25/12/2023
Jaruma ce Sadaukiya, Mai Qarfin Jiki da Qarfin Imani.
Ta ciri tuta a tsakanin Matayen duniya.
Tayi abin da Mazaje da dama s**a kasa yi a lokacin YAƘIN UHUDU.
Ba kowa bace, fa ce Nusaibah bintu Ka'ab.
Ana yi mata alkunya ko lakabi da "Ummu 'Ammarah".
An haifeta a garin Madinah, kuma tana daya daga cikin farkon waɗanda s**ayi imani da Allah s**a gaskata Manzon Allah.
Ta halarci Bai'atul Aqabah (Mubaya'ar yarjejeniya wacce mutanen Madinah s**a yi ma Manzon Allah kafin yayi hijirah zuwa garesu).
Ta halarci Bai'atur Ridhwan (Mubaya'ar da Sahabbai sama da dubu goma s**ayi ma Manzon Allah) a karkashin wata bishiya, wacce a nan take Allah ya karba, yace ya yarda dasu kuma ya basu Aljannah.
Ta halarci Yakin Badar da Uhudu tare da Mijinta Zaidu bn Amru da 'Ya'yanta Habibu da Abdullahi.
Kuma ta halarci Yakin Yamamah.
Wato Yakin da akayi da 'Yan Riddah (Mutanen Musaylamah) a zamanin Khalifancin Sayyadina Abubakar (R.A).
A ranar Yakin Uhudu ne ta nuna Jarumtakar da kowa yake labarinta akai.
Jarumtakar da har abada ba zata mance da ita ba.
A ranar Yakin Uhudu lokacin da Kafirai s**a zagaye Muminai suna ta shahadantar dasu.
Mazaje sun tarwatse wasu dun sun warwatse amma "Ummu Ammarah" tana tare da Manzon Allah, ta rike Takobi da Garkuwa tana doke kafirai masu son cutar da Manzon Allah.
Manzon Allah ya bada shaida a gareta yana cewa:
"A duk lokacin dana waiga Damana ko Haguna sai na ganta tana yaki domin kareni".
Ibn Abdul Barri ya ruwaito cewa a ranar Yakin Badar, Ummu Ammarah ta samu nasarar kashe kafirai da dama.
A cikinsu har da wani katon kafiri Mahayin doki.
Domin ya zaburo dokinsa ya taho a guje domin cutar da Ma'aiki amma nan take Ummu Ammarah ta soke shi da Takobinta, ta aika dashi lahira.
Imamul Waqidiy yace:
Ummu Ammarah (R.A) tayi jinyar Sahabban da s**aji rauni a ranar Uhudu.
Kuma ita kanta ma taji raunuka har guda Goma Sha Biyu.
A cikin waɗannan raunukan har da wani a jikin wuyanta wanda sai da tayi jinyar shekara guda kafin ya warke.
Tana kwance bata gama warkewa ba, sai taji mai shelar Manzon Allah yana gayyatar Sahabbai zuwa Yakin nan na "HAMRA'UL ASAD".
Tana jin wannan shelar sai ta tashi ta d'aura 'd'amararta ta fito aka tafi da ita (Radiyallahu Anha).
Haka nan bayan Ma'aiki yayi wafati sai kabilun larabawan kauyuka s**a rika komawa kafirci.
Wasu kuma s**a rika hana Zakkah.
Don haka Sayyadina Abubakar ya rika tura rundunoni domin Yaki da masu riddah.
To a cikin waɗannan rundunonin babu wacce aka fafata Yaki kamar wacce aka tura Yankin Yamamah domin yaki da makaryacin nan mai suna Musaylamah.
To a cikin wannan rundunar akwai Sayyidah Nusaybah wato Ummu Ammarah (R.A) kuma ta dauki Takobinta da Garkuwa ta fafata yaki.
Tayi kokari sosai wajen kashe kafirai.
A cikin haka ne har wani kafiri ya sareta a hannunta, hannun ya cire daga jikinta, ga kuma raunuka.
Amma Ummu Ammarah bata dena Yaki ba.
Har sai da aka ci nasarar kashe babban kafirin wato Musaylamah.
Ya Allah ka kara yardarka bisa Sayyidah Ummu Ammarah.
Sannan wannan Baiwar Allah ta rasu a Shekara ta 13 bayan Hijrah.
Ka saka mata da alkhairi bisa hidimar da tayi ma Annabinka, Manzon tsira fiyayyen halitta Annabi Muhammadu, Sallallahu Alaihi Wa Sallam.
Don Allah Mazan mu da Matan mu muyi kokari mu yi koyi da wannan Baiwar Allah.
Daga dan uwanku a Musulunci, Kamalu Hassan Gaya 🖊️.
Kamalu Hassan Gaya.
Gaya Local Government,
Kano State,
Nigeria.
December 22nd, 2023.