23/06/2026
Jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq Ya Jaddada Aniyarsa Ta Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana
Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya sake jaddada aniyarsa ta gudanar da zanga-zangar lumana domin bayyana damuwa kan matsalolin tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, garkuwa da mutane da kuma kalubalen tattalin arziki da ke addabar al’ummar Najeriya.
Jarumin ya bayyana cewa ya saurari ra’ayoyi da shawarwari daga bangarori daban-daban, ciki har da masu goyon bayan shirin da kuma wadanda ke adawa da shi, amma ya ce hakan ba zai sa ya yi watsi da kudurinsa ba.
A wata sanarwa da ya fitar, Sadiq ya tabbatar da cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin tsari da lumana, yana mai jaddada cewa manufarta ita ce isar da sakon al’umma cikin bin doka da oda.
“Na saurari dukkan shawarwarinku kuma ina matukar godiya da gudunmawar da kuka bayar. Sai dai ba zan fasa gudanar da zanga-zangar ba, In Sha Allah. Za mu gudanar da ita cikin lumana,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa nan gaba kadan za a fitar da cikakken bayani kan yadda za a gudanar da zanga-zangar, tare da bayyana matakan da za a bi domin tabbatar da zaman lafiya da kauce wa duk wani tashin hankali.
Shirin zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalolin tsaro da matsin rayuwa da ke fuskantar al’umma a sassa daban-daban na kasar nan.