24/07/2025
Waiwaye.
A cikin bazarar shekarar 1979, Malam Moussa Ali, mai shekaru 85 a yanzu, na tsaka da noma a gonarsa a kusa da wani ƙaramin ƙauye a jumhuriyar Nijar. Kwatsam, sai fartanyarsa ta shuri wasu tarin ƙarafa. Tonawarsa ke da wuya sai ya sami tarin tsoffin harsasai da albarusai da aka yi amfani da su. Malam Moussa ya ci gaba da cewa: "Daga nan na fahimci lallai labarin da kakanninmu s**a gaya mana tabbas gaskiya ne,"
Labarin da Moussa ya ji a lokacin yarinta shi ne na yaƙin Koram Kalgo.
Domin kuwa a cikin watan Yuli na shekarar 1899, wani kamfani na sojan Faransa ɗauke da makamai, ya kai hari ƙauyen kakanninsa. Kuma idan da Malam Moussa ya sami damar shiga wani ɗaki na adana kayan tarihin mulkin mallaka na Faransa a Aix-en-Provence, da ya karanta wani saƙo da Faransawan s**a aiko a wannan ranar,
Saƙon dai ya ce, “Mun kai hari wani ƙaramin ƙauye mai kimanin mutane 600, mun rasa soja biyu, sannan soja 14 sun jikkata. Amma an kashe duk mazauna ƙauyen, an kuma ƙone ƙauyen ƙurmus."
Ina ma kuma ya iya karanta littafin diary na wani jami'in Faransa da aka aika don neman ƙarin bayani, kan wannan kisan kiyashin, bayan jita-jitar ta'addancin da aka yi ta isa birnin Paris. Ga abin da ya rubuta.
“Da tsakar rana, muka isa ƙauyen Koram Kalgo. Ba mu iske kome ba face tashin hankali. An baje ƙauyen, sai wani dattijo kawai da ke zaune a cikin toka, shi ya shaida mana cewa sojojin sun fice tun kwanaki huɗu da s**a wuce. Mun kuma iske wasu ‘yan mata biyu ‘yan kimanin shekara 10 a rataye a jikin bishiyar da ke ƙofar ƙauyen. A ko ina ba ka hangen komai sai gawarwakin mutane, wasu a rigingine, wasu rub da ciki, manyansu da ƙananansu kuwa."
Malam Moussa Ali ya ajiye harsashin nan sama da shekaru arba'in, domin adana hujjojin wannan mugun labari.
Gaskiya akwai bukatar ka nemi ƙarin bayani a kan abubuwan nan da s**a faru a Koram Kalgo da ke jumhuriyar Nijar cikin shekarar 1899. Har wani shiri BBC s**a yi, musamman domin tunawa da wannan ranar.