11/04/2024
Chain Economic and Staked Tokens:
___________________________
Wani lokaci zaka dinga ganin circulating supply na token yana 'karuwa, wani lokaci sai kaga ya ragu musamman akan chain din dake amfani da PoS a matsayin Consensus mechanism dinsa, already mun riga mun sani cewa duk lokacin da circulating supply ya 'karu toh dole farashin Coin ko token zai ragu in dai ba tokens da aka sako an hada su da Kudin su a tafe ba toh dole farashi zai sauka, wato zai yi dumping.
~ Sai dai a cikin rashin sani a lokuta da yawa mukan zargi developers da 'kara circulating supply, mukan zarge su da yin dumping ko rage Kudin dake cikin liquidity, amma kaso 90 cikin 'dari na zargin da muke yiwa developers ba gaskiya bane, rashin fahimtar me yake gudana akan Blockchain din ne yasa muke zargin su duk lokacin da muka ga supply ya karu ko anyi dumping me yawa.
Muna magana ne akan abubuwan da suke faruwa akan Blockchains da suke amfani da PoS (Proof of Stake) a matsayin Consensus mechanism dinsu, ko similar consensus mechanism kamar DPoS, PoL, PoA, PoH da sauran su.
~ Idan kaga Blockchain yana amfani da PoS ko similar consensus mechanism da PoS toh ana yin staking akan sa, staking din kuma zai iya zama Custodial Staking ko Non custodial Staking, duk tokens din da aka yi staking dinsu sun fita daga circulating supply, duk tokens din da aka yi staking dinsu cannot be traded, ba za'a iya sayan su ko siyar dasu ba, sannan duk token din da aka yi staking dinsu babu liquidity akan su.
Misali:
Bari in bayar da misali da CORE namu na gargajiya inji 'yan Baiwa, Engineer Adam Muhammad Mukhtar ya sayi CORE guda Miliyan 20,000,000 bayan ya saya sai yaje yayi staking dinsu su gaba daya, toh a zahiri zamu ga cewa an kwashe CORE guda Miliyan 20 daga circulation, sannan price din zai yi sama a wannan lokacin matukan babu wani selling force da yafi na yawan abinda Engineer yayi staking.
~ Hakan zai sa muyi farin ciki, amma duk ranar da Engineer yaje ya cire CORE dinsa guda Miliyan 20 daga staking, toh sun dawo kasuwa kenan, circulating supply zai 'karu, tokens din zasu shiga cikin liquidity pool su samu wajen zama, hakan zai shafi farashin sauran coins din da suke kasuwa.
Kaga circulating supply ya 'karu amma waye ya 'kara? developers ko investor? amsa itace investor ne, developers suma sai dai su gani kawai, domin basu da ikon hana Engineer cire coins dinsa daga staking.
~ Dan haka mu kiyaye cewa tokens din da aka yi staking dinsu:
1. Sun fita daga cikin circulating supply.
2. Basu da liquidity akan su.
3. Ba za'a iya trading dasu ba.
Har sai ranar da aka kunce su (aka yi unstake dinsu).
Sannan kafin mu zargi developers da yin dumping ko 'kara yawan supply na token muje mu duba currently action dinsu, abun nufi shin dama suna da wasu tokens da suke sakewa duk sati (Weekly) ko duk wata (Monthly) ko quarterly ko annually?
~ Misali RENEC da CORE da AVIVE idan kaga circulating supply ya 'karu dama already suna kan aikin sakarwa mutane tokens dinsu ne.
Sannan kaje ka duba shin suna da wani tsari da ake minting sabbin tokens? idan suna dashi toh kada ka zarge su, investors ko users ne s**a 'kara circulating supply, sai dai ka zarge su akan sun kawo tsarin da bai kamaci token dinsu ba a fahimtar ka.
~ Sannan idan circulating supply ya ragu ba zaka ga ya Canza total ko maximum supply ba, kamar coins din da aka yi burning dinsu ne, ko bayan an 'kona su ba zaka ga total supply ya Canza ba, zaka ga canjin ne kawai akan circulating supply.
Wani zai ce toh menene ya banbanta staking da burning 🔥?
Abu 'daya ne:
Shine "Resurrection Power" wato damar dawowa, su token din da aka kulle su (staked tokens) kamar mutumin da aka kulle shi a gidan Yari ne, baya da Takalma a kafar sa, baya da hula akan sa, baya da Kudi a hannun sa.
~ Duk ranar da aka kunce shi ya fito gari toh zai sa Riga (ya dawo cikin jama'a, circulation) zai sa hula (za'a iya trading, ko mu'amala dashi) sannan zai iya rike Kudi a hannun sa (yana da Liquidity) kenan.
Yayin da su kuma tokens din da aka yi burning dinsu, kamar mutumin da aka jefa shi a Rijiya mai Gaba dubu ne, ko aka saka shi a Kabari.
~ Ya tafi kenan babu damar dawowa, sai dai idan an tashi kirga mutanen gidan su za'a iya kirgawa dashi (in the total supply, among the members) amma babu shi a zahiri (in circulation).
Daga karshe a galibin lokuta idan developers sunyi renouncing token contract toh babu damar 'kara yawan maximum supply ko total supply. Allah yasa mu dace...
~ Na tabbata daga wannan bayanin ka fara hasaso yadda developers suke iya pumping token ba tare da wata babbar matsala ba, Allah yasa mu dace. Sauran bayanan zasu zo wani lokaci a nan gaba lokaci in sha Allah.