13/01/2026
Baffa Babba 'Dan Agundi: Yadda Ganduje Ya So Kwankwaso Ya Jawo Abba zuwa APC
Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nuna ɓacin ransa kan kalaman da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi a kansa
Duk da haka, Ganduje ya bayyana cewa APC na maraba da lale da yiwuwar dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin ikon jam’iyya mai mulki a matakin kasa
Makusancin tsohon Gwamnan, Alhaji Baffa Babba 'Dan Agundi ne ya tabbatar da haka a yayin da ake zaman jiran sauya shaƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan wasu kalamai da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a kansa.
Tsohon Gwamnan na Kano ya bayyana kalaman da cewa ba su dace ba, kuma masu tayar da hankali ne a yayin da maganar sauya sheƙa Gwamna Abba Kabir Yusuf ke kara kwari.
Wannan bayani ya fito ne daga makusancin Ganduje, Dakta Baffa Babba Dan’agundi, yayin da yake zantawa da manema labarai wanda kuma aka wallafa a shafin Facebook na DC Hausa.
Kalaman Rabiu Kwankwaso sun damu Abdullahi Ganduje
A cewar Baffa Babba 'Dan Agundi, Ganduje ne da kansa ya bayyana masa yadda kalaman s**a dame shi matuƙa, kuma bai ji dadinsu ba.
Ya ce: “Dr. Ganduje ya shaida min cewa bai ji daɗi ko kaɗan da kalaman da Sanata Kwankwaso ya yi a kansa ba."
'Dan Agundi ya bayyana cewa Ganduje ya zargi Sanata Kwankwaso da kiransa da suna makiyi a gaban magoya bayansa.
Ya ce hakan ya faru ne a lokacin da Kwankwaso ke zargin Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da shirin ƙwace iko da wasu hukumomin gwamnati domin amfani da su kan abokan hamayyarsa na siyasa.
Ya ce: “Ganduje ya bayyana min cewa irin waɗannan kalamai ba su dace ba, musamman a wannan lokaci da Jihar Kano ke buƙatar haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba na bai ɗaya.
APC na maraba da Gwamna Abba Gida Gida
Sannan Ya ƙara da cewa Ganduje ya yi imanin cewa yiwuwar dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC ya kamata ta zama dama ta sulhu da haɗin gwiwa a tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar, ba sabani da ƙarin rikici ba.
Ya ce: “A fahimtar Ganduje, dawowar Gwamnan Kano APC ya kamata ta zama wata hanya da za a haɗu, a manta da banbance-banbance, a mayar da hankali kan ciyar da Kano gaba."
Dakta Ganduje ya kuma jaddada cewa, la’akari da shekarunsu da gogewarsu a siyasa, shi da Sanata Kwankwaso ya kamata su rika taka rawar dattawan ƙasa, maimakon ci gaba da rikicin siyasa.
Ya ce: “Ya yi imanin babu dalilin ci gaba da saɓani, domin dukkanninsu sun kai matakin da ba su da wata babbar buƙata ta siyasa, tunda sun kammala iyakar wa’adin rike muƙaman zaɓe."
Da yake magana kan rahoton dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf APC, Dan’agundi ya bayyana hakan a matsayin abin farin ciki da ƙarfafawa ga jam’iyyar APC a Kano.
Ya ƙara da cewa shirye-shiryen tarbar Gwamnan a hukumance sun yi nisa, ya kuma yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da haɗin kai a Kano, tare da fatan dawowar Gwamna Abba APC za ta haifar da ci gaba mai ɗorewa.