25/12/2024
UZAIRIYYA NIGERIA
HAPPY CHRISTMAS
HALITTAR ANNABI ISA (A.S) BATARE DA UBA BA!
Daga:
Ruhullah Potisk*m
[email protected]
________________________
Shin halittar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, ba za a kidaya shi a matsayin abu ne mai babbar kima ba, k*ma fifiko ne? to idan haka al'amarin yake, me yasa wannan fifikon bai samu ba ga mafi daukakar halittu ba, wato Manzon mafi girma, Annabi Muhammad sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam. ?
SWALI
Shin halittar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, ba za a kidaya shi a matsayin abu ne mai babbar kima ba, k*ma fifiko ne? to idan haka al'amarin yake, me yasa wannan fifikon bai samu ba ga mafi daukakar halittu, wato Manzon mafi girma, Annabi Muhammad sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam. ?
Amsa a Dunkule
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, k*ma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a haifi mutum ba tare da uba ba ko da yake wani abu ne kebantacce fitacce wacce take da karfi sosai a wajen tabbatar da hujja, da isar da sakon Allah a wancan lokacin, to amma ba ta zamo a matsyain, wata kebancewa da fifiko akan kanta ba, da za a kirga wajen fifita mutum.
Hakika wannan kebancewar ta kasance wata hanya ce mai kyau a lokacin Annabi Isa (a. s) don isar da hukunce-hukucen Allah.
Sai dai k*ma idan muka yi dubi da yanda abubuwa suke a farkon musulunci, za mu ga yanda shirka ta baibaye ko ina, a cikin kiristoci da yahudawa, za mu ga yanda mushirikai na kasar hijaz suke sana'anta gumakansu da hannunsu, sannan k*ma su bauta musu.
Mai yiyuwa idan wani Manzon ya bayyana, shi ma aka haife shi ba tare da Uba ba, ta hanyar Mu'ujiza, zai sanya mushrikai, su yi zaton, wani sabon dan Allah ne, ke nan sai tunanunnaka na shirka su dawo a cikin sabon salo, wanda wannan k*ma bai dace da manufar koyarwar Allah ba game da aiko Manzanni. A saboda haka ne Ubangiji a cikin Kur’ani mai girma yake karfafawa akan dan'adamtaka na Annabi a wurare da yawa don ya dasa wannan imani a cikin zukatan mutane.
Amsa Dalla-dalla
Duk da yake Annabin Muslunci, shi ne mafificin Annabawa, k*ma ma fi daukakar daraja, sai dai hakan ba ya nufin cewa yana da dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Hususiyyarsu.
Akwai wasu kebance-kebance da siffofi na bai daya, wadanda ba su tsaya kawai a wani zamani daban, ko wani wuri kadai ba, k**ar ilimi, da kusanci da Allah, a wadannan hususiyyar (kebauce-kebance) Manzon Allah yana gaban dukkan Annabawa. Sai dai wasu siffofi wadanda sun shafi wani kebantaccen lokaci ne, to su ba dole ne, samuwar su ba, don tabbatar da fifikon Manzon Allah mafi girma.
Irin wadannan Al’amuran ba su zamo wajibi ba, samuwarsu ga Manzon Allah.
A hakika hanya ta dabi'a ta duniyar mu, shi ne cewa shi mutum ana haihuwarsa ne daga uba da uwa, wadanda ake ce musu mahaifa. To amma Allah ta'ala ya sanya wannan al'amarin ya canzu ga Annabawa guda biyu daga cikin Annabawa, ta yanda s**a zo duniya ba tare da uba da uwa ba, su ne Annabi Adam, ba Uba da uwa, da Annabi Isa an halicce shi ba tare da uba ba. Allah ta'ala, ya yi Ishara da haka a cikin wata aya daga cikin Ayoyin Kur’ani. Allah ta'ala ya ce "Hakika misalin Isa a wajen Allah, k**ar misallin Adamu ne, ya halicce shi daga turbaya sai ya ce masa zamo sai ya zamo".
hakika samuwar wadannan Annabawa guda biyu daga cikin Annabawan Allah dalili ne akan kudurar Allah azaliyya, wacce duk wasu dokoki na dabi'a, wadanda Allah subhanahu ya sanya su, shi ba su wajaba akansa ba, wato Allah wanda ya sanya dokar haihuwar mutum daga uba ne da uwa, wannan dokar shi bata hau kansa ba, k*ma hakika wannan al'amarin ya tabbata ta hanyar halittan Annabawa biyu daga cikin Annabawansa.
Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) da fifikon halittarsa ta dan adamtaka.
A farkon aiko Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) a wancan lokacin, su Yahudawa, da Nasara Mabiya Almasihu, sun karkata ga shirka, ko wani addini, daga cikin wadannan addinan sun sanya wa Allah da.
Allah ta'ala ya ce: ”Yahudawa sun ce Uzairu dan Allah ne, Nasara sunce Almasihu dan Allah ne”[2] k*ma a daidai wancan lokacin, mushirikan Hijaz, sun riki alloli masu yawa, suna ma zaton cewa Mala'iku ‘ya’ya ne mata na Allah. [3]
Hakika wadannan akidu sun yi karfi a wurin mutane, ta tabbata a cikin rayukansu, zuwa ga matsayin da ba su ma zaton wani Manzo, zai zo wanda yake cin abinci, yake shiga kasuwanni, k*ma yana zama a kasa yana barci, k**ar yanda suke barci, sai dai su manzo a ganinsu, ya wajaba ne, haihuwarsa da dukkan motsinsa, da rahsin motsinsa, da dukkan al'amaransa, su zamo al'amura ne wadanda ba na dabi'a ba.
To, a cikin wancan yanayi wanda ya gurbata da shirka, wanda k*ma, gaba daya an fi yarda da imanin cewa su Annabawa, ‘ya’yan Allah ne, ke nan idan aka haifi wani sabon Annabi, k**ar haihuwar Annabi Isa (a.s) ba tare da Uba ba, ko k**ar Annabi Adam (a. s). ke nan wasu irin hujjoji na barna zasu samu, a cikin kwakwalen mutane? shin wannan al'amarin ba zai sanya munanan akidu su kara samun karfi da tabbatuwa ba?
To, shin zai yiwu ga wani Annabi, wanda yake da irin wadannan siffofin, ya iya kiran mutane zuwa ga tauhidi, da ibadar Allah daya, k*ma yaci nasara a cikin da'awarsa?
Hakika Kur’ani ya yaki wadannan akidu, k*ma ya bayyana a wurare da yawa, k*ma a fili balo-balo, a cikin kunnuwar mutane, wannan babban sabanin, da irin a kidunsu, k*ma ya karfafa cewa shi Manzo, dan Adam ne irin halittarsu, a saboda haka ne za mu ga Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam), yana bayyanawa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, cewa shi mutum ne, k**ar sauran mutane, k*ma Kur’ani ya kasance yana zance da Annabin, yana nemansa akan ya bayyana wannan al'amarin ga mutane, yana k*ma karfafawa a kai, irin wannan ne ya zo a cikin fadarsa, madaukakin sarki cewa: "Ka ce iyaka kawai ni mutum ne irin ku, ana yin wahayi gare ni) [4] Natijar wannan magana ita ce, wannan hususiyyar idan ta kasance a zamanin Isa (a. s), za a iya kidaya ta a matsayin wata daraja ce don amfanarwa, da isar da sakon addini, to amma da ace ta faru ga Manzon Musulunci (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) da za a dauke ta a matsayin al’amari na raunana Addinin musulunci.
A cikin Kur’ani mai girma ana ambaton Isa Annabi (Alaihis salam) akan cewa shi kalmar Allah ce. [5]Ana yabon sa, ana girmama shi, k**ar sauran Annabawa akan hakuri, da turjiya[6] da zamowar sa Siddiki [7] k*ma Makusanci[8] k*ma mai yawan tuba[9] mai Basira [10] to amma bamu samu wani yabo da kwarzontawa ba, ga Annabi Isa (a. s) a cikin Kur’ani mai girma da ruwayoyin Ahlul bait a fuskar zawowansa an haife shi ne ba tare da uba ba.
A cikin wasu ayoyin, Allah Ubangiji madaukakin Sarki ya kidaya falala da ni'imomin da ya yi su ga Annabi Isa (a. s) da mahaifiyarsa, yana cewa: ”A lokacin da Allah ya ce ya kai isa dan Maryam, ka tuna ni'imata a kanka da mahaifiyarka a lokacin da na karfafa ka da ruhi mai tsarki, kana yin magana da mutane, alhali kana cikin tsumman goyo da lokacin da kake dattijo, da lokacin da na koyarda kai littafi da hikima da attaura da Injila, da lokacin da kake halitta suran tsuntsu daga tabo da izinina sai kayi huri a cikinta sai ta zamo tsuntsu da izini na, k*ma kana warkar da makaho da kuturu da izini na da lokacin da kake fitar da matattu da izini na, da lokacin da na kame banu Isra'ila daga barinka, a lokacin da ka zo musu da hujjoji sai wadanda s**a kafirta daga cikin su s**ace, hakika wannan ba komai ba ne sai dai tsafi a fili. )
Hakika haihuwar Annabi Isa (Alaihis salam) ta uwa kawai, k*ma ba tare da tana da miji ba, wani abu ne da ba a rasa hikima a cikinsa ba, ban da ma tabbatar da kudurar Allah buwayayye, gagara misali, marar iyaka, wacce dama su bani Isra'ila sun yi imani da ita, Ita haihuwar wata aya ce da hujja, a matsayin wata hanya ce ta shiryar da mutane, to amma wasu adadin mutane, sun fadi warwas, a wannan jarabawar.
Allah ya fada a cikin Kur’ani mai girma: (da wacce ta kiyaye farjinta sai muka hura ruhin mu a cikinsa, k*ma muka sanya ta da danta a matsayin aya ce ga halittu. ) [12]
Allama tabataba'i a kan ita wannan ayar ya ce: ”Wanann ayar ta kadaita su, wato ita Maryam da Isa (a. s) dukkansu biyu a matsayin aya guda daya ga halittu, don ayar ita ce haihuwar, k*ma ita Maryam ita ce farko wajen tsayuwar ayar, a saboda haka ne Allah ta'ala ya ce "mun sanya ta da danta a matsayin aya” amma bai ce: k*ma mun sanya danta da ita a matsayin aya ba) [13].
A saboda haka ke nan, wannan al'amari dalili ne akan kudurar Allah, k*ma hanya ce ta shiryar da mutane da jarabasu[14] duk da yake zai yiwu a ce mu'ujizar haihuwar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, a wancan lokacin, wanda ilimin magani yake tashe k*ma ya baibaye ko ina, ita mu'ujizar dalili ne akan kudurar Allah marar iyaka, k*ma wani nau'i ne, na girmamawa da fifitawa ga Annabi Isa (a. s) k*ma ya yi amfani da wannan daukakar, wajen isar da shari'arsa da hukunce hukucenta daga Allah.
[1] Suratu ali imran 59
[2] Suratut tauba aya ta 30
[3] Sun sanya wa Allah abokan tarayya a cikin aljannu alhali shi ya halicce su k*ma s**a kirkiri karyar cewa yana da ‘ya’ya maza da mata ba tare da suna da wani ilimi ba tsarki ya tabbata gareshi ya daukaka ga barin da abin da suke siffantawa, suratul an’ami aya ta 100.
[4] “s**a ce mene ne ya samu wannan manzon yana cin abinci k*ma yana tafiya a cikin kasuwanni ina ma da an sauko masa da mala’ika ya zamo mai wa’azi a tare da shi”
[5] Suratul kahafi, 11. suratu fussilat, 6
[6] Suratun nisa’i, 171
[7] Suratu maryam 14
[8] Suratu maryam 15
[9] Shafi na 17
[10] Shafi na 45
[11] Suratul ma’idah, aya ta 110.
[12] Suratul anbiya’i, aya ta 91.
[13] Littafin tarjumatul mizan, wallafar Muhammad Husain taba taba’i, juzu’i na 14, shafi na 447, maktab almanshurat al-islamiyya, k*m, 1347.
[14] Yazo a cikin wasu ruwayoyi cewa haihuwarsa jarawa ce ga mutane almas’udiy abul hasan a cikin littafinsa mai suna isbatul wasiyya lil imam aliyyu bin abi talib, shafi na 80, intisharat ansariyan, bugu na uku, 51624”an ruwaito cewa iblis ya tafi nemansa (neman annabi isa) a lokacin haihuwarsa day a iso wurinsa sai ya samu mala’iku sun kewaye shi, sai ya matsa zai je wajensa sai mala’iku s**a yi masa tsawa, sai ya ce:waye mahaifinsa?sai s**a ce masa:k**ar misalign annabi Adam yake. sai ya ce :na rantse da Allah sai nabatar da kaso hudu a cikin biyar na dukkan halittu a dalilinsa. ”
Daga cibiyar rubuce-rubucen na Uzairiyya Nigeria.
G-MAIL:- [email protected]
Facebook:- UZAIRIYYA NIGERIA or ROUHULLAH HARUNA DARUSSALAM
WhatsApp:- 08162819514
Kuci gaba da kasancewa dani Dr
Ruhullah Haruna Darussalam Amadadin Uzairiyya Nigeria