20/05/2026
Tirkashi 🤔
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Sadarwa da Manufofi, Daniel Bwala, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ‘yan ƙasa damar kare kansu daga hare-haren ‘yan ta’adda ko masu neman kashe su.
Bwala ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba, inda yake tsokaci kan hare-haren da s**a faru a ƙauyen Esiele da ke Ƙaramar Hukumar Orire ta Jihar Oyo, da kuma sace malamai da ɗalibai a makarantar firamare ta LA Primary School.
A cewarsa, kundin tsarin mulki ya tanadi haƙƙin kare kai ga kowane ɗan Najeriya.
“Tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan ƙasa damar kare kansa,” in ji Bwala.
“Idan aka haɗa haƙƙina da naka da na maƙwabci na, hakan ya zama haƙƙin gama-gari na kare kanmu, kuma ‘yan Najeriya suna da damar yin hakan.”
Ya ƙara da cewa, “Idan wani ya shigo gidana da niyyar kashe ni, duk wani makami da zan yi amfani da shi wajen kare kaina kundin tsarin mulki ya amince da shi.”
Sai dai Bwala ya yi gargaɗin cewa mallakar bindigogi da wasu makamai na ƙarƙashin dokar ƙasa ne, yana mai cewa ba kowane irin makami ne ɗan ƙasa zai iya mallaka ba sai wanda doka ta amince da shi.
Ya ce al’umma na iya haɗuwa su nemi izini daga gwamnati domin samar da tsarin tsaro na haɗin gwiwa don kare kansu.
Me zaku ce akan Maganar tasa??