suyi mata rakiya har ta bar jihar nan.
Alƙali yace ya gamsu da hujjojin da wannan lauya ya bayar don haka an saki wannan motar, yan HISBAH ku sa mota gaba, kusa mota baya, kusa motan giya a tsakiya, kuyi mata rakiya ta bar jihar.
Sai wani ya koma gefe ya raɗa wa ƴan HISBAH idan kun je wuri kaza, motar zata yi clear, to titin da zata hau na jiha ne, ku riqe ta a nan, ƴan HISBAH s**a yi rakiya ransu a ɓace ,sai iya wanda ya san bayanin, zuwa can zasu wuce sai s**a yi kwana, sai ga su sun faɗo kan titin jiha, sai yan HISBAH s**a ce ayi parking, an karya doka, mu koma, aka koma.
HISBAH ta ce to mun yi ɗa,a da biyayya lokacin da aka k**a giyan nan, kan titin nan na federal government ne, an bamu umarni mu je mu rakata, to mun rakata sai kuma ta faɗo kan titin jiha sai muka k**a ta.
Sai Alƙali yace, to yanxu kuma kuje ku fasata, kai kuma an baka kwana talatin (30) ai zaka yi appeal (ɗaukaka ƙara), in kwana talatin (30) ya cika baka yi appeal ba hukumar Hisbah, tazo ta karɓi court order taje ta gama da wannan giyan.
Daga cikin Maƙalar da SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA ya gabatar a ABU ZARIA.
Mai TAKEN ƘALUBALEN DA AIKIN HISBAH YAKE