27/10/2024
JAMI'AN ENVIRONMENTAL A KATSINA
A jihar katsina zaa dauki maaikata Wanda suke da alaka da aikin asibiti, Amma Babu masu kula da Muhallin asibiti, da lafiyar Muhallin da Wanda suke cikin asibitin (Environmental Health Officers).
Environment department yanada mahimmanci sosai, Amma jihar katsina ta maidashi ba komai ba, a dokar Nijeriya ma environmental Yana cikin top 5 courses da s**a zama komai-da-ruwanka, Amma a haka, aka maidashi baya.
Kowane sector a Nijeriya tana bukatar jami'in duba-gari (Environmentalist), a kowane kamfani, kowace masana'anta, kowane lungu-da-sako, kowane asibiti akwai Department na environmental, miyasa ba'a daukarsu aiki? Uwa uba ma STATE SEPA baa daukar kowa aiki.
DUK wannan abun, ya samo asali daga manyan masu rike da mukamai ne Wanda s**ayi karatun, Basu iya Kai koke a dauki masu karatu irin nasu, saidai kawai s**ai danginsu da makota, wasu ma ko makotansu Basu iya kaiwa, sai ka Bayar da kudi (Cin hanci) idan kanason samun gurbin aiki.
KADAN DAGA ABUBUWAN DA SUKEYI:
1. Kawo hanyoyin kare yaduwar cututtaka a tsakanin marasa lafiya zuwa ga masu jinyarsu
2. Tabbatar da tsafar kayan aiki na asibiti Wanda s**a hada da Almakashi, motar dauko Mara lafiya, keken dauko marasa lafiya, da sauransu.
3. Tabbatar da tsaftar dukkanin sassan asibitoci tun daga lokacin tattara shara har zuwa lokacin kaiwa wajen da aka tanada domin zubar da shara.
4. Wayar da kan marasa lafiya game da tsaftar muhalli, jiki da kayan sanyawa ko kayan abinci.
5. Wayar da kan malaman asibiti duk bayan wani lokaci akan mahimmanci zubar da shara Mai hatsari (Biohazard ☣️)
6. Kulawa da yanayin iskar da marasa lafiya suke shaka, domin kaucewa kamuwa da cutar kansa.
Akwai abubuwa dayawa Wanda idan ba jami'in duba-gari ba, Babu Wanda zai yisu yanda ya dace, shyasa asibiti kullum baya rabuwa da marasa lafiya, saboda Babu kulawa da tsaftar muhalli, jiki da abunda ake ci-ko-sha.
Da ace Ina da Iko, ko wata dama wacce zanyi magana takai har wajen Maigirma Gwamna (Dikko Umar Radda Phd) da zan bashi shawara da Kuma duk wata hujja day kamata na bashi akan cewa kowane sector tana bukatar jami'in duba-gari a Nijeriya ba katsina kadai ba ma.
Ina fata, wata Rana Sako na zaije wajen Daya dace, har inkai koken Yan'uwana Yan environmental a gaban Mai girma Gwamna, domin inada yakinin zaa samu chanji idan har yaji daga gareni.
San. Idris Shafiu Aliyu