TRC Hausa

TRC Hausa Kafar yaďa Labaran TRC Hausa na kawo muku labaran duniya musamman na gida Najeriya Da Dumi-Dumin su

Yanzu-Yanzu : Ƴan bindiga sun shiga cikin garin Tsiga sunyi awon gaba da al'umma da dama ciki har da Brig Gen Maharazu T...
06/02/2025

Yanzu-Yanzu : Ƴan bindiga sun shiga cikin garin Tsiga sunyi awon gaba da al'umma da dama ciki har da Brig Gen Maharazu Tsiga (RTD).

Daga Aliyu Adamu Tsiga

HOTUNA: Yadda wata sabuwar gobarar daji ta sake tashi tare da ci gaba da bazuwa a jihar Los Angeles, California a Ƙasar ...
23/01/2025

HOTUNA: Yadda wata sabuwar gobarar daji ta sake tashi tare da ci gaba da bazuwa a jihar Los Angeles, California a Ƙasar Amurka, inda cikin awanni kaɗan ta laƙume wurare da dama.

📸: AFP

Dokar Aure Tsakanin Namiji Da Mace Ne Kadai Zai Yi Aiki A Kasar Nan, Amma Batun Aurèn Jiñśi, Ma'àña Macè Ța Aùŕì Màce, K...
20/01/2025

Dokar Aure Tsakanin Namiji Da Mace Ne Kadai Zai Yi Aiki A Kasar Nan, Amma Batun Aurèn Jiñśi, Ma'àña Macè Ța Aùŕì Màce, Kò Nàmiji Ya Aùri Namìjì Babu Shi, Inji Sabon Shugaban Kasar Amurka Donald Trumph Bayan Ya Yi Rantsuwar K**a Aiki

Me za ku ce?

WATA SABUWA: Wani Matashi A Jihar Ya Ɗirkakawa Wata Tsaleliyar Budurwa Aljana Ciki A Rashin SaniLamarin Ya Faru A Ƙauyen...
20/01/2025

WATA SABUWA: Wani Matashi A Jihar Ya Ɗirkakawa Wata Tsaleliyar Budurwa Aljana Ciki A Rashin Sani

Lamarin Ya Faru A Ƙauyen Kaɗaki Dake Ƙaramar Hukumar Giwa Jihar Kaduna, An Zargin Matashin Saurayin Aljanan Habib (Bota) Da Ɗirkakawa Aljanar Ciki.

Wani Abokin Bota Ya Bayyana Cewa Bota Ya Na Ɗan Zagayawa Da Aljanar Ne Idan Zasuyi Fira Da Juna, Ya Kara Da Cewa : Wani Abokinsu Ke Taimaka Masu Da Ɗakinsa Na Kwana, Inda Ake Zargin A Nan Ne Suke Yin Sha'anin.

Kawo Yanzu Matashin Da Ya Ɗirkakawa Aljanar Cik1 Habib (Bota) Na Kwance Cikin Mawuyacin Hali, Sakamakon Cafkesa Da Aljanar Tayi, Kuma Take Bayyana Tabbacin Sai Ta Ga Bayansa, ko Kuma Ya Aure Ta Ya Samu Zaman Lafiya.

A Cewar Aljanar Mai Suna Mero : An Samu Shigar Juna Biyu Sakamakon Irin Yadda S**ayi Musayar Turmi Da Taɓarya Tsakanin Su, K**ar Yadda Take Bayyana Haka A Jikin Saurayin Nata.

YANZU-YANZU: Sojoji sun haramta amfani da jirgin sama maras matuki  a Arewa-maso-Gabas Dakarun haɗin gwiwa na 'Operation...
15/01/2025

YANZU-YANZU: Sojoji sun haramta amfani da jirgin sama maras matuki a Arewa-maso-Gabas

Dakarun haɗin gwiwa na 'Operation Hadin Kai' a Arewa-maso-Gabas sun haramta amfani da jiragen sama marasa matuka, da ake kira drones, a yankin.

Kwamandan Sashen Sojan Sama, Air Commodore U. U. Idris ne ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa da Daily Trust ta gani, inda ya ce amfani da drones ba tare da izini ba na iya haifar da barazana a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa.

Ya koka cewa hukumomin gwamnati da kuma wasu mutane masu zaman kansu na amfani da drones ba tare da amincewar Sashen Sojan Sama na Operation Hadin Kai ba.

ZU-YANZU: Tinubu ya dage taron FEC Ya Gayyaci Shugabannin tsaro Zuwa A*o RockAn dage taron majalisar zartaswa ta tarayya...
05/08/2024

ZU-YANZU: Tinubu ya dage taron FEC Ya Gayyaci Shugabannin tsaro Zuwa A*o Rock

An dage taron majalisar zartaswa ta tarayya da aka shirya yi da yammacin yau litinin. An hangi ministocin da s**a isa taron suna barin zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa da tsakar rana.

Ministoci ƙalilan ne s**a isa lokacin da aka sake tsara taron. Ana kyautata zaton cewa dage zaman na da nasaba da taron tsaro da ake yi yanzu haka a fadar shugaban kasa, wanda shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.

Hajiya Mariya Sunusi Dantata, Mahaifiya ga Alhaji Aliko Dangote tace Duk Waɗanda S**a fasa Mata Store S**a Kwashi Kayan ...
03/08/2024

Hajiya Mariya Sunusi Dantata, Mahaifiya ga Alhaji Aliko Dangote tace Duk Waɗanda S**a fasa Mata Store S**a Kwashi Kayan Abinci a Ranar da akayi Zanga Zanga Duk ta Yafe musu.

Tace daman Su ake diba a dafa a rabawa Kullum don haka duk ta yafe musu tunda suma dafawar zasuyi a gida suci.

DA DUMI-DUMI: Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kafa wata tawaga Ta Musamman domin Ganawa da Shu...
03/08/2024

DA DUMI-DUMI: Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kafa wata tawaga Ta Musamman domin Ganawa da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan halin da ake ciki a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Kamfanin Sadarwa na MTN a Najeriya ya rufe ɗaukacin shagunansa da cibiyoyinsa a sassan ƙasar jim kaɗan shan caccaka daga...
30/07/2024

Kamfanin Sadarwa na MTN a Najeriya ya rufe ɗaukacin shagunansa da cibiyoyinsa a sassan ƙasar jim kaɗan shan caccaka daga tarin kwastamominsa da ya kulle musu layukansu a ranar Lahadin da ta gabata.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UNAllah ya yi rasuwa wa Wakilin Shaikh Zakzaky  na Jos, Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos ba...
30/07/2024

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN

Allah ya yi rasuwa wa Wakilin Shaikh Zakzaky na Jos, Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos bayan ƴar gajeruwar jinya.

Daga zuwa duba ginin gidajen yan gudun hijira a Borno, Gwamna Zulum ya tara Leburorin da ke aiki s**a tattauna.Yayin hir...
20/10/2023

Daga zuwa duba ginin gidajen yan gudun hijira a Borno, Gwamna Zulum ya tara Leburorin da ke aiki s**a tattauna.

Yayin hirarsu ne ya gano 37 daga ciki sun kammala Sakandire, ya ɗauki nauyin karatunsu na jami'a har su gama.

Mai girma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai bayar da tallafi na naira 50K ga mutane 1,300 a fadin ƙananan hukomomi 774...
03/09/2023

Mai girma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai bayar da tallafi na naira 50K ga mutane 1,300 a fadin ƙananan hukomomi 774 dake fadin Najeriya.

Sannan za'a bawa masu kananen sana'oi bashin dubu 500k zuwa Mliyan daya 1m. Zaku ma a bawa masu manyan Jari suma bashi na kudade masu yawa duk dan su bunkasa harkokin su.

Wannan yana cikin kokarin gwamnati Tarayya na bunkasa tattalin Arzikin Kasa da kuma ragewa mutane radadi na yanayin da ake ciki.

Abdulaziz Abdulaziz
SSA PMedia

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TRC Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to TRC Hausa:

Share