UGN HAUSA

UGN HAUSA Jarida don yada gaskiya zuwa ga Al'umma

UZAIRIYYA NIGERIA MUNA FARIN CIKI DA ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR SAYYIDA KHADIJA (AS)Yau Muna farin ciki da zagayowar ranar...
10/06/2025

UZAIRIYYA NIGERIA MUNA FARIN CIKI DA ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR SAYYIDA KHADIJA (AS)

Yau Muna farin ciki da zagayowar ranar haihuwar Matar Manzon Allah (S), Sayyida Khadija (as) wacce tazo duniyya a ranar 13 ga watan ZUL-HIJJA a Shekara Daya bayan shekarar Giwaye.
Sayyida Khadija (as) ta ba da gaggarumar Gudumawa Wajen kare Ma'aikin Allah (S) da Kuma ci gabantar da musulunci a lokacin da yake mawuyacin hali da dukiyarta.
Saboda irin wannan gudunmawa da Nana Khadijatu ta bayar ne aka rawaito.
Manzon Allah (S) yana cewa: "Ba don kariyar Abu Dalib ba, da Kuma dukiyar Khadija da Kuma takobin Ali ba, da Addini bai tsaya da kafarsa ba.

Sayyida Khadija (as) ta Kasance mace ta Masamman wacce tayi fi ce takere sa'annin ta cikin mata.
Maulaty Khadija Bata ta6ayin Sujuda ga Lata da Uzza ba domin tana da tsarkakan zuciya Kuma tayi gadon yakini.

Marhaba biki ya Khadijatu Kubra (as) Uzairiyya Nigeria khadimanki dakarun ki jarumanki ke Mikie jinjina ta Masamman gareki ya Maulaty.




Group Nigeria

UZAIRIYYA GROUP NIGERIAJADAWALIN GARURRUWAN DA ZA SU GABATAR DA MAULUDIN SAYYIDA KHADIJA (AS) NA 2025Tini Shirye-shiryen...
15/05/2025

UZAIRIYYA GROUP NIGERIA

JADAWALIN GARURRUWAN DA ZA SU GABATAR DA MAULUDIN SAYYIDA KHADIJA (AS) NA 2025

Tini Shirye-shiryen Maulud Na Sayyida Khadija (as) yayi nisa, a bana Muna da sababbin tsare-tsare.

A ranar 13 Ga Watan Zul Hijja Uzairiyya International Zamu Gabatar Da Gaggarumar Mauludin Sayyida Khadija a sassan kasa gaba Daya, a garurruwa k**ar haka:

1. MAIRUA✓
2. BAJOGA✓
3. JIGAWA✓
4. KANO✓
5. FAGGO✓
6.
7.
8.
9.
10.
11.

Afuwan ga dik garin da s**aji suna da ra'ayin raya wannan munasabar toh Kai Tsaye su tuntu6i KWAMITIN SHIRYE-SHIRYE A MATAKIN KASA BAKI DAYA

A Number Kamar Haka:
09155092532
08162819514
07036568788
07064367674
09066331935

KWAMITIN KULADA MUNASABOBIN SAYYIDA KHADIJA (AS)

© Uzairiyya Nigeria

SAKON BARKA DA SAFIYA    DAGA UZAIRIYYA GROUP NIGERIA        Imam Baƙir (AS) Yace:Mutum Ba Zai Kasance Malami Ba Har Sai...
29/01/2025

SAKON BARKA DA SAFIYA

DAGA UZAIRIYYA GROUP NIGERIA

Imam Baƙir (AS) Yace:Mutum Ba Zai Kasance Malami Ba Har Sai Ya Kasance Baya Hassada ga Wanda Yake Sama Dashi, Baya Kuma Wulaƙanta Wanda Yake ƙasa Dashi.

UGN HAUSA NEWS
©FATIMA AHMAD TIJJANI
29/1/2025

UZAIRIYYA NIGERIAHAPPY CHRISTMASHALITTAR ANNABI ISA (A.S) BATARE DA UBA BA!Daga:Ruhullah Potisk*mrouhullah202@gmail.com_...
25/12/2024

UZAIRIYYA NIGERIA
HAPPY CHRISTMAS

HALITTAR ANNABI ISA (A.S) BATARE DA UBA BA!

Daga:
Ruhullah Potisk*m

[email protected]
________________________

Shin halittar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, ba za a kidaya shi a matsayin abu ne mai babbar kima ba, k*ma fifiko ne? to idan haka al'amarin yake, me yasa wannan fifikon bai samu ba ga mafi daukakar halittu ba, wato Manzon mafi girma, Annabi Muhammad sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam. ?
SWALI
Shin halittar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, ba za a kidaya shi a matsayin abu ne mai babbar kima ba, k*ma fifiko ne? to idan haka al'amarin yake, me yasa wannan fifikon bai samu ba ga mafi daukakar halittu, wato Manzon mafi girma, Annabi Muhammad sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam. ?
Amsa a Dunkule
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, k*ma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a haifi mutum ba tare da uba ba ko da yake wani abu ne kebantacce fitacce wacce take da karfi sosai a wajen tabbatar da hujja, da isar da sakon Allah a wancan lokacin, to amma ba ta zamo a matsyain, wata kebancewa da fifiko akan kanta ba, da za a kirga wajen fifita mutum.

Hakika wannan kebancewar ta kasance wata hanya ce mai kyau a lokacin Annabi Isa (a. s) don isar da hukunce-hukucen Allah.

Sai dai k*ma idan muka yi dubi da yanda abubuwa suke a farkon musulunci, za mu ga yanda shirka ta baibaye ko ina, a cikin kiristoci da yahudawa, za mu ga yanda mushirikai na kasar hijaz suke sana'anta gumakansu da hannunsu, sannan k*ma su bauta musu.

Mai yiyuwa idan wani Manzon ya bayyana, shi ma aka haife shi ba tare da Uba ba, ta hanyar Mu'ujiza, zai sanya mushrikai, su yi zaton, wani sabon dan Allah ne, ke nan sai tunanunnaka na shirka su dawo a cikin sabon salo, wanda wannan k*ma bai dace da manufar koyarwar Allah ba game da aiko Manzanni. A saboda haka ne Ubangiji a cikin Kur’ani mai girma yake karfafawa akan dan'adamtaka na Annabi a wurare da yawa don ya dasa wannan imani a cikin zukatan mutane.

Amsa Dalla-dalla
Duk da yake Annabin Muslunci, shi ne mafificin Annabawa, k*ma ma fi daukakar daraja, sai dai hakan ba ya nufin cewa yana da dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Hususiyyarsu.

Akwai wasu kebance-kebance da siffofi na bai daya, wadanda ba su tsaya kawai a wani zamani daban, ko wani wuri kadai ba, k**ar ilimi, da kusanci da Allah, a wadannan hususiyyar (kebauce-kebance) Manzon Allah yana gaban dukkan Annabawa. Sai dai wasu siffofi wadanda sun shafi wani kebantaccen lokaci ne, to su ba dole ne, samuwar su ba, don tabbatar da fifikon Manzon Allah mafi girma.

Irin wadannan Al’amuran ba su zamo wajibi ba, samuwarsu ga Manzon Allah.

A hakika hanya ta dabi'a ta duniyar mu, shi ne cewa shi mutum ana haihuwarsa ne daga uba da uwa, wadanda ake ce musu mahaifa. To amma Allah ta'ala ya sanya wannan al'amarin ya canzu ga Annabawa guda biyu daga cikin Annabawa, ta yanda s**a zo duniya ba tare da uba da uwa ba, su ne Annabi Adam, ba Uba da uwa, da Annabi Isa an halicce shi ba tare da uba ba. Allah ta'ala, ya yi Ishara da haka a cikin wata aya daga cikin Ayoyin Kur’ani. Allah ta'ala ya ce "Hakika misalin Isa a wajen Allah, k**ar misallin Adamu ne, ya halicce shi daga turbaya sai ya ce masa zamo sai ya zamo".

hakika samuwar wadannan Annabawa guda biyu daga cikin Annabawan Allah dalili ne akan kudurar Allah azaliyya, wacce duk wasu dokoki na dabi'a, wadanda Allah subhanahu ya sanya su, shi ba su wajaba akansa ba, wato Allah wanda ya sanya dokar haihuwar mutum daga uba ne da uwa, wannan dokar shi bata hau kansa ba, k*ma hakika wannan al'amarin ya tabbata ta hanyar halittan Annabawa biyu daga cikin Annabawansa.

Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) da fifikon halittarsa ta dan adamtaka.

A farkon aiko Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) a wancan lokacin, su Yahudawa, da Nasara Mabiya Almasihu, sun karkata ga shirka, ko wani addini, daga cikin wadannan addinan sun sanya wa Allah da.

Allah ta'ala ya ce: ”Yahudawa sun ce Uzairu dan Allah ne, Nasara sunce Almasihu dan Allah ne”[2] k*ma a daidai wancan lokacin, mushirikan Hijaz, sun riki alloli masu yawa, suna ma zaton cewa Mala'iku ‘ya’ya ne mata na Allah. [3]

Hakika wadannan akidu sun yi karfi a wurin mutane, ta tabbata a cikin rayukansu, zuwa ga matsayin da ba su ma zaton wani Manzo, zai zo wanda yake cin abinci, yake shiga kasuwanni, k*ma yana zama a kasa yana barci, k**ar yanda suke barci, sai dai su manzo a ganinsu, ya wajaba ne, haihuwarsa da dukkan motsinsa, da rahsin motsinsa, da dukkan al'amaransa, su zamo al'amura ne wadanda ba na dabi'a ba.

To, a cikin wancan yanayi wanda ya gurbata da shirka, wanda k*ma, gaba daya an fi yarda da imanin cewa su Annabawa, ‘ya’yan Allah ne, ke nan idan aka haifi wani sabon Annabi, k**ar haihuwar Annabi Isa (a.s) ba tare da Uba ba, ko k**ar Annabi Adam (a. s). ke nan wasu irin hujjoji na barna zasu samu, a cikin kwakwalen mutane? shin wannan al'amarin ba zai sanya munanan akidu su kara samun karfi da tabbatuwa ba?

To, shin zai yiwu ga wani Annabi, wanda yake da irin wadannan siffofin, ya iya kiran mutane zuwa ga tauhidi, da ibadar Allah daya, k*ma yaci nasara a cikin da'awarsa?

Hakika Kur’ani ya yaki wadannan akidu, k*ma ya bayyana a wurare da yawa, k*ma a fili balo-balo, a cikin kunnuwar mutane, wannan babban sabanin, da irin a kidunsu, k*ma ya karfafa cewa shi Manzo, dan Adam ne irin halittarsu, a saboda haka ne za mu ga Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam), yana bayyanawa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, cewa shi mutum ne, k**ar sauran mutane, k*ma Kur’ani ya kasance yana zance da Annabin, yana nemansa akan ya bayyana wannan al'amarin ga mutane, yana k*ma karfafawa a kai, irin wannan ne ya zo a cikin fadarsa, madaukakin sarki cewa: "Ka ce iyaka kawai ni mutum ne irin ku, ana yin wahayi gare ni) [4] Natijar wannan magana ita ce, wannan hususiyyar idan ta kasance a zamanin Isa (a. s), za a iya kidaya ta a matsayin wata daraja ce don amfanarwa, da isar da sakon addini, to amma da ace ta faru ga Manzon Musulunci (sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) da za a dauke ta a matsayin al’amari na raunana Addinin musulunci.

A cikin Kur’ani mai girma ana ambaton Isa Annabi (Alaihis salam) akan cewa shi kalmar Allah ce. [5]Ana yabon sa, ana girmama shi, k**ar sauran Annabawa akan hakuri, da turjiya[6] da zamowar sa Siddiki [7] k*ma Makusanci[8] k*ma mai yawan tuba[9] mai Basira [10] to amma bamu samu wani yabo da kwarzontawa ba, ga Annabi Isa (a. s) a cikin Kur’ani mai girma da ruwayoyin Ahlul bait a fuskar zawowansa an haife shi ne ba tare da uba ba.

A cikin wasu ayoyin, Allah Ubangiji madaukakin Sarki ya kidaya falala da ni'imomin da ya yi su ga Annabi Isa (a. s) da mahaifiyarsa, yana cewa: ”A lokacin da Allah ya ce ya kai isa dan Maryam, ka tuna ni'imata a kanka da mahaifiyarka a lokacin da na karfafa ka da ruhi mai tsarki, kana yin magana da mutane, alhali kana cikin tsumman goyo da lokacin da kake dattijo, da lokacin da na koyarda kai littafi da hikima da attaura da Injila, da lokacin da kake halitta suran tsuntsu daga tabo da izinina sai kayi huri a cikinta sai ta zamo tsuntsu da izini na, k*ma kana warkar da makaho da kuturu da izini na da lokacin da kake fitar da matattu da izini na, da lokacin da na kame banu Isra'ila daga barinka, a lokacin da ka zo musu da hujjoji sai wadanda s**a kafirta daga cikin su s**ace, hakika wannan ba komai ba ne sai dai tsafi a fili. )

Hakika haihuwar Annabi Isa (Alaihis salam) ta uwa kawai, k*ma ba tare da tana da miji ba, wani abu ne da ba a rasa hikima a cikinsa ba, ban da ma tabbatar da kudurar Allah buwayayye, gagara misali, marar iyaka, wacce dama su bani Isra'ila sun yi imani da ita, Ita haihuwar wata aya ce da hujja, a matsayin wata hanya ce ta shiryar da mutane, to amma wasu adadin mutane, sun fadi warwas, a wannan jarabawar.

Allah ya fada a cikin Kur’ani mai girma: (da wacce ta kiyaye farjinta sai muka hura ruhin mu a cikinsa, k*ma muka sanya ta da danta a matsayin aya ce ga halittu. ) [12]

Allama tabataba'i a kan ita wannan ayar ya ce: ”Wanann ayar ta kadaita su, wato ita Maryam da Isa (a. s) dukkansu biyu a matsayin aya guda daya ga halittu, don ayar ita ce haihuwar, k*ma ita Maryam ita ce farko wajen tsayuwar ayar, a saboda haka ne Allah ta'ala ya ce "mun sanya ta da danta a matsayin aya” amma bai ce: k*ma mun sanya danta da ita a matsayin aya ba) [13].

A saboda haka ke nan, wannan al'amari dalili ne akan kudurar Allah, k*ma hanya ce ta shiryar da mutane da jarabasu[14] duk da yake zai yiwu a ce mu'ujizar haihuwar Annabi Isa (a. s) ba tare da Uba ba, a wancan lokacin, wanda ilimin magani yake tashe k*ma ya baibaye ko ina, ita mu'ujizar dalili ne akan kudurar Allah marar iyaka, k*ma wani nau'i ne, na girmamawa da fifitawa ga Annabi Isa (a. s) k*ma ya yi amfani da wannan daukakar, wajen isar da shari'arsa da hukunce hukucenta daga Allah.



[1] Suratu ali imran 59

[2] Suratut tauba aya ta 30

[3] Sun sanya wa Allah abokan tarayya a cikin aljannu alhali shi ya halicce su k*ma s**a kirkiri karyar cewa yana da ‘ya’ya maza da mata ba tare da suna da wani ilimi ba tsarki ya tabbata gareshi ya daukaka ga barin da abin da suke siffantawa, suratul an’ami aya ta 100.

[4] “s**a ce mene ne ya samu wannan manzon yana cin abinci k*ma yana tafiya a cikin kasuwanni ina ma da an sauko masa da mala’ika ya zamo mai wa’azi a tare da shi”

[5] Suratul kahafi, 11. suratu fussilat, 6

[6] Suratun nisa’i, 171

[7] Suratu maryam 14

[8] Suratu maryam 15

[9] Shafi na 17

[10] Shafi na 45

[11] Suratul ma’idah, aya ta 110.

[12] Suratul anbiya’i, aya ta 91.

[13] Littafin tarjumatul mizan, wallafar Muhammad Husain taba taba’i, juzu’i na 14, shafi na 447, maktab almanshurat al-islamiyya, k*m, 1347.

[14] Yazo a cikin wasu ruwayoyi cewa haihuwarsa jarawa ce ga mutane almas’udiy abul hasan a cikin littafinsa mai suna isbatul wasiyya lil imam aliyyu bin abi talib, shafi na 80, intisharat ansariyan, bugu na uku, 51624”an ruwaito cewa iblis ya tafi nemansa (neman annabi isa) a lokacin haihuwarsa day a iso wurinsa sai ya samu mala’iku sun kewaye shi, sai ya matsa zai je wajensa sai mala’iku s**a yi masa tsawa, sai ya ce:waye mahaifinsa?sai s**a ce masa:k**ar misalign annabi Adam yake. sai ya ce :na rantse da Allah sai nabatar da kaso hudu a cikin biyar na dukkan halittu a dalilinsa. ”

Daga cibiyar rubuce-rubucen na Uzairiyya Nigeria.
G-MAIL:- [email protected]
Facebook:- UZAIRIYYA NIGERIA or ROUHULLAH HARUNA DARUSSALAM
WhatsApp:- 08162819514

Kuci gaba da kasancewa dani Dr
Ruhullah Haruna Darussalam Amadadin Uzairiyya Nigeria

25/12/2024

An ruwaito cewa; Yayinda Maryam ta je wajen mutanen ta tana ɗauke da Annabi Isah (A.S.) sai s**a ce; Ya ke Maryam lallai kin zo da babban lamari, ya 'yar'uwar Haruna mahaifinki ba mutumin banza ba ne, mahaifiyarki ma ba mutuniyar banza ba ce. Yayinda ta ji wannan zargi daga mutanenta sai ta yi musu nuni da Annabi Isah tana nufin su tambaye shi. Sai s**a ce: Ta ya ya za mu yi magana da jariri a cikin zanin goyo?
Sai Allah ya buɗi bakin Annabi Isah ya ce da su:

"Ni bawan Allah ne ya bani littafi yasan yani Manzo yayi albarka a gareni duk inda nake yayimin wasiyya da sallah da Zakka matukar ina raye, sannan da yin biyayya ga Mahaifiyata. Bai san yani shakiyyi mai girman kai ba, farkon Kalmar da Annabi Isah ya fara magana da ita itace, ni bawan Allah ne domin yanke hanzari ga wadanda za s**e shi dan Allah ne.

Rouhullah Haruna Darussalam
UGN HAUSA

An ruwaito daga Salmanul Farisi (R.A.) ya ce: hawariyawa sun faxa ga Annabi Isah s**a ce shin Ubangijinka zai iya suako ...
25/12/2024

An ruwaito daga Salmanul Farisi (R.A.) ya ce: hawariyawa sun faxa ga Annabi Isah s**a ce shin Ubangijinka zai iya suako mana da Ma'ida daga sama? Sai ya'amsa musu ya ce, ku dai ku ji tsoron Allah in kun kasance muminai, sai s**a ce lallai muna da buqatar haka, sai Annabi Isah ya fita ya shiga sahara ya yi ta kuka yana qanqan da kai ga Allah yana cewa: "Ya Ubangiji ka saukar mana da Ma'ida daga sama domin ta zama idi ga na farkonmu da na qarshenmu, ta kasance aya daga gareka, ka arzurtamu kai ne fiyayen mai arzutawa."
Sai Allah ya yi wahayi gare shi ya ce: "Ni zan saukar da ita gareku, amma wanda duk ya kafirta a cikinku bayan wannan haqiqa zan masa azaba irin wadda ban tava yiwa wani irinta ba, a cikin talikai."

Imamutturmuzi ya ce: Sai Allah ya saukar musu da teburin abinci daga sama a tsakanin giragizai guda biyu, yayin da Annabi Isah ya ganta sai ya ce: Ya Ubangiji ka sanya ta zama Rahama, kada ta zama azaba.
Ba ta gushe ba tana saukowa a hankali a hankali har sai da teburin abincin nan ya sauko qasa mutane na kallo an lulluve shi da mayafi, sai Annabi Isah ya fadi ya yi sujjada ga Allah ya yi godiya. Hawariyawa suma s**a yi sujjada tare da shi, sannans uka ce Annabi Isah ya tashi ya bude su ga abinda yake ciki. da aka bude sai ga soyayyen kifi da zaitun da dabino da gurasa, da wani nau'in kayan marmari. Sannan sai Annabi Isah ya cewa kifin nan tashi da izinin Allah, sai Allah ya raya kifin ya riqa juyawa yana kallon jama'ar Banu Isra'ila, sannan sai ya cewa kifin ya koma yadda yake da izinin Allah. sai Hawariyawa s**a cewa Annabi Isah shi ya k**ata ya fara cin abincin nan. Sai ya ce: A'a wanda ya nemi a kawo shi zai ci. sai duk s**a qi ci, suna tsoron kada ta zama fitina, sai ya sa aka kirawo talakawa da miskinai da guragu da makafi, ya ce su ci. A cikinsu har da marasa lafiya da masu cutar albasar da sauransu duk s**a haxu s**a ci abincin. Suna gama ci marasa lafiyar nan sai duk s**a warke, nan take. Yayin da mutanen gari s**a ji labari sai suma s**a zo s**a ci, har s**a riqa turereniya, da Annabi Isah ya ga haka sai ya sa aka kasa mutane kashi biyu, rana daya ta talakawa, rana daya k*ma ta mawadata.

Sai Ma'idar ta zama tana sauka sau daya bayan kwanaki biyu. Sannan k*ma wannan tebur idan ya sauka duk yawan mutanen da suke wajen kowa zia ci ya qoshi, ya bari sannan ya tashi ya koma sama k**ar yadda ya sauko. An ce haka Ma'idar nan ta riqa sauka har tsawon kwana arba'in. Sannan sai wata jama'a daga Bani Isra'ila s**a aibata Ma'idar s**a ce ba Allah ne yake saukar da ita ba, da s**a faxi haka, sai Allah ya mayar da wasunsu aladu, wasu k*ma birori. An ce adadin waxanda s**a haxu da wannan matsala sun kai mutum talatin, s**a zuana a cikin wannan hali tsawon kwanaki bakwai sannan sai qasa ta haxiye su.

*m

HAIHUWAR ANNABI ISA (AS) DAN MARYAM!DAGA UZAIRIYYA INTERNATIONAL ⌨️ National Editor Ruhullah rouhullah202@gmail.com ANNA...
25/12/2024

HAIHUWAR ANNABI ISA (AS) DAN MARYAM!

DAGA UZAIRIYYA INTERNATIONAL
⌨️ National Editor Ruhullah
[email protected]

ANNABI ISA (AS)::

Yayin da Nana Maryam ta kai munzalin girma sai al'ada ta zo mata, saboda haka, sai ta fita bayan gari wajen wata qorama don ta yi tsarki, sai Mala'ika Jibril ya zo mata a siffar wani saurayi daga Banu Isra'ila mai suna Taqiyyu, shi wannan mutum ya yi qaurin suna da ɓarna a wannan lokaci Allah Madaukakin Sarki ya ce, "Sai muka aika mata da ruhu (shi ne Mala'ika Jibrilu) ya je mata a surar saurayi, sai ta ce "Ni ina neman tsari da Ubangijin Rahama daga gareka idan kai ne Taqiyyu. "Sai Mala'ika Jibril ya ce, mata "Ni Manzon Ubangijinki ne, Allah ne ya aiko ni. Domin in ba ki kyautar ɗa mai qwazo.

"Sai ta ce da shi: Ta ya ya zan sami ɗa, bayan wani mutum bai shafe ni ba, k*ma ni ban taɓa yin alfasha ba? Sai ya ce: Haka al'amarin yake, haka Allah Ya hukunta, k*ma wannan abu ne mai sauqi a wajen Allah. Allah ya ce: "Za mu sanya shi ya zama izina a wajen mutane, k*ma Rahama daga garemu, wannan lamari ne zartacce." (Surar Maryam, Aya ta 17) Mala'ika Jibrilu yana gama wannan bayanin sai ya k**a gefen rigarta ya yi busa a ciki, nan take sai Allah ya halicci Annabi Isah a cikin cikinta. Malam wahabu ya ce: Tsakanin ɗaukar cikin Annabi Isah da haifarsa sa'a guda ne kawai, saboda faɗin Allah Ta'ala ya ce, "Sai ta ɗauki cikinsa, sai ta tafi da shi wuri mai nisa, sai naquda ta zo mata a wajen kututturen dabino, sai ta ce: Ya kaicona dama na mutu kafin faruwar wanan na zama mantacciya abar mantawa."

Sai Allah ya ce; Sai muka kirata ta qarqashinta muka ce: Kada ki yi baqin ciki, Allah ya gudano da qoramar ruwa a kusa da ke, ki girgiza kututturen dabinon nan zai zubo miki da lubiya nunanniya, ki ci, ki sha, ki kwantar da hankalinki. An ce wannan dabinon da ta girgiza shekararsa saba'in bai yi 'ya'ya ba, amma ana haihuwar Annabi Isah a kusa da shi, nan take sai ya yi ganyen, ya fitar da 'ya'ya saboda mu'ujizar Annabi Isah (A.S.)

RUWAYA:

An ruwaito cewa; Yayinda Maryam ta je wajen mutanen ta tana ɗauke da Annabi Isah (A.S.) sai s**a ce; Ya ke Maryam lallai kin zo da babban lamari, ya 'yar'uwar Haruna mahaifinki ba mutumin banza ba ne, mahaifiyarki ma ba mutuniyar banza ba ce. Yayinda ta ji wannan zargi daga mutanenta sai ta yi musu nuni da Annabi Isah tana nufin su tambaye shi. Sai s**a ce: Ta ya ya za mu yi magana da jariri a cikin zanin goyo?
Sai Allah ya buɗi bakin Annabi Isah ya ce da su:

"Ni bawan Allah ne ya bani littafi yasan yani Manzo yayi albarka a gareni duk inda nake yayimin wasiyya da sallah da Zakka matukar ina raye, sannan da yin biyayya ga Mahaifiyata. Bai san yani shakiyyi mai girman kai ba, farkon Kalmar da Annabi Isah ya fara magana da ita itace, ni bawan Allah ne domin yanke hanzari ga wadanda za s**e shi dan Allah ne.

Anruwaito cewea yayin da Annabi Isah ya girma sai yarika yawo aba yan kasa, baya zama da waje daya, saboda haka ma bai taba mallakar dakin kwana ba. Bare gida ko mata, ko abun hawa tufafinsa k*ma jubbace ta sufi. Baya cin abinci sai daga kasabin Mahaifiyarsa ta kasance tana saka tufafi tasiyar suci abinci. a irin wayace-wayacen da yake yi ya je wani gari da ake cewa Nasira a qasar Sham, shida mahaifiyarsa s**a zauna a can.
Saboda haka ne ake dan ganta mutanensa da sunan wannan garin ake ce musu NASARA.

SALATIN ANNABI MAI LADAR SALLAH RAKA'A 70👉🏻Dr. Ruhullah Potisk*m             UZAIRIYYA NIGERIAAbu Basirin ya ce; "Na ji ...
24/12/2024

SALATIN ANNABI MAI LADAR SALLAH RAKA'A 70

👉🏻Dr. Ruhullah Potisk*m
UZAIRIYYA NIGERIA

Abu Basirin ya ce; "Na ji Imam Sadiq (AS) Yana Cewa; "Ladar mutumin da ya yi wa Annabi da iyalan gidansa Salati a tsakanin Alfijir da fitowar Rana, tamkar ladar mutumin da ya yi Sallah raka'a Saba'in ne!"
(Safeenatul Bihar, 02-50)



WANNAN SHI NE 'POSTING' DIN DA SHAHID SAYYID BASHIR YA YI NA KARSHE KAFIN SOJOJI SU KASHE SHI.Sai yanzu muka san cewa Bu...
13/12/2024

WANNAN SHI NE 'POSTING' DIN DA SHAHID SAYYID BASHIR YA YI NA KARSHE KAFIN SOJOJI SU KASHE SHI.

Sai yanzu muka san cewa Burutai ne ya kawo mana hari! Abin da kawai muka sani k**ar wasa, dazu da rana an kawo Sojoji masu yawa a cikin wata katuwar motar Soji aka aje su a gaban Hussainiyyah Bakiyatullahi Zariya. 'Yan'uwa ba su aminta da su ba, saboda a shekarar 2014 da rana tsaka Sojoji da kaki karkashin wani Laftanar-Kanar S. Oku s**a bude mana wuta a PZ da Hussainiyyah. Don haka an nemi a ji dalilin zuwansu su tsaya a nan wajen dai, sai ba su fadi ba. Har wasu a cikin mu sun fara yi musu uzurin wai ko sun zo bikin yaye daliban Soji ne! Muka ce, to a Hussainiyyah ake yaye daliban Sojojin ko a Bariki?

Ba jimawa s**a fara harbe-harbe sama ba tare da wani ya ce musu uffan ba. Kuma hotuna da 'Video clips' na nan na lamarin. Daga bisani k*ma s**a fara harbi kan 'yan'uwa Musulmi da ke Eriyar muhallin na Hussainiyyah, wadanda sun zo wajen a yau ne don bikin sauya Tutar Ashura zuwa ta Maulud saboda sanarwar da ta gabata cewa yau za a yi.

To, abin mamaki, sai yanzu muke ganin kafar Yahudawa ta BBC sun rubuta cewa wai Shugaban Sojojin Nijeriya ya tsallake rijiya da baya. Wai an yi masa kwanton bauna. Wai an kai masa hari. To, yanzu ne ma muka ji ashe wannan karon Shugaban Sojojin Nijeriya da kansa ne ya zabi ya kawo mana harin k*ma da tsakar rana, tare da yin karya baro-baro, wai an yi masa kwanton bauna an nemi a kai masa hari. Yaushe hankali zai dauki wannan sakarci da wautar maganar taku? Mutanen da ba su da ko reza da sunan makamin yaki, shi ne za su kai muku hari?

Waye ma a tarihin wannan harkar da ta shekara kusan 40 ta taba kai masa hari? Su hare-haren da kuke kai mana, akwai abin kariyar kanmu da ya wuce jifa da dutse da kiran sunan Allah? Waye za ku mai da wawa!? Waye bai san ku kuke kashe mutane ba, ba dare, ba rana ba, da sunan wata tsiya wai ita Boko Haram?! Kashe 'Ya'yan Malam Zakzaky da Almajiransa da kuka yi a 2014, waye bai san ku kuka yi ba? Waye bai san kun yi hakan ne don ku mai da yankin k**ar Borno da Yobe ba? Muna da karfin da ya wuce naku?! Karfinmu k*ma shi ne Allah (T). Kar ku fasa kisa, kar ku fasa sharri. Amma ba za ku mai da mu shashashu ba!

Sayyed Bashir Shahid Adam, December 12, 2015 karfe 8:27nd.

Duka Wadan Nan Dakuke ganin Fuskokinsu Sojojin Nigeria Sun Shahadantar Dasu a Zaria Bisa Umar Janar Buhari (L.A)
13/12/2024

Duka Wadan Nan Dakuke ganin Fuskokinsu Sojojin Nigeria Sun Shahadantar Dasu a Zaria Bisa Umar Janar Buhari (L.A)

MAGANAR SHEIKH ZAKZAKY (H) A RANAR 12/12/2015 "Wallahi karyane! kasan dai yau shekaranmu 37 cur muna harkar nan, sau naw...
13/12/2024

MAGANAR SHEIKH ZAKZAKY (H) A RANAR 12/12/2015

"Wallahi karyane! kasan dai yau shekaranmu 37 cur muna harkar nan, sau nawa muka taba kai wa wani hari?. Soja yake ko dan sanda ko wani mutum. Wai har munyi kokarin halaka Tukur Burutai, Sau nawa soja na wucewa ta Husainiyya? Yaushe aka taba kai wa wani hari?Ina ganin da ma kame kame suke yi".

"Yanzu haka an yi mana kawanya. Tun sama da awowi 12 suke ta harbi a kan gidana. Sun rusa mana Husainiyya da manyan bama -bamai, yanzu k*ma suna kawo hari gidana. A yanzu haka ma suna harbin bangwayen gidan ne. Sun zo nan tun misalin karfe 10:00 na dare ranar Asabar. Kuma tun lokacin harbi suke yi kawo lokacin da muke maganar nan".

"Hakika rayuwata tana cikin hatsari. Amma ba abin da na iya yi, Allah ne kawai zai kubutar da ni, saboda ba wata mafita. Sun riga sun yi wa gidan kawanya. Suna kowa ne lungu da zai iya kawo wa zuwa gidan nan. Ya zuwa yanzu da nake magana ba mu san adadin mutum nawa s**a kashe ba".

- Sheikh Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H) a ranar 12/12/2015, Ranar da Gwamnatin Nijeriya ta afka masa a gidansa dake Gyallesu Zaria. Ibrahim Almustapha Saminaka ya naqalto muku.

Address


Telephone

+2348106511583

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when UGN HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to UGN HAUSA:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share