08/04/2025
Sakon wani Dan Nigeria mazaunin kasar Qatar
Har Yanzu Bamuga Hukunci Ko Cikakken Rahoto Dake Nuna An Dauki Mataki Akan Kisan Mutane 16 a Edo Ba.
Amma sai gashi jiya muna ganin yadda aka gayyato Sarkin Kano zuwa Abuja domin kawai yayi hawan Sallah — alhali har yanzu ana yi masa barazana saboda siyasa.
Ina jami’an tsaro musamman AIG Me ya hana shi gayyato Gwamnan Edo ko Sarkin Edo domin tattauna yadda za a shawo kan lamarin kisan mutane 16 da aka yi? Ko kuwa rayuwar 'yan Edo bata da daraja ne?
Yak**ata AIG ya mayar da hankali kan aikinsa, ba kokarin rage kimar masarauta ba. Masarautu al’adun mu ne, alfarma ce kuma tushen zaman lafiya.
Gwamnatin tarayya ta daina amfani da rundunar ‘yan sanda wajen cimma manufofinta na siyasa. Subar al’ummar Kano su zauna lafiya. Kuma a tabbatar da adalci ga wadanda aka kashe a Edo Mutanen Kano.
Abdoull Elberla...