05/01/2023
Marigayi Dr Ahmad Ibrahim BUK yana cewa: "idan ka nemi wani abu a rayuwa kaga baka samu ba, to ka tuna da cewa Allah Maɗaukakin Sarki dai ba marowaci bane, kuma ba maƙetaci bane, tunda kaga ya hanaka, to tabbas hanakan shi ne alkhairi a gare ka."
Haƙiƙa Dr Ahmad BUK yana daga cikin malamai masu tsantseni da gudun duniya, waɗanda suke koyar da al'umma tsantsar tarbiyyar rayuwa, da amintuwa, tare da sakankancewa da Allah Maɗaukakin Sarki wajen samun duk wata nasara, da nutsuwa a rayuwa, wanda ire-iren sa kaɗan ne a yanzu.
Bayan hukunce hukunce da yake yawaita bayani tare da warwarewa a cikin karatuttukan sa, da sauran lakcocin sa, Malam yakan kuma mayar da hankali wajen sake bayyanawa al'umma hanyoyi da yawa da za su fahimci masalahar rayuwar su, ta hanyar fito da ɓoyayyun ma'anonin nassoshin ayoyi da Hadisai, wanda hakan yana taimakawa al'umma wajen ƙara fahimtar rayuwa, da samun nutsuwa yayin da wasu matsalolin s**a same su.
Allah Akbar. Tababs munyi babban rashin Malam. Ina addu'a, tare da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Yasa Al-Jannah ce makoma a gare shi, Amin.
Adamu Kazaure !
Ɗan Almajiri.