Daily Enquirer Hausa

Daily Enquirer Hausa News/Media Website
(2)

TARIHI BAYA MANTUWA : A shekarar 2000, a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo, Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar ayy...
19/03/2025

TARIHI BAYA MANTUWA : A shekarar 2000, a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo, Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar ayyana dokar taɓaci a Jihar Legas, a lokacin Bola Ahmed Tinubu ke gwamna.

Dalilin da aka bayar shi ne don dakile ayyukan kungiyar Oodua People's Congress (OPC), wata ƙungiyar ‘yan aware ta Yarbawa da aka zarga da haddasa rikice-rikice da tashin hankali a wancan lokaci.

Duk da barazanar, gwamnatin Obasanjo ba ta aiwatar da dokar a Jihar Legas ba. Wannan lamari yana bada wani sabon hangen nesa kan matakin da Tinubu ya ɗauka a 2025 na ayyana dokar taɓaci a Jihar Ribas.

HATSARI BIYU SUN CANZA RAYUWAR NURADDIN, AMMA BASU DAKUSHE BURINSA BANuraddin ya fuskanci manyan jarabawa guda biyu a ra...
18/03/2025

HATSARI BIYU SUN CANZA RAYUWAR NURADDIN, AMMA BASU DAKUSHE BURINSA BA

Nuraddin ya fuskanci manyan jarabawa guda biyu a rayuwar sa—hatsarurruka da s**a bar shi da nakasa, amma bai bar hakan ya hana shi ci gaba da rayuwa da kwazon sa ba.

An haifi Nuraddin a shekarar 1991 a karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano. Rayuwar sa ta fara kamar ta kowane yaro mai lafiya, ya kuma fara makarantar firamare da himma. Bayan kammala firamare a 2003, ya shiga sana’ar injin nika don tallafawa iyayensa. A nan ne hatsari na farko ya auku—hannunsa ya makale a injin nika, wanda ya tilasta a yanke shi. Duk da haka, bai karaya ba, ya koma sana’ar sayar da fetur a bakin t**i, har ya samu damar ci gaba da karatun sakandire.

Bayan ya kammala sakandire a 2014, ya samu gurbin karatu a Northwest University, Kano, kuma ya dauki nauyin kansa har ya kai ga bautar kasa a 2019. Lokacin da ya shiga sansanin NYSC, an ba shi damar komawa gida saboda lalurar da ke tare da shi, amma ya nace cewa zai iya yi wa kasa hidima a ko'ina.

Hakan ya kai shi Taraba, inda hatsari na biyu ya faru. A hanyarsu ta zuwa garin Gembu, motarsu ta yi mummunan hadari. A sakamakon haka, hannunsa na dama ya yanke, kuma idonsa guda daya ya samu matsala mai tsanani. An dauki tsawon lokaci ana jinyar sa, an kuma yi masa aiki don sanya hannun roba. Duk da matsalolin da s**a faru, bai tsaya ba—ya cigaba da kokarin inganta rayuwarsa.

A karshe, Nuraddin ya samu aiki a Kano State Polytechnic, daga nan kuma aka tura shi Nigeria Social Insurance Trust Fund (NSITF). Duk da irin jarabawarsa, bai taba barin burinsa ba.

Yanzu haka yana fuskantar wasu kalubale biyu: jinkirin ci gaba da kula da idonsa a Kaduna, da kuma sharadin da asibitin Legas ya gindaya na komawa bayan wata uku don duba hannun roba da aka sanya masa.

Nuraddin ya zama abin koyi na jajircewa, kwazo, da nuna cewa nakasa ba ita ce karshen rayuwa ba.

Tinubu Ya Cutar da Al’ummar Rivers Ta Hanyar Ƙaƙaba Dokar Ta ɓaci — AtikuTsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar...
18/03/2025

Tinubu Ya Cutar da Al’ummar Rivers Ta Hanyar Ƙaƙaba Dokar Ta ɓaci — Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza ɗaukar matakan da s**a dace wajen magance rikicin siyasar da ke addabar jihar Rivers. Atiku ya bayyana cewa, maimakon yin sulhu da warware matsalar cikin lumana, gwamnatin Tinubu ta zabi kakabawa al’ummar jihar dokar ta ɓaci, abin da ya kira cutarwa da tauye haƙƙin ‘yan ƙasa.

Ya ƙara da cewa, wannan mataki na nuna rashin iya jagoranci da gazawar gwamnati wajen yin adalci. Atiku ya bukaci a nemo hanyoyin warware rikicin ta hanyar tattaunawa maimakon amfani da ƙarfin gwamnati.

Tun bayan rikicin siyasar da ya kunno kai a jihar Rivers, an sha samun cece-kuce game da rawar da gwamnatin tarayya ke takawa wajen shawo kan lamarin.

Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan Rikon Kwarya a Jihar RiversShugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Vice Admiral Ibokette Ib...
18/03/2025

Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan Rikon Kwarya a Jihar Rivers

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya) a matsayin sabon gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers na tsawon watanni shida.

Idan za a iya tunawa, Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, tare da majalisar dokokin jihar, bayan da aka ayyana dokar ta-ɓaci a jihar saboda rikicin siyasa da ya daɗe yana addabar yankin.

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaban kasa ya bayyana cewa, bayan nazari da duba halin da ake ciki, dole ne a aiwatar da sashi na 305 na kundin tsarin mulki domin tabbatar da doka da oda a jihar Rivers daga yau, 18 ga Maris, 2025.

Tinubu ya ce ya yi iyakar kokarinsa don warware matsalar siyasar da ke tsakanin gwamnan da majalisar dokokin jihar, amma dukkan ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin sasanci. Haka nan, shugaba ya bayyana cewa, wasu jiga-jigan siyasa sun yi ƙoƙari wajen samar da mafita, amma har yanzu babu wata sahihiyar gwamnati a jihar.

A saboda haka, gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa na tsawon wata shida, tare da naɗa Vice Admiral Ibokette Ibas domin jagorantar jihar har zuwa lokacin da za a kammala tantancewar da kuma samar da cikakken shiri na siyasa a jihar.

Jirgin saman kamfanin Max Air ya yi hatsari a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.Jirgin dai ya taso ne daga Legas lokac...
28/01/2025

Jirgin saman kamfanin Max Air ya yi hatsari a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Jirgin dai ya taso ne daga Legas lokacin da lamarin ya faru.

Wani fasinja da ya tsallake riniya da baya maisuna Aliyu Inuwa, yace al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:45pm na daren ranar Talata daidai lokacin da tayar jirgin ta samu matsala.

Har ila yau, Manajan Max Air Kano, Malam Bello Ramadan ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ba a samu asarar rai ba

Yadda mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, mataimakinsa Atiku Abubakar da s...
16/11/2024

Yadda mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, mataimakinsa Atiku Abubakar da sauran manyan baki s**a iso Kano, domin halartar daurin auran yar gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamnan Kano Abba Kabir  Ya Ce Cin Fuska Ne A Wajena Kalmar "Abba Tsaya Da Kafarka"Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir  Yusuf ...
07/11/2024

Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Ce Cin Fuska Ne A Wajena Kalmar "Abba Tsaya Da Kafarka"

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce cin fuska ne a wajena kalmar "Abba Tsaya Da Kafarka" kamar yanda wasu suke Faɗa
Abba ya ce shekaru 40 nayi da Kwankwaso na kwashe tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Kuma Muna Tare Dashi har yanzu
Ina mamakin yadda wasu suke cewa na Tsaya da Kafata Kuma wanna Cin Fuska ne gare ni, domin kuwa Kwankwaso Mai gidana ne Muna zaune Lafiya dashi Dan Haka Babu Wata Baraka a tsakaninmu

Daga Yau Laraba 6-11-2024 Duk Wani jami'in Gwamnati ko abokan Arziki ko masoya na haramata masa Kara Cewa na Tsaya da Kafata

Kwankwaso shine Jagoran mu Kuma shine Shugaban mu, Anna Saboda San zuciyar Wasu Suke Kokarin Kawo Mana rikici a Jam'iyyar NNPP Dan Haka nake Muku rantsuwa da Cewa wallahi bani da masaniya akan abinda Wasu Ke Cewa wai Akwai rigima tsakanina da Kwankwaso.

Nayi niyyar zuwa Kotu akan Cewa wai Kwankwaso ya kirani sau 33 ban dauka ba, to Amma na hakura Saboda Yadda nake girmama Yan Jarida acewar Abba Kabir Yusuf Yayin Zanatwarsa da manema Labarai a Daren Laraba a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Tinubu dai ko yara basu tsira daga ukubar gwamnatinsa ba. In ji Atiku a yayin da ya soki Tinubu kan Azabtar da kananan y...
02/11/2024

Tinubu dai ko yara basu tsira daga ukubar gwamnatinsa ba.

In ji Atiku a yayin da ya soki Tinubu kan Azabtar da kananan yara saboda sun masa zanga-zanga.

Gurfanar Da Ƙananan Yara A Gaban Kotu Tsantsar Zalunci Ne

Wannan abu na tayar da hankali ya tuna min da zaluncin ’yan aƙidar N**i.

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan abin da ya kira zalunci dangane da gurfanar da ƙananan yara a gaban kotu domin yi musu shari’a.

A ran Juma’ar ce wani bidiyo ya nuna wasu ƙananan yara aƙalla 20 kwance a zauren kotu suna numfashi da ƙyar da ke alamta yunwa ta yi musu illa.

Sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya ce ya damu da bidiyon yaran da aka nuna “bayan yunwa ta yi musu illa, a inda aka tsare su.”

“Wannan abu na tayar da hankali ya tuna min da zaluncin ’yan aƙidar N**i, tare da ƙara fito da yadda gwamnati ke nuna rashin kulawa da rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, musamman ƙananan yara”, in ji Atiku.

Ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa ƙananan yara cikakken ’yancin mutuntawa, amma abin mamakin sai s**a rasa hakan a Najeriya, a cewar Atikun.

“Ina mamakin mutumin da ke iƙirarin kare dimokuraɗiyya, har ya jagoranci zanga-zanga a baya, amma a yanzu yake barazana ga waɗanda ke yunƙurin nuna damuwarsu kan halin da s**a shiga sakamakon manufofinsa masu tsauri.”

Ya ƙara da cewa ƙananan yaran waɗanda su ne s**a fi cutuwa kan manufofin gwamnatin Tinubun na da damar gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su dama.

Malam Shekarau Ya Fara Jagorantar Sabuwar Tafiyar Samar Da Shugabanci Na Gari A NajeriyaTsohon gwamnan Kano kuma tsohon ...
23/10/2024

Malam Shekarau Ya Fara Jagorantar Sabuwar Tafiyar Samar Da Shugabanci Na Gari A Najeriya

Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya fara jagorantar wata tafiya domin tabbatar da samar da shugabanci na gari a Najeriya.

Wata tawaga da tsohon gwamnan ya jagoranta zuwa birnin Abeokuta ta ziyarci tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da tsohon ministan Tsaro Theophilus Yakubu Danjuma domin tattaunawa da samun shawarwari a kan manufarsu.

Bayan kammala ziyarar a Lagos tsohon gwamnan Kano Malam Shekarau ya shaidawa RFI Hausa cewa babban dalilin da ya sa s**a fara tintibar masu ruwa da tsaki shine, domin nemo masu tunanin samar da shugabanci na gari ba kawai a yankin arewacin Najeriya ba har ma da ƙasar baki ɗaya.

Shekarau ya ce a cikin tafiyar da s**a fara suna son su zaburar da al’umma tun daga matakin mazaba har zuwa matakin ƙasa domin su gano waɗanda zasu yi musu adalci, kuma su tallata su a basu dama ta shugabanci a Najeriya.

Ba mu ce mun fi kowa iyawa ba, amma mun yarda cewa a arewa da kuma ƙasar nan baki ɗaya muna da nagartatttun mutane da gogaggun waɗanda idan aka basu dama, zamu zaburar da al’umma domin su hango duk wanda s**a san yana da wata gogewa da adalci da kuma gaskiyar da zai jagoranci mutane da adalci, domin mu yi yunkuri mu tallata su, mu fito da su a basu dama su zo su gabatar da abinda suke yi.

A yadda ake tafiya an mayar da siyasa ta zama ta kuɗi, ta zama ta ubangida, suna ɗorawa mutane shugabanci ko sun iya, ko ba su iya ba, ko sun dace, ko ba su dace ba, ko suna da ƙwarewa ko basu da ita, kuma duk yadda s**a dama haka ake sha.

Shekarau ya ce suna son su zaburar da ƴan ƙasa daga arewa dake da ƙuri’a mafi yawa da ma ƙasa baki ɗaya cewar su daina la’akari da abinda ake basu ranar zabe ta yadda wasu ke dasa shugabannin da basu cancanta ba.
Tsohon gwamnan na Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce za su nemi haɗin kan duk wanda yake son bada gudunmawa kuma zasu samu nasara.
Ya ce babban ƙudirinsu a ƙarshe shine a samar da shugabanci na gari a Najeriya.

Makarantun Gwamnati A Sabon Gari Sun Zama Maboyar Masu Aikata Laifuka—BincikeWani bincike da aka gudanar na nuni da cewa...
18/10/2024

Makarantun Gwamnati A Sabon Gari Sun Zama Maboyar Masu Aikata Laifuka
—Bincike

Wani bincike da aka gudanar na nuni da cewa an kwace makarantun gwamnati guda uku a yankin Sabon Gari, inda Makarantun s**a zama maboyar ‘yan fashi da makami.
Makarantun da ake magana a kai su ne Maikwatashi Secondary School, Zawa’i Junior Secondary School, and Government Girls Secondary School Maikwatashi, duk suna kan t**in Igbo a unguwar Sabon Gari.
Waɗannan Makarantun An mamaye Waɗannan makarantun masu aikata laifuka dauke da muggan makamai sun mamaye yankin, hakan na barazana ga lafiyar dalibai da ma’aikata, da kuma kawo cikas ga yanayin karatun daliban.
Lamarin ya sa iyaye da masu kula da yara da dama s**a janye ‘ya’yansu, daga zuwa makaranta saboda wannan lamarin.
Yanzu haka dai dalibai hudu ne kawai ke zuwa makarantar Zawa’i Junior Secondary School saboda makarantun sun zama maboyar miyagu da ‘yan daba.
Haka zalika Makarantun sun lalace gaba daya, ba rufi,ba tagogi, ko kofa, su kansu gine-ginen sun tsattsage ga matsalar tsaro.
Da aka tuntubi hukumomin makarantar da Kano State Senior Secondary Schools Management Board (KSSSMB) da kungiyar iyaye da malamai ta (PTA) sun bayyana cewa an aika wasiku da dama ga hukumomin da abin ya shafa kan harkokin tsaro da samar da ababen more rayuwa da s**a shafi makarantun.
Mista Samuel Mbadwe, mamba a kwamitin kula da makarantu (SBMC) a GSS Maikwatashi, ya nuna damuwarsa kan halin da makarantar ke ciki da rashin tsaro.
Ya bayyana cewa kwamitin SBMC ya yi iya bakin kokarinsa wajen shiga tsakani amma bai samu nasara ba saboda kalubalen tsaro da ake fuskanta.
Lamarin dai ya ja hankalin majalisar dokokin jihar inda ta umarci kwamitin ta na ilimi da ya binciki kudirin da Hon. Yusuf Bello Aliyu, mamba mai wakiltar mazabar Nassarawa ya yi.
Kudirin ya bukaci a mayar da makarantun zuwa unguwar Kaura Goje, saboda yawancin daliban sun fito ne daga makwabtan yankunan kamar Brigade, Tudun Wada, da Gwagwarwa.
A cikin ajujuwa goma, uku ne kawai ake amfani da su a halin yanzu, yayin da masu laifi da 'yan daba s**a mamaye sauran filin.
Kwamitin ya ba da shawarar cewa gwamnati ta magance wadannan matsaloli masu mahimmanci tare da tabbatar da tsaro da kuma gudanar da ayyukan Makarantun
NIGERIAN TRACKER ta ruwaito cewa ana amfani da rufin ajujuwa wajen adana makamai.
A ranar 25 ga Janairu, 2024, ‘yan sanda sun kwato bindiga kirar AK-47 daga harabar, tare da harsashi masu yawa.
Bayan samun rahoton karshe da shawarwari, majalisar ta sake tura kwamitin ilimi domin ya binciki dalilin da ya sa gwamnatin jihar ba ta da masaniya kan halin da ake ciki.
An fahimci cewa daya daga cikin manyan batutuwan da s**a addabi makarantun shi ne rashin zuwan dalibai Makarantun,
Kuma Makarantun dai na karkashin yakin Fagge ne, yayin da mafi yawan daliban sun fito ne daga yakin Nassarawa.

Ba na so na ce uffan game da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'iyyar NNPP a jihar Kano - Rabi'u Musa Kwankwaso Dan...
15/10/2024

Ba na so na ce uffan game da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'iyyar NNPP a jihar Kano - Rabi'u Musa Kwankwaso

Dan takarar shugabancin Nijeriya karkashin jami'iyyar NNPP a zaben da ya gabata na shekarar 2023 Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ya yanke shawarar ba zai ce komai ba game da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'iyyar NNPP a jihar Kano.

Kwankwaso na magana ne a gidansa na Miller Road a ranar Talata, a lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi kan rikicin da ya mamaye jami'iyyar, ya ce shi ba ya da abin cewa kan wannan batu kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Yadda Ƙarin farashin man fetur  ke tilasta Kanawa yin tafiyar ƙafaƘarin farashin man fetur da aka yi ƙara jawo guna-guni...
15/10/2024

Yadda Ƙarin farashin man fetur ke tilasta Kanawa yin tafiyar ƙafa

Ƙarin farashin man fetur da aka yi ƙara jawo guna-guni a wajan fasinjoji yayin da direbobi ke cewa da ma can ba wata ribar kirki suke samu ba jihar Kano.
Tun kafin ƙara farashin a yanzu mazauna jihar Kano kan sayi litar mai kan sama da N1,000.
Amma a yanzu masu ababen hawa kan ce akan samu man a NNPCL kan N1,070, yayin da 'yankasuwa kan sayar a N1,050 zuwa N1,250.
Wata ɗaliba ta bayyana cewa N1,500 bai zama lallai su kai ta inda za ta je ba kuma ta riga ta fito t**i.
"Daga Unguwar Uku na ke zuwa Yusuf Maitama University da ke Kabuga kuma Naira 800 ba zaka kaini makaranta ba ni ɗaliba ce," a cewar ɗalibar da ba ta bayyana sunanta ba.
Wani ɗankasuwa ya ce tsadar kuɗin Adaidaita sahu ya sa yake tafiyar kusan N100 a ƙafa kullum idan zani kasuwa.
"Ina kashe N1,200 daga gidana zuwa kasuwa, ," kamar yadda ya baiyyana wa Jaridar INDA RANKA
"Gaskiya an shiga wani hali na takura, ya kamata shugabanninmu su duba halin da talakawa ke ciki, su nema mana sassauci," a cewarsa.
Bisa al'ada, kuɗin zirga-zirga na ƙaruwa nan take da zarar an ƙara farashin fetur ɗin, kuma a wannan karon direbobi ma sun koka cewa lamarin ya shafe su sosai.

Tsadar Wake Na Ci Gaba Da Karya Jarin Masu Sana'ar Kosai A Kano Mafi akasarin masu sayar Kosai a cikin birnin Kano sun d...
14/10/2024

Tsadar Wake Na Ci Gaba Da Karya Jarin Masu Sana'ar Kosai A Kano

Mafi akasarin masu sayar Kosai a cikin birnin Kano sun daina kasuwanci saboda tsadar wake da man girki a jihar .
Kosai, wanda aka fi sani da Akara a wasu sassan Najeriya, wani abinci ne da aka fi amfani da shi don karin kumallo a yankuna da dama na Arewacin Najeriya ciki har da jihar Kano.
Tsadar kayan masarufi ya wuce gona da iri a ‘yan kwanakin nan, domin galibin masu yin sa a jihar ba za su iya cigaba ba Sakamakon tsadar wake da man gyada.
A yanzu dai ana sayar da wake tsakanin Naira 3,800 zuwa Naira 4,200, gwargwadon irin nau’in da ake samu a kasuwa, yayin da man gyada da aka fi soya ƙosan, ana sayar da shi tsakanin Naira 1,700 zuwa Naira 1,900.
Wani bincike da jaridar Prime time ta gudanar a sassan birnin Kano da s**a haɗa da Kurmawa, Indabawa, Mubi, Tarauni da Nasarawa, ya nuna cewa galibin masu sayar da ƙosan sana'ar ta gagare su a halin yanzu.
Wasu kuma sun koma Gurasa, abincin gida da ake yi da fulawa, da s**ari, ko kuma wainar wake.

Yanzu-yanzu: gobara ta tashi a kasuwar Kantin KwariWata mummunar gobara ta tashi a yammacin yau Asabar a babbar kasuwar ...
05/10/2024

Yanzu-yanzu: gobara ta tashi a kasuwar Kantin Kwari

Wata mummunar gobara ta tashi a yammacin yau Asabar a babbar kasuwar yadudduka ta Kantin Kwari da ke Kano.

A yanzu haka dai dandazon matasa da masu ƙoƙarin kashe wutar suna cikin kasuwar domin samo hanyar kashe gobarar.

Address

No. A1 Dantsoho Plaza, Abdullahi Bayero Road
Kano
700101

Telephone

+2348022400739

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daily Enquirer Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Daily Enquirer Hausa:

Share