18/09/2025
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano
Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin samar da megawatt bakwai (7MW) na wutar sola a asibitin.
Yayin bikin kaddamar da aikin a Kano a jiya Laraba, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Bichi, Abubakar Bichi, ya bayyana cewa an ware fiye da naira biliyan 12 domin aikin, wanda ake sa ran zai baiwa asibitin wutar lantarki ba tare da dogaro da tsarin wutar lantarki ta kasa ba.
Bichi, wanda shi ne ya kawo aikin, ya ce wannan shiri ne na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da sola ga dukkan manyan makarantu da asibitocin koyarwa a fadin kasar, inda aka fara da AKTH.
Ya nuna godiya ga Shugaba Tinubu bisa amincewa da kuma goyon bayan wannan aiki.
A nasa jawabin, Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Uche Nnaji, ya ce wannan aiki farkon mataki ne na aiwatar da shirin Sabon Fata da gwamnatin Tinubu ta zo da shi.