
28/08/2025
MAULUDIN ANNABI S,A,W KASHI (3)
BAYANIN SHAYAR DA ANNABI S A W
๐ฒ๐ฒ
Saiyada Halimatu sa adiya takasance macece Wanda take cikin kunci na rayuwa masamman wajan abinci Amma takasance aduk halinda tasami kanta narayuwa na wadata ko kunci ko talauci sai tace Alhmdu lillahi
๐ฒ๐ฒ
Sai tasamu ciki suna cikin wannan halin na rashi ta haifi yaron nata babu abinci babu ruwan nonon dama yaron zaisha saboda babu abinci sai tace Allah kaciyar damu daga arzikin kasanka kawa sai taji murya anace mata zaki ciyar da danki zaki shayar dashi kuma zaki tar biyartar dashi
๐ฒ๐ฒ
Kawai tana bacci sai taga wani mutun yakama hannunta yakaita wani korama ruwa wanda farinshi yafi nono zakinshi yafi zuma yace Mata Kisha tace nasha dayawa sai yace mata kinsan koni wanene tace a a yace nine kalman nan da k**e yawan fadi na Alhmdu lillahi
๐ฒ๐ฒ
Saiyada Halimatu tace ina farkawa naga nonona sun cicciko har mutanan garinmu suna mamakina nakara gyau da kiba gari nawayewa sai muka tafi gona da matayen gari
๐ฒ๐ฒ
Kawai sai mukaji murya ko taina gabas da yamma kudu da arewa anace mana Anhaifi wani abin haihuwa acikin garin makka aljannan Allah ta tabbata gadukkan wanda tashayar dashi
๐ฒ๐ฒ
Kawai matannan kowa tayi sauri Takoma gida domin tanemi izinin mijinta ta tafi makka Dan dauko wannan jaririn da aka haifa sunyi zatton dan masu kudine ko Dan sarakunane
๐ฒ๐ฒ
Allahu kabamu wani martaba da hususiya da mukamai acikin gidan Annabi Muhammadu s a w Aduniya da lahira
๐ฒ๐ฒ
๐๐ผ๐๐ผ SAUTIN๐๐ผ๐๐ผKUSFA